Daga Abdullahi I. Mahuta
Wata rana a makarantar manya, malamin koyar da Darasin Sanin Halayyar Ɗan Adam (Psychology) ya shiga aji ya ce: “yau za mu yi wani wasa!”
Malam ya ce “a cikinku wa zai fito gaban allo a fara da Shi?”
Sai wata ɗaliba mai suna Salma ta fito. Sai malam ya ce ta ɗauki alli ta rubuta sunan mutane 30 masu muhimmanci a rayuwarta. Salma ta rubuta dangi, ƙawaye, abokan karatu da maƙwabtanta.
Sai Malam ya ce ta goge sunayen mutum uku, waɗanda ba su da muhimmanci sosai a wajenta. Salma ta goge suna uku na abokan karatunta.
Sai malam ya ce ta ƙara goge mutum biayar marasa muhimmanci. Salma ta goge maƙwabtanta. Malam
ya yi ta umartar ta tana gogewa har sai da ya rage saura
sunayen mutum huɗu kaɗai, su ne:
1. Mahaifiyarta.
2. Mahaifinta.
3. Mijinta.
4. Ɗanta ɗaya tilo.
Gaba ɗayan ɗalibai sai suka natsu, domin sun gane cewa
wannan ba wasa ba ne, kamar yadda Malam ya faɗa da farko. Ya dai zo musu ne da wani darasi mai muhimmanci.
To! Sai Malam ya kalli Salma ya ce ta ƙara goge mutum biyu daga sunayen nan da suka rage. Wannan zaɓin fa yana da wuya. Salma ta yi jimmm! Hannunta yana rawa, ba a son ranta ba, idonta ya cika da ƙwalla: ta goge sunan mahaifiyarta da mahaifnta.
Cikin sunayen mutum biyu da suka rage, sai Malam ya ce ta ƙara goge sunan ɗaya.
Nan fa sai Salma ta saka kuka amma cikin hawaye ta goge sunan ɗanta ɗaya tilo da ta haifa.
Daga nan sai Malam ya ce ta koma wajenta ta zauna.
Bayan wani ɗan lokaci sai Malam ya yi tambaya, ya ce: “Ko me ya sa Salma ta bar mijinta, ta goge sauran?”
Ya ce: “Iyaye fa su ne suka kawo ki duniya, suka raine ki har kika girma. Ɗanki kuma ke kika yi cikinsa kika sha wahalar laulayin cikin, har kika haife shi, kika raine shi. Kuma da iyaye da ɗa, ba za ki iya sake waɗansu ba. Amma miji koyaushe za ki iya canja wani.”
Aji aka yi shiru ana jiran amsar Salma. Ita kuwa, cikin nutsuwa da sanyin murya ta ce: “Wata rana ina tare da iyayena sai suka ɗauke ni suka kai ni gidan miji. Idan na kawo musu ziyara sai su tambaye ni ko lafiya?
Idan ya yi mini laifi na taho gida sai su kira shi su yi ta ba shi haƙuri, su ce na tashi na koma gidansa.”
Ɗana kuma wata rana zai bar ni idan ya girma. Zai mai da hankali kan sana’arsa da hidimar iyalinsa. Mutum ɗaya wanda zai ƙare rayuwarsa tare da ni shi ne MIJINA. Kuma…” Kafin ta ƙara magana sai ɗalibai suka ɗauki tafi gaba ɗaya saboda ta faɗi gaskiyar yadda rayuwa take.
Sai malam ya ce “Gaskiya ne, Allah ya sanya aure a tsakanin miji da mata ya zama dangantaka ta tsowon rayuwarsu. Koyaushe ka girmama abokin rayuwarka (miji ko mata).
*
Allah Ya sanya miji da mata su zama abu ɗaya, kamar yadda ya zo a cikin Alƙur’ani mai tsarki, Allah Yana cewa: “Yana daga cikin ayoyinSa, Ya halitta muku matayenku daga jikinku, don ku rayu da su. Ya sanya a tsakaninku soyayya da jin ƙai. Haƙiƙa a cikin wannan akwai aya ga ma’abuta TSAKANINKU tunani.”
Don haka ku ma’aurata, ku za ku saka wannan dangantaka ta zama sama da kowace dangantaka a duniyar nan. Son Allah da Manzonsa ita ce hanyar da za a rabauta. Yardar Allah tana cikin bin dokokinsa. Ma’aurata ya zama wajibi ku bai wa aurenku abinci ya girma ya yi ƙarfi, abincin kuwa shi ne bin dokokin Allah, gaskiya, riƙon amana, haƙuri, zaman lafiya, soyayya da tsoron Allah.
Ya Allah Ka sa albarka a cikin aurenmu, Ka sa muna cikin bayinKa da Farin Jakada Ɗan Abdullahi Manzon tsira (saw) zai yi alfahari da mu amin.













