Za A Dasa Bishiyoyi Miliyan 11 Domin Yaƙi Da Hamada A Jihar Katsina
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D. ya ƙaddamar da kwamitocin dasa itatuwa guda miliyan 11 a ‘Shirin Mutum Ɗaya Itace Ɗaya A Jihar Katsina’ (KT1T).
An ƙaddamar da wannan shiri ne a ranar Alhamis da ta gabata (27-08-2026), a wani muhimmin mataki na ƙarfafa kare muhalli da daƙile barazana ga sauyin yanayi a faɗin Jihar Katsina.
Bikin ya gudana ne a babban ɗakin taro da ke cikin gidan gwamnati, domin samar da ingantaccen tsarin da zai tabbatar da aiwatar da shirin a ƙananan hukumomi 34 da mazaɓu 361 na faɗin jihar.
Shirin na daga cikin manufofin Gwamnatin Gwamna Radda na “Building Your Future (BYF)” kuma an gina shi ne bisa tsarin shuka bishiya ɗaya ga duk mutum ɗaya na Jihar Katsina. Manufarsa ita ce shuka bishiyoyi guda miliyan 11 a faɗin jihar, don ƙarfafa al’umma wajen dasa itatuwa, kare su da kuma ɗaukar nauyin kiyaye muhalli.
Tsarin kwamitocin matakai huɗun ya ƙunshi Babban Kwamitin Gudanarwa, Kwamitocin Sa-ido a kowace shiyya, Kwamitocin Kula da Aiwatarwa na Ƙananan Hukumomi da Kwamitocin Aiwatarwa na Mazaɓu.
Kamar yadda aka tsara kwamitocin, za su kasance kamar haka: Mai Bai Wa Gwamna Shawara Kan Harkokin Sauyin Yanayi, Farfesa Al’amin Muhammad zai kasance shugaban shirin na jiha. Hon. Abdullahi Aliyu Turaji zai kasance shugaban kwamitin shiyyar Katsina, yayin da Hon. Shafi’u Abdu Duwan zai kasance shuhaban shirin na Shiyyar Daura; inda Hon. Iyaku Dabai zai kasance jagoran shirin na Shiryar Funtua. Hakazalika, kowane shugaban ƙaramar hukuma zai kasance jagoran shiri a ƙaramar hukumarsa, yayin da kowane kansila zai kasance jagoran shirin a mazaɓarsa.
Kwamitocin za su jagoranci ayyukan shirin a faɗin yankunan da suka fi buƙatar shirye-shiryen ayyukan sauyin yanayi (Climate Intervention Areas) guda 6,652, tare da haɗin gwiwar shirin CDP, domin tabbatar da cewa an kare itatuwan da aka dasa kuma an kula da su yadda ya kamata.
Gwamna Radda ya jaddada cewa nasarar shirin ba za ta ta’allaƙa ne kawai kan yawan itatuwan da aka dasa ba, sai dai kan yawan waɗanda suka rayu, suka girma kuma suka samar da tasiri mai ɗorewa ga al’umma. Ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin addini, ƙungiyoyin matasa da mata, ƙungiyoyin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da su mallaki shirin tare da bayar da cikakken goyon baya.
Ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen yaƙi da kwararowar hamada da zaizayar ƙasa, tare da ƙarfafa al’umma ga tsarin sauyin yanayi, bunƙasa noma, inganta lafiyar jama’a da samar da hanyoyin more rayuwa.
Da yake jawabi a wajen taron, Mai Bai wa Gwamna Shawara na Musamman kan Sauyin Yanayi, Farfesa Al’amin Muhammad, ya bayyana shirin a matsayin wata muhimmiyar hanya ta tunkarar ƙalubalen muhalli da ke fuskantar Jihar Katsina. Ya ce haɗin gwiwar al’umma, sa ido a kai-a kai da kuma kula da itatuwan da aka dasa, za su kasance muhimman ginshiƙai wajen cin ma manufofin shirin.
Shi ma Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautun Gargajiya, Hon. Bishir Tanimu, ya yaba wa Gwamna Radda bisa sanya al’umma a tsakiyar manufofin kare muhalli. Ya tabbatar da cewa ƙananan hukumomi 34, sarakunan gargajiya da sauran tsarin shugabanci na matakin ƙasa, za su haɗa kai domin tabbatar da ingantaccen aiwatar da shirin da ɗorewarsa.
Gwamna Radda ya sanar da cewa za a fara aiwatar da shirin dasa itatuwan a hukumance a faɗin Jihar Katsina daga ranar 10 ga Satumba, 2026, yayin da kwamitocin da aka ƙaddamar za su fara shirye-shirye da wayar da kan jama’a gabanin ranar ƙaddamarwar.
Taron ya samu halartar shugaban ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Alh Abdulkadir Mamman Nasir, Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dokoki, Hon Dabai, kwamishinoni, shuwagabannin ƙananan hukumomi, kansiloli da sauran ‘yan kwamitoci.
__________












