• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, July 27, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Addini

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi

NASIHA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 29, 2025
in Addini
0
Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi

A sama, marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi. A ƙasa, Malam Baffa Hotoro Kano

42
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRIYYA

BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRIYYA

June 16, 2026
Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
A sama, marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi. A ƙasa, Malam Baffa Hotoro Kano


                              •••••••
Akwai takaici da ƙunar zuciya, mutum ya ga abin da bai kamata ba daga hannun wanda ya kamata a ce ya san ya kamata.

Na ci karo da wani faifan bidiyo a Soshalmidiya, inda na ga matashin malamin Musulunci, Baffa Hotoro Kano yana kausasa harshe, cikin izzar rashin ta ido, yana antaya antayayyun kalamai a kan marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi. Ba sai na maimaita kalaman ba a nan saboda muninsu kuma ina da tabbacin mutane da dama sun ji kalaman nasa a wannan saha da waninta.

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Haba Malam, don Allah ina ilimin naka yake, ina ka manto Sunnar Manzon Allah (saw)? Maganar gaskiya ka ci amanar ilimi kuma ka cutar da Sunnar Manzon Allah (saw). Ya kamata ka gaggauta tuba, ka gaggauta fitowa fili ka nemi gafarar iyalan marigayi, ka nemi gafarar miliyoyin Musulmi da suka ji ba daɗi daga munanan kalamanka.

Malam Hotoro, na san ka san da umurnin da ke cewa: “Ka tunatar, tunatarwa tana amfanar muminai.” Don haka ina kyautata maka zaton cewa kai mumini ne.

Bisa ga haka, bari in tunatar da kai wannan hadisin na Manzon Allah (saw) daga Sahih Bukhari, mai lamba 1393, wanda ya yi hani da tozarta mamata: “Kada ku zagi matattu, domin sun riga sun kai ga abin da suka aikata.”

Ko ba komai, marigayi mahaddacin Alkur’ani ne mai girma. Ya karanta kuma ya karantar da shi. Ko ba komai, marigayi ya yi tsufan da ya yi kakan-kaka da kai kuma Allah ya fitar masa da furfura, wacce Manzon Allah (saw) ya ce a girmama mai ita. Ko don waɗannan dalilai kaɗai, bai kamata ka kausasa harshe a kansa ba. Da ma shiru ka yi da bakinka, wallahi da ya fi alheri.

Malam Baffa Hotoro, ina yi maka da ni kaina da dukkan al’ummar Musulmi nasiha. Mu ji tsoron Allah, mu kiyaye harshenmu, mu kiyaye amanar ilimi, mu kiyaye tozarta bayin Allah.

Ya Allah ka yi mana uzuri, ka kawar da Shaiɗan daga hanyarmu, ka yafe mana zububbanmu. Amin-Summa-Amin!
_______________

Previous Post

Global Standards and Regional Realities: The Evolution of Anti-Money Laundering… Under Review

Next Post

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

Related Posts

BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRIYYA
Addini

BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRIYYA

June 16, 2026
Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
Addini

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba
Addini

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Next Post
Kada Ka Karaya Da Rayuwa

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

PSG DA ARSENAL: ZARATAN ‘YAN WASAN DA ZA SU BA DA MAMAKI

PSG DA ARSENAL: ZARATAN ‘YAN WASAN DA ZA SU BA DA MAMAKI

April 29, 2025
SUBHANALLAHI: ‘Yan Sanda Sun Kulle Danladi Haruna

SUBHANALLAHI: ‘Yan Sanda Sun Kulle Danladi Haruna

October 7, 2023
SASSANYAN AMINCI (1)

SASSANYAN AMINCI (1)

September 4, 2025
Neman Hanyar Gaskiya A Addini

Neman Hanyar Gaskiya A Addini

October 17, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.