• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, June 9, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

SHARHIN LITTAFI

Jibrin Yusuf Kaila by Jibrin Yusuf Kaila
January 17, 2026
in Adabi
0
Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Marubuci Bashir Yahuza Malumfashi da bangon littafin Tarkon Mut'a

27
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Daga Jibrin Yusuf Kaila

Related posts

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

June 8, 2026
ALHAMDU LILLAH

ALHAMDU LILLAH

May 15, 2026
Marubuci Bashir Yahuza Malumfashi da bangon littafin Tarkon Mut’a

 

                •••••••

Sunan Littafi: Tarkon Mut’a

Marubuci: Bashir Yahuza Malumfashi 

Kamfanin Wallafa: Gizago Publishing Enterprises.

Bugun Farko: 2019

Lambar ISBN: -978-2149-99-3

Yawan Shafuka: 91

                  •••••••

Jigo:

Littafi ne da yake magana a kan ɗaya daga cikin aƙidojin Shi’a, wato Auren Mut’a. Yana nuni da illolinsa a kan rayuwar  ɗan Adam da kuma nuna haramcinsa ƙarara ga koyarwar addinin Musulunci.

A karon farko, littafin da na karanta  a salon wasan kwaikwayo a rubuce, ya ƙayatar da ni kuma ya ja hankalina sosai. Haƙiƙa marubucin littafin ya fito da abubuwan da ake ribatar matasa da su a kan Auren Mut’a, ta hanyar a ruɗarwa da kalamai da ake kiran su ‘Kalamus Sihiri.’ Ya nuna da a nemi ilimi kuma kar a biye wa zuciya a faɗa halaka.  Littafin ya ƙara haska mana yadda masu aƙidar suke kushe da tsine  wa sahabbai, wanda ya saɓa da koyarwar Manzon Allah (saw) da faɗinsa:  “Ku bi sunnata da kuma ta khalifofina (Abubakar, Umar, Usman da Aliyu).” Masu wannan aƙidar, suna kaucewa, suna faɗin cewa ƙarya ake musu. Suna yin abin da ake kira da  ‘Taƙiyya,’ wato ƙudurce abu daban a zuci amma a baki ya bambanta.

Marubucin ya kawo hujjoji  bayyane a kan Auren Mut’a. Ya kuma bayyana wasu aƙidoji da ‘yan Shi’a  suke ƙaryatawa, a kan  abin da aka cewa suna yi; wanda ya tabbatar da suna yi, bisa hujjoji da ya kawo a cikin littafinsu ƙarara…

A gefe guda, marubucin ya yi nuni ga mu marubuta, da idan za mu rubuta littafi, to mu nemi ilimi. Domin marubuci ya nuna a shirye yake ga duk wanda ya ƙaryata cewa abin da ya faɗa a cikin littafin, da ya kawo hujja zai iya kare kansa. Daga karanta littafin za ka fahimci cewa marubucin bai yi rubutun kawai bisa ga ra’ayinsa ko son zuciyarsa ba. Sannan ya nuna cewa marubuta mu yi rubutu (littafi) da bincike, yadda ko bayan shekaru, za mu yi alfahari da shi.

A gaskiya littafin tamkar sadaƙatu jariya ce, domin ko da  bayan ba ya raye, marubucin zai rika sanun lada. Duk shekarun da littafin zai ɗauka, zai ci gaba da amfanar da al’umma.

Ba zan yawaita sharhi ba saboda littafin manyan malamai da manazarta sun yi sharhi a kansa, kasancewar littafin fitacce ne kuma sananne a duniyar makaranta. Littafin ya shiga lungu da saƙo na faɗin Najeriya.

Abin da Labarin Lttafin ya Ƙunsa:

Manyan taurari (Nana da Dandangi). Nana ɗaliba ce kuma budurwa. Tana zaune da iyayenta, ta faɗa soyayya da wani saurayi kyakkyawa. Zaƙin soyayya ya kai ta ga yin auren Mut’a da saurayi ɗan shi’a mai suna Ɗandangi. Shi kuwa ɗalibi ne ɗan ƙwalisa, wanda ya ja hankalin Nana da kalamai. Ta biye masa, daga ƙarshe ta shiga nadama da takaici. An rubuta littafin a tsari na wasan kwaikwayo.

Bisa al’adata l, idan na ɗan yi tsokaci ko sharhin littafi, ina yi wa marubuci tambayoyi da fatan marubuci zai amsa mun.

1-Me ya ba ka sha’awar rubuta littafin nan?

2-Shin akwai wanda ya ƙaryata abin da ka rubuta, har ma ya yi inkarin cewa zai ƙalubalence ka?

3-Ko ka taɓa faɗawa wannan aƙidar daga karshe ka fahimta ka fita? Don littafin ya nuna ka yi wa aƙidar farin sani. Ko kawai baiwa ce ta marubuci da Allah yake ba shi?

4-Ka taɓa gani zahiri a kan wasu sun yi wannan mummunan abin (Auren Mut’a)?

5-Amma wannan yana cikin Bakandamiyar littafin da ka rubuta?

Na gode.

Sanarwa:

Littafi yana cikin littattafai sama da goma da marubucin littafin ya ba ni, a ranar marubuta ta duniya a birnin Dutse, 31/12/2025.

__________

Amsoshin Tambayoyi:

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

                       •••••••

1-Me ya ba ka sha’awar rubuta littafin nan?

Amsa:

To, na farko dai Alhamdu lillahi. Allah cikin hukuncinsa ni marubuci ne, manazarci, sha’iri, ɗan jarida kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum. Na fara rubutu tun ina aji ɗaya na sakandare (1981). Bisa ga haka nakan yi rubutu kan duk wani al’amari da zai faɗakar da al’umma, musamman wanda hankalina ya ɗauku a kansa. Wannan shi ne dalili na farko da ya sanya hankalina ya kai kan wannan al’amari na ‘yan Shi’a kuma na yi nazari da bincike, na rubuta wannan littafi mai taken: TARKON MUT’A.

2-Shin akwai wanda ya ƙaryata a kan abin da ka rubuta, har ma ya yi inkarin cewa zai ƙalubalence ka?

Amsa:

Babu shakka an samu mutane da dama, musamman ma mabiya Shi’a da suka ƙaryata kuma suka ƙalubalance ni a baɗini da zahiri. Misali, akwai wani abokina ɗan Shi’a, ɗan jarida ne kuma marubuci mai suna Mu’awiyah amma daga bisani ya canja suna zuwa Muhammad Ibrahim (saboda ƙiyayyarsa ga Sayyiduna Mu’awiyah bn Abu Sufyan). Ya rubuta martani mai tsauri a kan littafin.

Haka kuma a zahiri, wasu ‘yan Shi’a a Malumfashi har taron addu’a suka yi, inda suka yanka kaji, suka tara garwashi suna kiran sunana suna tofawa a jikin duwatsu, suna jefawa a ciki. Sun yi wannan ƙulumboton wai da nufin su naƙasa lafiyata. Wannan lamari ya faru da gaske, domin ɗaya daga cikinsu ya shaida wa wani ɗan uwana wannan lamari, ya ce masa: “Nan da kwana uku, za ka ga abin da zai faru da ɗan uwanku, saboda ya taɓo mu.” Amma abin ikon Allah, babu abin da ya same ni.

Sanadiyyar littafin nan, an tsangwami ɗaya daga cikin ‘ya’yana da yake karatu a wata babbar makaranta. Wani malaminsu, wanda ɗan Shi’a ne, ya yi ta ba shi “Carry Over,” har sai da aka kore shi daga makarantar. Sai da aka turo mani da saƙon tes cewa, “yaronka wane yana da ƙoƙari, amma ba zai gama karatu a makarantar nan ba.” Nan ma dai haka lamarin ya kwaranye, yanzu sai labari.

Haka kuma an samu nazarin littafin a wasu jami’o’i na ƙasar nan. Misali, a Sashen Hausa na Jami’ar Jihar Kaduna, akwai ɗalibar da ta yi nazarin littafin a matsayin kundinta na samun digirin farko.

3-Ko ka taɓa faɗawa wannan aƙidar daga ƙarshe ka fahimta ka fita? Domin littafin ya nuna ka yi wa aƙidar farin sani, ko kawai baiwa ce ta marubuci da Allah yake ba shi?

Amsa:

A’a, ban taɓa shiga Shi’a ba. Abin da na sani shi ne, a shekarar 1983, ina aji uku a sakandare, nakan bibiyi gidan jaridar ‘Saƙon Musulunci’ da takwararta  ta Ingilishi, ‘The Message of Islam’ da ake wallafawa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A lokacin, duk wata sai an aiko mani da waɗannan mujallu kyauta, ta hanyar Post Office. Ba a daina aiko mani da mujallun nan ba, har sai da aka daina wallafa su a wajen 1990.

Haka kuma daga shekarar 1987 zuwa 1989, lokacin da nake karatu a CAS (College of Advanced Studies) Zaria, na kasance mai bin Sheikh Ibrahim Zakzaki a da’awarsa ta Muslim Brothers. Lokacin babu ma labarin Shi”a ko kaɗan. Zan iya tunawa, daga makarantarmu da ke Unguwar Gaskiya, ni da wasu abokaina, mukan taka a ƙasa har zuwa ABU Zaria, domin sauraren wa’azin Zakzaky.

Ban yi Shi’a ba, amma ina da abokai masu yawa da suke Shi’a. Lokacin da na zauna Kano, a matsayin Editan Shiyya (Zonal Editor) na Jaridar Aminiya, ina da wasu abokai biyu ‘yan Shi’a, Wakilan Jardar Almizan a Kano. Mun yi faɗi-tashi tare da su. Na ziyarci tarukan ‘yan Shi’a da yawa a Kano tare da su. Wannan ta ba ni dama na san abubuwa da yawa game da aƙidarsu. Ba su taɓa ɓoye mani matsayarsu ba game da Auren Mut’a.

Lokacin kuma da na ƙuduri aniyar rubuta wannan littafi, na yi bincike sosai game da wannan batu na Mut’a. Na nazarci littattafai da suka haɗa da Alƙur’ani mai girma, Sahih Bukhari da Sahih Muslim. Na nazarci littafin “Ɓacin Tafarkin ‘Yan Shi’a Da Aƙidojinsu” na Farfesa Umar Muhammad Labdo da kuma kusan dukkan littattafan da Farfesa Mansur Sakkwato ya wallafa game da ‘yan Shi’a na duniya baki ɗaya, ba wai na Najeriya kaɗai ba.

Haka kuma na samu nazarin wasu littattafai na ‘yan Shi’a, kamar babban littafin aƙidun Shi’a mai taken “Man La Yahduruhul Faƙih” na Ibnu Babawaihi Alkummi da littafin “Minhajus Sadiƙin” na Fatahallah Kashani da littafin “Kashful Asrari” na Sayyid Hussain Masawi. Akwai kuma littafin “Fuurul Kafi” na Kaulani da “Nahjul Balaga” na Shariff Alradi.

Sauran littattafai da suka yi mani jagora, sun haɗa da “Almusnad” na Imam Ahmad Bin Hanbal da kuma “Siyaru A’alamil Nubala” na Sheikh Zahabi. Haka kuma na karanta muƙalu da sauraren lakcoci daban-daban da suka shafi aƙidun Shi’a.

4-Ka taɓa gani zahiri a kan wasu sun yi wannan mummunar abin (Auren Mut’a)?

Amsa:

Kamar yadda na gaya maka, na yi tarayyar zumunci da abokantaka ta kusa da ‘yan Shi’a. Don haka daga cikinsu akwai mutum uku da na sani da suke yin irin wannan aure kuma suna sanar da ni. Cikin ukun, akwai marigayi Mu’awiyah (Muhammad Ibrahim), wanda har littafi ya rubuta mai suna “Na Yi Auren Mut’a.” Haka kuma, a dukkan musharaƙarsa da mu’amalarsa, bai taɓa ɓoye akidarsa ba. Hasali ma, a shafukansa na Soshalmidiya, ya sha bayyana cewa yana yin auren Mut’a. Ya sha gayyatar mutane, ya sha rubuta muƙaloli, yana fayyace fa’idoji da falalar auren, domin jan ra’ayin mutane da su riƙa yin wannan aure na Mut’a.

5-Amma wannan yana cikin Bakandamiyar littafin da ka rubuta?

Amsa:

A batun gaskiya, wannan littafin ba shi ne Bakandamiyata ba, duk da cewa ina alfahari da shi. Littafin ya jawo mani farin jini kuma na samu tsanin alaƙa da manyan mutane da manyan malaman addini a ƙasar nan. Sai dai duk da haka ina da littafin da nake kan rubutawa, wanda nake son wallafa shi idan Allah ya sa na cika shekara 60 a duniya, nan da shekara ɗaya da rabi mai zuwa, in sha Allah. Shi ne nake son ayyanawa a matsayin Bakandamiyata.

Na gode sosai da wannan sharhi naka da kuma waɗannan muhimman tambayoyi da suka ƙara mani wani ilimin na daban, game da wannan littafi. Allah saka da alheri. Ina yi maka fatan alheri.

_______________

Previous Post

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

Next Post

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

Related Posts

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido
Adabi

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

June 8, 2026
ALHAMDU LILLAH
Adabi

ALHAMDU LILLAH

May 15, 2026
Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
Adabi

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Next Post
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

ADC: The Wind of Change Has Come – Dr. Aminu Waziri

ADC: The Wind of Change Has Come – Dr. Aminu Waziri

July 7, 2025
Gwamnan Jigawa Ya Amso Walida Daga Hukumar DSS

Gwamnan Jigawa Ya Amso Walida Daga Hukumar DSS

February 26, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (7)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (7)

January 9, 2026
GOBARA TA TASHI A KASUWAR MADALLA

GOBARA TA TASHI A KASUWAR MADALLA

January 29, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido
  • Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji
  • Wasu Daga Manyan Ayyukan Sardauna Ga Al’ummar Arewa (1954-1966)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

June 8, 2026
Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

June 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.