• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Wawason Dukiyar Al’umma: Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Ba’asin Tsohon Gwamna Matawalle

webmaster by webmaster
June 3, 2023
in Babban Labari
0
Wawason Dukiyar Al’umma: Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Ba’asin Tsohon Gwamna Matawalle
19
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Gwamnatin Jihar Zamfara a ƙarƙashin shugabancin sabon Gwamna, Alhaji Dauda Lawal, ta bayyana wata sanarwa da Jam’iyyar APC reshen Zamfara ta fitar, a matsayin shisshigi don neman suna daga jam’iyyar da ta gaza farfaɗowa daga magagin faɗuwar zaɓe.

 

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026

A wata sanarwar manema labarai da Jami’in Watsa Labari na Gwamnan Jihar Zamfara, Malam Suleiman Bala Idris ya fitar, an bayyana cewa:

 

“Jam’iyyar APC ta fidda sanarwar ce tana ƙalubalantar Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa zancen da ya yi na cewa tsohon Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya kwashe tare handame motocin gwamnati da sauran abubuwan amfani a gidan gwamnatin da ke Gusau.”

 

Takardar ta ce sumbatun da APC ke yi, ba komi ba ne face ƙoƙarin ba da kariya ga handama da badaƙalar da Matawalle ya aikata. Wanda wannan ke nuna irin halin da jam’iyyar ta APC ke ciki.

 

“Gwamnatinmu tana nan kan ƙudurinta na ganin ta cika alƙawurran da ta ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe, wanda a ciki har da batun bin diddigin irin ɓarnar da aka aikata a gwamnatance don ƙwato wa jama’a haƙƙinsu.” In ji Bala Idris.

 

Ya ci gaba da cewa “wannan sanarwar ta rashin kan gado da APC ta fitar, sun yi ne da zimmar ɗauke mana hankali daga ayyukan da muka fara don tsamo Zamfara daga halin da take ciki. Lokacinmu yana da tsada, ba za mu tsaya ɓata shi wurin musayar yawu da jam’iyyar da ta kwashe shekaru huɗu kan mulki ba tare da ta yi wa jama’a komai ba, sai dai ma tulin almundahana da waushe asusun jiha.

 

“Muna da hujja da alƙalumma da suka fallasa irin ta’asar Matawalle. Amma saboda rashin ta-ido shi ne har APC reshen Zamfara ke da bakin magana. Tsohon Gwamna Matawalle ya bayar da kwangilar sayo motocin gwamnati kan kuɗi Naira Biliyan 1,149,800,000.00; wanda aka ba kamfanin Hafkhad Properties and Facilities Management Nig. LTD.

 

“Matawalle ya biya waɗannan maƙudan kuɗaɗe ne domin a sayo motocin gwamnati kamar haka: Toyota Lexus VIP 2021 (me sulke); Toyota Land Cruiser VIP 2021 (mai sulke); Toyota Prado V6 2021; Toyota Prado V4 2021; Peageot 2021; Toyota Hilux 2021; Toyota Land Cruiser 2021 (mai sulke); da kuma Toyota Lexus 2021.”

 

A ci gaba da bayyana yadda aka wawashe kuɗaɗen, takardar ta ci gaba da lissafi. “A ranar 4 ga watan Oktoba 2021, tsohon gwamna ya biya Naira 484, 512, 500.00 ga kamfanin MUSACO, domin su kawo motoci uku ƙirar Jeep masu sulke; haka nan an sake ba shi aikin kawo motoci ƙirar Prado Jeep da Land Cruiser guda bakwai akan Naira 459, 995, 000.00; sai kuma aikin kawo motocin Toyota Hilux guda bakwai akan kuɗi Naira 228, 830, 000.00.

 

“A ranar 19 ga watan Mayun 2021, tsohon gwamna Matawalle ya biya naira miliyan 61, 200, 000.00 ga kamfanin TK Global Services domin a sayo motoci ƙirar Peugeot 406 guda 30. Haka kuma a ranar 15 ga watan Disamba 2021, Matawalle ya ba kamfanin Nadeen Butta aikin sayo mota ƙirar Land Cruiser (mai sulke) kan Naira Miliyan 130, 000, 000.00.

 

“A ranar 26 ga watan Fabrairu 2022, tsohon gwamna ya ba kamfanin Dapiyau B. Linus aikin sayo motoci biyu ƙirar Land Cruiser Jeep kan kuɗi Naira miliyan 160, 000, 000.00; a ranar 20 ga watan Maris 2022, tsohon gwamnan ya sake biyan MUSACO naira miliyan 120, 000, 000.00 aikin kawo motoci guda uku, waɗanda za a ajiye a ofishin mataimakin gwamna.

 

Mai magana da yawun gwamnan ya ƙarkare sanarwarsa da cewa: “Tuni mun tura wa tsohon Gwamna Matawalle takardar neman bahasi kan motocin da aka kwashi biliyoyi daga asusun gwamnati aka sayo su. mun ba shi wa’adin kwana biyar.”

 

Taskar Gizago ta yi ƙoƙarin jin ta bakin tsohon Gwamna Matawalle ko wani makusancinsa, sai dai abin ya ci tura har zuwa haɗa rahoton nan.

Previous Post

Kuskure Kan Ingilishi: Wane Ne Ke Son Wulaƙanta Gwamnan Kano?

Next Post

Rusau A Kano: Ina Bayan Gwamna Abba Gida-Gida

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Babban Labari

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume
Babban Labari

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel
Babban Labari

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026
Next Post
Rusau A Kano: Ina Bayan Gwamna Abba Gida-Gida

Rusau A Kano: Ina Bayan Gwamna Abba Gida-Gida

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

July 14, 2023
DAY 3 FESTIVAL OF AUTHORS KADUNA 2024

DAY 3 FESTIVAL OF AUTHORS KADUNA 2024

October 25, 2024
Ali Nuhu Ya Shiga Rukunin Fitattun Taurarin Fim 100 Na Afirka

Ali Nuhu Ya Shiga Rukunin Fitattun Taurarin Fim 100 Na Afirka

July 9, 2023
NAJERIYA A 65: MU SAKE DUBAWA

NAJERIYA A 65: MU SAKE DUBAWA

October 1, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.