Wasa Farin Girki: Yau Ake Fara Gasar Kofin Duniya
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
A yau ne aka buɗe Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026, inda mai masaukin baƙi, ƙasar Mexico za ta fafata da South Africa a wasan farko na gasar.
Wannan wasa mai ɗaukar hankali zai gudana ne a filin wasa na Estadio Azteca da ke birnin Mexico City, wanda ya zama filin wasa na farko a tarihin Kofin Duniya da zai karɓi bakuncin wasan buɗe gasar har sau uku.

Dubban magoya baya daga sassa daban-daban na duniya sun hallara domin shaida fara wannan babbar gasa.
A ɓangaren Mexico, ana sa ran manyan ‘yan wasa kamar Raúl Jiménez, Edson Álvarez da Guillermo Ochoa za su taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar tawagar zuwa nasara. Ochoa na neman kafa tarihin zama ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan da suka yi Gasar Kofin Duniya sau da dama, yayin da Jiménez da Álvarez ke daga cikin ginshiƙan ƙungiyar.
A gefe guda kuma, tawagar South Africa na da ƙwararrun ‘yan wasa da ake sa ran za su haskaka, ciki har da Lyle Foster da Teboho Mokoena. Kocin ƙungiyar, Hugo Broos, ya bayyana cewa ‘yan wasansa sun shirya tsaf domin ƙalubalantar Mexico duk da goyon bayan da za ta samu daga dubban magoya bayanta.
Masana ƙwallon ƙafa na hasashen za a ga wasa mai zafi da armashi yayin da kowace ƙasa ke neman fara gasar da ƙafar dama.












