Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
_________
Kamar yadda aka saba, yau ma wakilinmu yana ɗauke da rahoton tariyar muhimman al’amuran da suka wakana a Jihar Katsina a makon da ya gabata, wanda ya faro daga ranar Juma’a zuwa Lahadi (24-30-08-2026).
Muhimmin al’amarin da za mu taba, shi na ranar Talata, 25 ga Agusta, 2026, inda Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D, CON, ya yi kira ga malamai da al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W.) wajen yawaita addu’o’i domin zaman lafiya, tsaro da ci gaban Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da wasu malamai da al’ummar Musulmi suka ziyarce shi a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina domin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (S.A.W.).
Ai’amari na gaba mai matuƙar muhimmanci da ya gudana a makon da ya gaba, shi ne inda mai girma Gwamna Malam Dikko ya ƙaddamar da kwamitocin dasa itatuwa guda miliyan 11 a ‘Shirin Mutum Ɗaya Itace Ɗaya A Jihar Katsina’ (KT1T).
An ƙaddamar da wannan shiri ne a ranar Alhamis da ta gabata (27-08-2026), a wani muhimmin mataki na ƙarfafa kare muhalli da daƙile barazana ga sauyin yanayi a faɗin Jihar Katsina.
Bikin ya gudana ne a babban ɗakin taro da ke cikin gidan gwamnati, domin samar da ingantaccen tsarin da zai tabbatar da aiwatar da shirin a ƙananan hukumomi 34 da mazaɓu 361 na faɗin jihar.
Shirin na daga cikin manufofin Gwamnatin Gwamna Radda na “Building Your Future (BYF)” kuma an gina shi ne bisa tsarin shuka bishiya ɗaya ga duk mutum ɗaya na Jihar Katsina. Manufarsa ita ce shuka bishiyoyi guda miliyan 11 a faɗin jihar, don ƙarfafa al’umma wajen dasa itatuwa, kare su da kuma ɗaukar nauyin kiyaye muhalli.
Al’amari na gaba shi ne wanda Gwamna Malam Dikko Umar Radda, ya halarci bikin naɗin sabbin sarautu da Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar ya gudanar a Masarautar Daura, bayan kammala bikin Hawan Sallar Gani.
A yayin bikin, Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar ya naɗa Ministar Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙire-Ƙirƙire ta Tarayya, Barista Hannatu Musa Musawa, sarautar Mairamar Kasar Hausa.
Haka kuma, Mai Martaba Sarkin ya naɗa babbar ‘yar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Hajiya Mujidat Folashade Iyaloja Tinubu, matsayin Jakadiyar Kasar Hausa.
Al’amari na gaba mai muhimmanci, ya gudana ne a ranar Alhamis da ta gabata, inda Majalisar Zartarwa ta Jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, ta gudanar da taronta karo na 14, na bana a babban ɗakin taro na Gidan Gwamnati.
A yayin taron, Majalisar ta yi duba ga wasu takardu da rahotanni da aka gabatar gabanta, tare da amincewa da abubuwa kamar haka:
1. Siyen Karin Kayan Aiki ga Cibiyar Binciken Cututtuka da Maganin Ciwon Daji (Cancer Center).
2. Aikin Titi a Unguwar Rafukka
3. Amincewa da Ƙudirin Kasafin Kudi na Shekarar 2027
Majalisar Zartarwa ta amince da Ƙudirin Kasafin Kudin Jihar Katsina na shekarar 2027, wanda ya kai kimanin Naira Biliyan Ɗari Takwas da Ashirin da Takwas da Miliyan Ɗari Shidda da Talatin da Takwas da ‘yan kai (₦828,638,844,091.48).
An yi wa kasafin kudin laƙabi da “Building Your Future IV” wanda ke nuna ci gaba da ƙudurin gwamnatin wajen bunƙasa ɗan Adam, haɓaka tattalin arziki, sabunta ababen more rayuwa da inganta ayyukan jin daɗin al’umma.
Waɗannan su ne kaɗan daga cikin muhimman al’amuran da suka gudana a Jihar Katsina a makon da ya gabata. Sai kuma Allah ya kai mu ƙarshen wannan makon da muka shiga, domin kawo maku sabon rahoto.
_________











