‘Yan ta’addan Daji Kafirai Ne
– Sarkin Musulmi
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa duk wanda yake kashe rayukan bayin Allah haka kawai, ba za a kira shi da Musulmi ba, duk kuwa da cewa yana faɗin “Allahu Akbar” a yayin da yake aikata ta’addancinsa.
Mai Alfarma ya jaddada cewa, makomar duk wani ɗan ta’adda, ita ce wuta, inda zai fuskanci azabar wannan mugun aiki da ya aikata. Ya ƙara da cewa yawancin tashe-tashen hankali da ake dangantawa da addini, ana fahimtarsu ne ba daidai ba, lamarin da ke ƙara haifar da zargi da rashin yarda tsakanin jama’a.
Kamar yadda Jaridar Vanguard ta ruwaito, Sultan Sa’ad ya bayyana hakan ne a Larabar da ta gabata, a yayin taron farko na bana, na Majalisar Addinai ta Ƙasa (NIREC) da aka gudanar a Abuja, a matsayinsa na shugaban majalisar. Sauran abokan aikinsa da suka yi jawabi a yayin taron, sun haɗa da Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Daniel Okoh da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.
Da yake fayyace matsayarsa dangane da ‘yan ta’adda, a cewarsa: “Mu gyara yadda ake bayyana wannan batu. Ta’addanci ba batun addini ba ne. Mu daina jawo addini cikin wannan al’amari.
“Ya kamata mu riƙa kiran su da sunansu na gaskiya na ‘yan ta’adda. A daina jingina laƙanin “Musulmi” gare su. A daina kiran su da masu laifi Musulmi, ko ‘yan ta’addan Musulmi, ko ‘yan bindigar Musulmi. Ko da mutum ya ce shi Musulmi ne, abin da yake aikatawa ya saɓa wa koyarwar Musulunci, to ba za a laƙa wa addini laifin da ya aikata ba.”
Yayin da yake danganta matsalar da jahilci, Sultan ya yi gargaɗi kan yadda wasu ke ƙaryar cewa sun mallaki ilimin addini, yana mai cewa: “Kasancewar mutum ya iya Larabci ba ya sa ya zama Sheikh. Larabci harshe ne kawai. Saboda haka ilimi yana da matuƙar muhimmanci.
“Wani zai iya zuwa kasuwa ya tayar da bam, ya kashe mutane sannan ya yi ihu da ‘Allahu Akbar.’ Eh, Allah Maɗaukaki ne amma kai za ka tafi zuwa wuta. Za ka sha azaba saboda kashe rayukan bayin Allah da kake yi, marasa laifi.” In ji Mai Alfarma Sarkin Musulmi.
A yayin taron na bana, an buƙaci mabiya addinai mabambanta a ƙasar nan da su kai zukatansu nesa, su samar da zaman lafiya da fahimtar juna. An jaddada cewa, kowane addini yana kira ne zuwa ga bautar Allah shi ɗaya, don haka bai dace a yi amfani da shi wajen haddasa fitina a tsakanin al’umma ba.









![Lost Heritage Series #1 – Mazari [Spindle]](https://taskargizago.com.ng/wp-content/uploads/2023/09/FB_IMG_1695164994735-120x86.jpg)



