Malumfashi: Mun Yi Babban Rashin Uba
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Babu shakka Allah shi ne Sarkin Gaskiya, wanda ya ƙaga halitta kuma ya ƙadarta mutuwa. Ya ce dukkan rai sai ya ɗanɗani mutuwa!
Da safiyar yau Litinin, 26-03-1448 (Hijiriyya), 07-09-2026, muka wayi gari da labarin rasuwar ɗaya daga cikin iyayenmu da suka rage – Baba Hali, Gwamutsawa, Malumfashi, Jihar Katsina.
Baba Hali, kawuna ne, domin kuwa ƙane ne ga mahaifiyata (Allah ya ji ƙan su da rahama).
Allah da ikonsa, da rabon zan yi ganawar ƙarshe da shi, kasancewar na shigo garin Malumfashi tun kwanaki huɗu da suka gabata. Ni da ɗan uwana, Nasiru Ibrahim Jume, bayan mun gama Sallar Magriba, sai muka ce mu je mu gaishe shi, domin a kwanakin baya ya yi jinya.
Mun isa Gwamutsawa kuwa, sai muka iske shi, tare da Liman a bakin Masallaci suna tattaunawa, suna jiran Sallar Isha’i. Mun iske shi cikin ƙoshin lafiya, fuskarsa cike da annuri da haiba. Muka gaishe shi cikin jin daɗi da walwala tare da shi, muka yi bankwana – ashe bankwanan ƙarshe ke nan.
Da safiyar yau Litinin, sai Nasiru Ibrahim Jume ya kira ni, ya sanar da ni rasuwarsa, cikin alhini da ta’ajibi. Karfe goma na safe aka yi masa sutura, aka yi masa jana’iza, bisa ƙa’idar Musulunci. Mutane iya ganinka ne suka samu ikon sallatarsa.
Baba Hali, dattijo mai haƙuri, mai zumunci da kawaici, ya rasu yana da shekaru 86. Ya bar matarsa da ‘ya’ya da jikoki da ‘yan uwa da abokan arziki.
Wasu daga ‘ya’yan da ya bari sun haɗa da Najmudden Hali, Bello Hali, Hafizu Hali, Mubasshir Hali, Surajo Hali, Abba Hali, Ibrahim Hali, Asama’u Hali, Mabaruka Hali, Saude Hali, Maijidda Hali, Hadiza Hali da Zainab Hali.
Muna roƙon Allah ya ji ƙan shi da rahama, ya sanyaya makaancinsa, ya ba shi Aljanna Firdausi. Mu kuma da ke raye, idan namu lokacin ya zo, Allah ya ba mu ikon cikawa da ingantaccen imani! Amin-Summa-Amin!
__________













