Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
Daga Dr. Bukar Usman, OON

_______________
Da yardar Allah, na cika shekaru 83 a ranar 10 ga Disamba, 2025. Kamar yadda al’adarmu ta tanada, babu wani bikin shagali mai yawa a gidana. Abin da kawai na tuna a wannan rana shi ne, ni da matata Dupe muna tsaye a kicin da misalin ƙarfe 11:00 na safe, sai ta fara rera waƙar “Happy birthday…” cikin farin ciki, sannan ta bi da doguwar addu’a tana roƙon Allah Ya albarkace ni da lafiya da tsawon rai.
Daga baya, sauran mutanen gidana, Ruth da Victoria suka zo daban-daban, suka durƙusa suka gaishe ni tare da yi mini fatan murnar ranar haihuwa.
A cikin wannan rana, sai baƙi daga waje suka fara zuwa. Afeez Bello, mai aikin famfon ruwa (plumber) ɗinmu, ya zo da katin taya murna mai kyau. Bayan haka, Abdulrazak Yusuf, kafinta (carpenter) ɗinmu, shi ma ya zo da babban katin taya murna mai ado. Bai same ni a gida ba domin na fita kaɗan domin aski. Haka ma mai gyaran talabijin ɗinmu, Luka Yakubu, ya zo amma bai same ni ba. Ya kawo mini kyauta a cikin baƙin kwali, cike da kayan tunawa daban-daban, ciki har da littafin rubutu (diary), kofi na shayi, alƙalami mai tawaida (fountain pen), mahallin wuyan hannu (cufflink), abin riƙe mabuɗi (key holder) da kuma kunshin katunan gaisuwa, dukkaninsu da zanen sunana “Dr. Bukar.”
Tsohon jakadan Najeriya a Rasha da Belarus, kuma abokin zumunta na kusa, Ambasada A. Y. Shehu, ya zo min gaisuwa. Da ya zauna, ya fara da doguwar addu’a yana roƙon Allah ya ba ni lafiya da tsawon rai domin ci gaba da ayyukan alheri da nake yi. Bayan tafiyarsa, sai Janar L. P. Ngubane, wani abokin zumunta, shi ma ya zo. Ya zauna tare da ni muna hira muna tattauna al’amuran yau da kullum. Ya nuna damuwa kan rikicin ƙabilanci da ke faruwa a yankinsu na Jihar Adamawa, wanda ya haddasa asarar rayuka masu yawa. Ya faɗa mini cewa kawai ya zo ne domin yin gaisuwar da ya saba yi, bai san cewa ranar haihuwata ba ce. Sai ya taya ni murna da zuciya ɗaya. Wani abokin zumunta kuma, Sanda Galadima, ya kawo min kwanon “masa” tare da gutsattsarin kaji da aka soya. Dukkansu na yi musu godiya da farin cikin wannan zumunci da suka nuna mani.
A cikin ranar, na ci gaba da karɓar saƙonnin fatan alheri daga mutane da kamfanoni ta hanyoyi daban-daban: rubuce-rubucen yabo, saƙonnin waya, imel da kuma baki-da-baki. Ga wasu daga cikin waɗanda suka aiko da saƙonni tare da wuraren zamansu: Mohammed Alkali – Damaturu, Japh Nwosu – Abuja, Adamu Mohammed – Kano, Memunat Alli-Owe – Lagos, Ladu C. Gali – Abuja, Amb. Abdullahi Y. Shehu – Abuja, Moyo Olanipekun – Ibadan, Olabode Moses – Kaduna, Fatima Ibrahim Abba Gana – Abuja, Dr. Adaobi Nwoye – Enugu, Justice George Nnamani – Enugu, Busuyi Onabolu – Lagos, Bala Ibrahim Mohammed – Biu, Denja Abdullahi – Abuja, Cecilia Dabo – Jos, Bashir Yahuza Malumfashi – Abuja, Chartered Institute of Directors – Lagos, Catherine Nwosu – Lagos, Africa Prudential Plc – Lagos, Mohammed Umar Midala – Biu, Damcida Umar – Biu, Regina Ogechukwu Nwangele – Ireland, Kemi Ayelabola – Ireland, Khalid Imam – Kano, Michael Ayivor – Zaria, Hafsat Abimbola Usman – Spain, Halimat Folake Usman – San Francisco, California, Amurka, Abubakar Adam Ibrahim – Amurka, da Access Bank – Abuja.
Saƙonnin yabo sun haɗa da rubutattar waƙa daga Bashir Yahuza Malumfashi daga Abuja da kuma muƙala daga Khalid Imam daga Kano. Kimanin mako guda kafin ranar, Tijjani Garga daga Maiduguri, Jihar Borno, ya riga ya aiko da saƙon yabo. ’Ya’yana mata Halimat daga San Francisco, California, ta aiko da saƙon waya, yayin da Hafsat daga Barcelona, Spain, ta aiko da imel, dukkansu suna miƙa fatan alheri da addu’o’insu a gare ni.

Yayin da nake kiran wasu domin nuna godiya, sai na sake jin ana rera “happy birthday…” cikin farin ciki daga Cecilia Dabo daga Jos da Mrs. Catherine Nwosu da Memunat Alli-Owe daga Lagos da kuma Dr. Adaobi Nwoye daga Enugu.
Da daddare, na je ɗakin ɗaukar hoto (studio) domin yin hotuna. Matata Dupe ce ta kai ni tare da Ruth, wata ma’aikaciyar gidanmu da kuma ’yata Hadizat da ’yarta mai shekara ɗaya (jikata), Morayo. Dukansu sun yi haƙuri sun jira ni har na gama ɗaukar hotuna. Na yi amfani da damar wajen ɗaukar hoto tare da jikar tawa.
Da muka dawo gida, mun ci abincin Sinawa (Chinese food) da muka sayo daga gidan abinci. Bayan haka, matata Dupe ta zo wurina a falo ta ba ni wani abu da aka nannaɗe da kyau, tana cewa kyautarta ce a bikin ranar haihuwata. ’Yata Zara tana nan. Na roƙe ta ta taimaka ta buɗe kyautar. Tufafi ne da za a ɗinka shi ya zama jamfa. Na gode wa matata ƙwarai da wannan kyautar ta alheri da taya murna.
Zara, wadda ta cika shekaru 13 a wannan watan, ta dawo daga makarantar kwana (boarding school) a wannan maraice. Abin ban sha’awa, tun kafin ta sauko daga motar mamanta, da ta hango ni a cikin gida, sai ta ce “happy birthday.” Na amsa cikin raha, na ce: “Ba za ki fara saukowa daga mota ba ne?”
Saƙonnin fatan alheri sun ci gaba washegari daga Rukayya S. Bayero a Abuja; Ambasada Segun Apata daga Atlanta, Georgia, a Amurka; Sumaila Umaisha daga Abuja; Hassana Ali daga Abuja da Joseph Adonoo daga Lagos. Rev. Samuel Osivwemu ya aiko min da kyautar rago. A rana ta uku kuma, an karɓi saƙonni daga Salamatu Sule da Farfesa Razinat T. Mohammed, duk daga Abuja. Haka kuma, Funmilayo Theresa Akinwande daga Ibadan ta aiko saƙo a ranar 13 ga Disamba, 2025, sannan Deborah C. Uzoma daga Owerri ta biyo baya washegari. A wannan rana kuma, tawagar ƙungiyar Bura Women Development Association (BUWDA) ta kawo mini ziyara tare da gabatar da kambin zayyana (roll-up banner), wanda ke ɗauke da kyakkyawan rubutun jinjina, addu’a da fatan alheri a gare ni.

To, a takaice, wannan shi ne labarina game da yadda na yi bikin cikar shekaru 83 na haihuwa, cikin godiya ga Allah bisa dukkan ni’imominsa. Cike nake da godiya da farin ciki, kuma da wannan farin ciki nake sake wallafa saƙonnin fatan alheri da rubuce-rubucen yabo.

Tabbas, ranar ba ta ƙare ba tare da samun saƙonnin fatan alheri masu yawa daga sassa daban-daban na duniya ba. Ga ɗaya daga cikinsu, daga Mohammed Alkali:
“Fatan alheri a ranar haihuwa. Barka da safiya, Mr. President Sir. Yayin da muke bikin ranar haihuwarka, ina gode wa Allah da Ya sanya ka cikin rayuwata. Allah Ya cika ranka da farin ciki, tunani mai zurfi, da fatan alheri ga shekarar da ke gaba kuma ya ci gaba da yi maka albarka, ya kuma kare ka a dukkan kwanakin rayuwarka. Ranka ya daɗe, ka huta lafiya da alheri.”
_______________
Dr. Bukar Usman, tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa kuma Shugaban Ƙungiyar Bunƙasa Al’adun Gargajiya ta Najeriya (Nigerian Folklore Society) a halin yanzu, ya yi bikin cikar shekarunsa 83 a ranar 10-12-2025 a Abuja.













