• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, June 20, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Maryam ‘Yar Aljanna

ADABI

Nasir G. Ahmad by Nasir G. Ahmad
June 20, 2026
in Adabi
0
Maryam ‘Yar Aljanna

Maryam 'Yar Aljanna

2
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Maryam ‘Yar Aljanna
__________
Gabatarwa:
Wannan labari ƙirƙirarre ne kuma mun same shi ne daga haziƙin adibi, Malam Nasiru G. Ahmad. Labari ne mai mai cike da abin tausayi da kuma darussa masu yawa.
__________

Maryam ‘Yar Aljanna

Wani mutum ne da matarsa mai suna Maryam, suna zaman lafiya da kyautata wa juna. Rannan sai wata tafiya ta kama shi, ta fuskar neman abincinsa. Ya shiga tunanin wanda zai bar wa wasicin kula da ɗawainiyar matar ta yisa saboda tana da tsananin kyau, irin na a tsegunta wa yarima.

Related posts

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

June 8, 2026
ALHAMDU LILLAH

ALHAMDU LILLAH

May 15, 2026

Bai samu wanda zai ɗora wa wannan nauyi ba da ya wuce ɗan uwansa shaƙiƙi. Don haka ya danƙa al’amarin kula da iyalin nasa a hannunsa, ya kama hanya ya tafi.

Mutumin bai daɗe da tafiya ba, sai Shaiɗan ya shiga ya fita a zuciyar ɗan uwan nan da aka bar wa wasici, har ya je ga Maryam, matar ɗan uwan nasa da nufin neman ta. Ita kuwa ta ƙeƙasa ƙasa ta ce ba ta san wannan mugun aiki ba. Ya yi mata barazanar cewa, idan ba ta yarda ba zai kunyata ta. Ita ko ta ce ya yi duk abin da ya so, ita kam ba za ta ci amanar mijinta ba. Allah kuma zai kare ta daga kaidinsa.

Bayan dawowar maigidan, sai ɗan uwan nasa ya shaida masa cewa matarsa ta yi ta ƙoƙarin sa shi ya neme ta amma ya ƙi. Ba tare da wani kokwanto ba mijin matar nan ya sake ta, ya kuma kore ta daga gidansa. Ga shi ita Maryam ba ‘yar wannan garin ba ce. Mijin nata ya hana ta ko ɗan kuɗin da za ta yi guzuri da shi.

Maryam ta fita ba ta san inda ta nufa ba, har Allah ya kai ta can bayan gari, gidan wani mutum mai ibada kuma ma’abocin zuhudu. Ya tambaye ta labarinta, ta faɗa masa. Ya nemi ta zauna ta riƙa yi masa rainon wani ƙaramin yaronsa bisa wani lada da ya yanka mata. Ta kuwa amince, ta zauna a gidan wannan mai ibada.

Ana nan sai mai ibadar nan ya yi wata ‘yar tafiya. Sai hadiminsa ya shiga wajen Maryam, ya neme ta da ta biya masa buƙatarsa. Ita kuwa ta ce atafau ba dai ita ba. Ya ce in ba ta yarda ba, zai ƙulla mata sharri. Ta ce ya yi duk abin da ya so, Allah zai fisshe ta sharrinsa.

Sai hadimin ya sami yaron da take raino ya kashe shi.Yayin da mai ibada ya dawo, sai hadimin nan ya ce matar nan ce ta kashe yaron. Mai ibada ya yi matuƙar baƙin ciki da jin haka, ya fusata ainun. Amma sai ya tuna da faɗin ubangiji da ya ce, “Da masu haɗiye baƙin ciki, da masu yin afuwa ga mutane (da suka saɓa musu). Allah kuma yana son masu kyautatawa.” (Aal-Imran: 134) Sai ya haɗiye baƙin cikin nasa, ya ce ya yafe mata. Ya kuma kawo ladan aikinta na kwanakin da ta yi ya ba ta, ya nemi ta bar masa gidansa.

Cikin jimami da alhini, Maryam ta fita daga gidan Malam mai Zuhudu. Da yake ba ta san inda za ta nufa ba, sai ta yi nufin komawa cikin gari. Tana isa ƙofar gari sai ta iske wasu mutane sun kama wani mutum, suna ta dukan sa. Ta tsaya ta tambayi me ya yi? Sai suka ce mata bashin wasu kuɗi ake bin sa. Muddin kuwa bai biya ba, to ya zama bawan masu bin sa bashin.
•••
• A saurari kashi na biyu na wannan labari.
__________

Previous Post

Dr. Bukar Usman Reviews Historical Book on the Lassa Community

Related Posts

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido
Adabi

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

June 8, 2026
ALHAMDU LILLAH
Adabi

ALHAMDU LILLAH

May 15, 2026
Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
Adabi

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Kaduna State Pilgrims are to Deposit ₦2.5 Million

Kaduna State Pilgrims are to Deposit ₦2.5 Million

October 6, 2023
An Kama ‘Yan Sandan Bogi Da Motoci Biyu Maƙare Da Wiwi

An Kama ‘Yan Sandan Bogi Da Motoci Biyu Maƙare Da Wiwi

October 2, 2025
₦16,000 Za Mu Sayar Da Taki A Jigawa – Gwamna Namadi

₦16,000 Za Mu Sayar Da Taki A Jigawa – Gwamna Namadi

July 26, 2023
BAKIN JAƁA (4)

BAKIN JAƁA (4)

September 16, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Maryam ‘Yar Aljanna
  • Dr. Bukar Usman Reviews Historical Book on the Lassa Community
  • Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Maryam ‘Yar Aljanna

Maryam ‘Yar Aljanna

June 20, 2026
Dr. Bukar Usman Reviews Historical Book on the Lassa Community

Dr. Bukar Usman Reviews Historical Book on the Lassa Community

June 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.