KANNYWOOD JIYA DA YAU: DARASIN RAYUWA DAGA WASU TAURARI (1)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Akwai darussa masu yawa na rayuwa daga hotunan bayin Allan nan biyu da ke tare da wannan tsokacin. Ɗaya sunanta Ummi Nuhu, ɗaya kuma Fatima Hussaini.
Suna da kamanceceniya ta fuskoki da dama, kamar kuma yadda suke da wasu bambance-bambance. Dukkansu dai mata ne kuma masu sana’ar fim a masana’antar Kannywood. Haka kuma dukkansu Musulmi ne kuma babu wacce take da aure.
Dukkansu sun samu shahara da ɗaukaka a fagen sana’ar tasu. A shekarun baya, Ummi ta shahara iyaka shahara. Ta samu kuɗi, ta kece raini, ta yi rayuwar ƙwalisa iya ƙwalisa – wasu sun tabbatar da cewa har ma ta yi rayuwar shaye-shayen muggan ƙwayoyi. Ta samu masoya da suka so su aure ta amma ba ta yi auren ba har zuwa yau ɗin nan.

Fatima Hussaini, wacce ake kira da Maryam Labarina, ita a yanzu ne take tata ganiyar. Sai dai ko kusa ba ta kai shaharar Ummi ba, ba ta kai ta samun abin duniya ba kuma ina ganin ba ta kai ta samun MASOYA da suke neman ta da aure ba.
Ba a samu labarin Fatima tana shaye-shaye ba AMMA kam tana da jiji-da-kai, tana da ƙaryar arziƙi, tana da cika baki kuma ga ta da iya wuce makaɗi da rawa da feleƙe.
Ta kafa tarihin gwalangwaso da taƙama da TURANCI, alhali alamu sun nuna ba ta da zurfin iliminsa. Ko a kwanan nan ta caɓa magana game da AURE.

Kamar yadda ta ce: “Ni ba zan yi wa mijina wanke-wanke da shara ba, ba aikina ba ne. Ba zan auri namijin da zai bar ni da TUWO-TUWO ba alhali gidanmu ana cin FIZZA!”
•••
Darussan za mu iya ɗauka a nan su ne: Mu kiyayi ɗagawa da jiji-da-kai a rayuwa. Mu daraja lokaci – mu riƙa aikata abin da ya dace a lokacin da ya dace. Mu kiyayi raina asali, mu kiyayi rayuwar bushasha da alfahari. Mu gane cewa RAYUWA gajera ce, musamman ga ɗiya mace – babu abin da ya kai AURE daraja a rayuwar ɗiya mace!













