Malumfashi Mun Yi Babban Rashi

__________
A yau Litinin, 23-11-1447 (Hijiriyya), 11-05-2026 (Miladiyya), mun wayi gari da labarin rasuwar fitaccen Malamin Musulunci, Malam Bala Makaho, Fayamasa, Malumfashi, Jihar Katsina.
Marigayi Malam Bala, makaho ne a gululun ido amma mai gani ne tantagaran da hasken ilimin addinin Musulunci.
Kafin rasuwarsa, Malam Bala ya kasance mai yi wa Musulunci gagarumar hidima da ilimin da Allah ya hore masa. Shi ne Limami mai gabatar da khamsussalawati a masallacinsa da ke Unguwar Fayamasa. Haka kuma shi ne babban malamin da ke koyar da ilimi a makarantarsa, ba tare da gajiyawa ba.
Muna roƙon Allah ya ji ƙan shi da rahama, ya sanya ayyukansa a mizani. Allah ya inganta bayansa. Mu kuma da muka rage, Allah ka sa mu cika da ingantaccen imani, idan lokacinmu ya zo.
__________













