KATSINA_2026:
Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Ma sha Allah! Allah ya ƙara kawo mu lokacin wannan gagarumin biki na Ranar Marubutan Hausa ta Duniya kuma in sha Allahu a Katsina za a gudanar da wannan biki.
Bikin bara (2025), duk da cewa a wannan shekarar aka gudanar da shi (an makara), an gudanar da shi ne a garin Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa. Kuma sai godiya ga Allah, yadda bikin ya gudana.
A Katsina, ina da yaƙinin taron na bana zai ba da suga fiye da ƙima, in sha Allah! Wannan kuwa, saboda waɗannan dalilai:
• A Katsina aka fara ƙyanƙyashe marubutan Hausa da ma na Ingilishi a duk faɗin Arewa. Katsina College ce ta samar da marigayi Abubakar Imam, mai Ruwan Bagaja da Magana Jari Ce.
• A Katsina aka samu marigayi Malam Labo Yari, marubucin da ya fara rubuta littafin Ingilishi na farko a Arewa mai taken “Harvest of Corruption.”
• A Katsina aka yi shahararren ɗan wasan kwaikwayo kuma marubuci, marigayi Ɗanjuma Kasagi, marubucin littafin Kulɓa Na Ɓarna.
• A Katsina muke da manyan marubuta da manyan ‘yan jarida. Muna da Farfesa Ibrahim Malumfashi, muna da Dakta Ibrahim Sheme muna da Ɗanjuma Katsina kamar kuma yadda muke da almajirin ɗan jarida kuma marubuci, Fasihin Galadiman Katsina, Bashir Yahuza Malumfashi
• A Katsina muke da manyan masana kuma manazarta Hausa, irin su Farfesa Bashir Abu Sabe Dakta Abdulrahman Aliyu da Farfesa Aliyu Ibrahim Kanƙara da Fasihin Kaita, Malam Isyaka Dankama, da sauransu.
• A Katsina muke da manyan Sha’irai, irin su Malumman Matazu, Malam Abdulhamid Matazu muke da Sanƙiran Zamani, Kabir Bahaushe da masu kishin Hausa, irinsu Dikko Bala Kofar Sauri da sauransu.
• A Katsina muke da manyan mawaƙan Hausa, irin su marigayi Dakta Mamman Shata, margayiya Barmani Choge da kuma Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa, Dauda Kahutu Rarara da sauransu.
• A Katsina muke da Sarki Dikko da Gwamna Dikko, Dr. Dikko Umaru Radda ga kuma Sarkin Daura, Daura jagorar ƙasashen Hausa.
Muna roƙon Allah ya kai mu ranar wannan biki lafiya kuma mu kammala lafiya!
MARUBUTAN HAUSA, KATSINA TANA YI MAKU LALE MARHABUN!
___________













