SASSANYAN AMINCI (7)
Diwanin
Bashir Yahuza Malumfashi

_______________
36
Dole ne fa mu zam imani,
Komai ya zam mizani,
Shi ya aiko dukkan manzanni,
Ko’ina kuma kowane zamani,
Ko a daji an san gamba.
37
Kafin zuwansa Muhammadu,
Mustapha Manzo mujaddadu,
Nurun hasken hana hassadu,
Mai ƙin sa shi yai kasadu,
Ya bar Juma’a tun Laraba.
38
Mu dai duka mun imani,
Da manzannin duka zamani,
Babu shirka babu gunaguni,
Daga Adamu har shi tsani,
Muhammadu Manzo babba.
39
Shikashikan Musulunci,
Biyar ne babu ƙunci,
Mu duba mu yi nazarci,
Shi Allah ba ya barci,
Mahaliccin yaro da babba.
40
Na ɗaya Kalmar Shahada,
Dole ne ka zam mai hadda,
Ba abin bauta yau ko da,
Manzonmu ne Nurulhuda,
Mujtapha jigo ne babba.
(Za Mu Ci Gaba)
_______________
Akwai bayin Allah da suke taimakawa domin ganin nasarar an wallafa wannan Diwani, saboda ƙaunarsu ga Fiyayyen Halitta. Don haka, muna addu’a ta musamman ga waɗannan bayin Allah (Masoya Manzon Allah – Saw), da suke taimakawa wajen wannan aiki:
1-Alhaji Jibrin Sama’ila (Jibson).
2-Injiniya Muntari Sagir
3-Injiniya Tukur Tingilin.
4-Malam Labiru Musa Ƙafur.
5-Malam Haruna Musa Rugoji.
6-Dr. Aminu Waziri.
7-Abdul’aziz Abdul’aziz
8-Zainab Ahmad Mohammed.
9-Alhaji Sa’idu Sabi’u Mahuta.
Allah ya saka maku da mafificin alheri, ya ƙara mana ƙaunar Manzonsa (saw), ya sa muna cikin cetonsa, Amin!
GUDUNMOWA:
Haka kuma, ƙofa a buɗe take ga dukkan al’umma masoya Manzon Allah, ga duk mai son saka jarinsa a wannan aiki, domin tarayya cikin lada, sai a tuntuɓi Bashir Yahuza Malumfashi a wannan layin waya, kira ko Whattsap: 08065576011
Allah sa mu dace Amin!
_______________













