• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, August 8, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

SASSANYAN AMINCI (1)

Diwanin Bashir Yahuza Malumfashi

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 4, 2025
in Adabi
0
SASSANYAN AMINCI (1)

Diwanin Bashir Yahuza Malumfashi (1)

19
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

SASSANYAN AMINCI (1)
(Diwanin Bashir Yahuza Malumfashi)

Diwanin Bashir Yahuza Malumfashi (1)

                          __________
Gabatarwa:
A yau Alhamis, 11 ga Rabi’ul Auwal, 1447 Hijiriyya, wacce ta yi daidai da 04 ga Satumba, 2025 Miladiyya. A yau muke murnar zagayowar ranar da aka haifi Manzon Allah, Muhammadu (saw). Daga yau za mu fara wallafa wannan diwani, mai ƙunshe da baitoci dubu ɗaya cur, na begensa – Sallallahu Alaihi Wasallam.

Related posts

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

Nazari Da Sharhin Littafin Tarihin Garin Lassa

July 18, 2026
Maryam ‘Yar Aljanna (2)

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026

Akwai bayin Allah da suke taimakawa domin ganin nasarar an wallafa wannan Diwani, saboda ƙaunarsu ga Fiyayyen Halitta. Don haka, muuna addu’a ta musamman ga waɗannan bayin Allah (Masoya Manzon Allah – Saw), da suke taimaka wajen wannan aiki:

1-Alhaji Jibrin Sama’ila (Jibson).
2-Injiniya Tukur Tingilin
3-Malam Labiru Musa Kafur
4-Malam Haruna Musa Rugoji
5-Dr. Aminu Waziri
6-Abdulaziz Abdulaziz
7-Zainab Ahmad Mohammed

Allah ya saka maku da mafificin alheri, ya ƙara mana ƙaunar Manzonsa (saw), ya sa muna cikin cetonsa, Amin!

GUDUNMOWA:
Al’ummar Allah, ga duk mai son saka jarinsa a wannan aiki, ƙofa a buɗe take. A tuntuɓi Bashir Yahuza Malumfashi a wannan layin waya:
+234 8065576011
_______________

1
Bismillah na ɗau niyya,
A cikin ladabi da biyayya,
Zan tsara baitin soyayya,
Ga halittar Allah fiyayya,
Ban ɗaura yin wasa ba.

2
Ya Allah ka ba ni basira,
Ka raba mu da dukkan asara,
Zan yabon mai hana fitsara,
Sha yabo tuli ya sahara,
Shugaban muƙami babba.

3
Assalamu alaika Nabiyyu,
Shugaban dukkan anbiya’u,
Alhashimi, Ƙuraishiyyu,
Kai ne badadin Hayyu,
Kai ke da haske babba.

4
A halittu ba ka da tamka,
Kyakkyawa ko ba wanka,
Babban danni mai tanka,
Girmanka ya wuce jinka,
Sirri na Allah babba.

5
Kai Maliya ka wuce gulbi,
Tsarki gare ka a ƙalbi,
Aikinka gyaran ƙalbi,
Tauraro ka wuce halbi,
Shugaba kake ba wai ba.

6
Manzo muna ƙaunarka,
Muna ta ƙin mai ƙinka,
Mun gane duk girmanka,
Mun san da duk tsarkinka,
Mai sonka ba zai taɓe ba.

7
Ɗan Amina ka wuce karo,
Ran Litinin kag gangaro,
Babu kuka ba wani ɓaro,
Sai murmushi ka ƙaro,
Murna ga dangi babba.

8
Na Khadijah babban gwarzo,
Ga baituka naka murzo
Bisa izza duka naka furzo,
Maƙiyanka duk zan gurzo,
Bauta nake ba wai ba.

9
Ka fi ruwan sanyi a bazara,
Kyauta wurinka ba tazara,
Kyan ɗaki sai da azara,
Murmushi kullum ka zizara,
Kai ke da hairi babba.

10
Ka fi zuma zaƙi ko madara,
Kai kake izza ga mahara,
Ja’irai sun zam a makara,
Ba su da riba sai dai takura,
Kai ke da turke babba.

11
Haƙuri ka zarce wa damo,
Ba ka murna da ƙanƙamo,
Mai ƙaunarka ya kandamo,
Alheri za ya fantamo,
Ba zai rasa yin dace ba.
__________
© Bashir Yahuza Malumfashi,
11-03-1447 (Hijiriyya)
03-09-2025 (Miladiyya)

(Za mu ci gaba)

Previous Post

BAKIN JAƁA (2) (Labarin Cin Amana)

Next Post

SASSANYAN AMINCI (2)

Related Posts

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage
Adabi

Nazari Da Sharhin Littafin Tarihin Garin Lassa

July 18, 2026
Maryam ‘Yar Aljanna (2)
Adabi

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026
Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa
Adabi

Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

June 21, 2026
Next Post
SASSANYAN AMINCI (2)

SASSANYAN AMINCI (2)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

RAMADAN KARIM: 02-1447

RAMADAN KARIM: 02-1447

February 19, 2026
Gargaɗin Amurka kan Nijeriya na tada hankulan jama’a, kuma ya na yin illa ga tattalin arzikin ƙasa – Minista

Gargaɗin Amurka kan Nijeriya na tada hankulan jama’a, kuma ya na yin illa ga tattalin arzikin ƙasa – Minista

November 8, 2023
ALLAH YA JI ƘAN ASP ALHAJI ƊAHIRU

ALLAH YA JI ƘAN ASP ALHAJI ƊAHIRU

September 24, 2025
True Christianity: A Powerful Insight

True Christianity: A Powerful Insight

September 24, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Hukuma Ta Kafa Sabbin Sassa Domin Bunƙasa Al’umma A Jihar Katsina
  • Garin Zango Ya Samu Babban Asibiti na Farko A Tarihi
  • Zango Local Government Enjoys First-Ever General Hospital

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Hukuma Ta Kafa Sabbin Sassa Domin Bunƙasa Al’umma A Jihar Katsina

Hukuma Ta Kafa Sabbin Sassa Domin Bunƙasa Al’umma A Jihar Katsina

August 8, 2026
Garin Zango Ya Samu Babban Asibiti na Farko A Tarihi

Garin Zango Ya Samu Babban Asibiti na Farko A Tarihi

August 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.