• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, August 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Muhimmanci Da Tasirin Biyayya Ga Ubangida

MUƘALA

Bukar Usman, OON by Bukar Usman, OON
August 25, 2025
in Adabi
0
COMMENDATION: Essence of Loyalty to a Principal

Daga hagu, Dr. Bukar Usman ne, sai littafin da kuma marubucinsa, Malam Garba Shehu

23
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Muhimmanci Da Tasirin Biyayya Ga Ubangida

Daga Bukar Usman

Related posts

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

August 22, 2026
Malam Ɗan Masani

Malam Ɗan Masani

August 20, 2026
Daga hagu, Dr. Bukar Usman ne, sai littafin da kuma marubucinsa, Malam Garba Shehu

 

•••••••

Ɗan uwana Malam Garba Shehu,

Na rubuto wannan taƙaitaccen tsokaci ne, domin in bayyana godiyata ta musamman, bisa ziyarar da kuka kawo mani, kai da abokinka Malam Idris Ado Baba Nabegu a kwanakin baya; inda har kuka kawo mani sabon littafinka mai take ‘According to the President’ (Venturion, 2025). Lallai wannan babban karimci ne kuka nuna mani.

Littafin ya kasance abin sha’awa da daɗin karatu. Ɗan kaɗan da na fahimta daga cikinsa shi ne, yadda ka tsaya tsayin daka wajen yi wa iyayen gidanka hidima. Na farko, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da dangantakarsa da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da sauran abokai. Na biyu kuma, ka yi iya bakin ƙoƙarinka wajen bayyana ƙimar ubangidanka na ƙarshe, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari – a lokacin mulki da bayan barinsa. Ka kare gaskiyarsa da sahihancin shugabancinsa har zuwa ƙarshe.

Kodayake ba tarihin rayuwarka kai tsaye ka rubuta a littafin ba, ka bayyana wasu sassa na rayuwarka a taƙaice, cikin tawali’u. Ka nuna yadda ka taso a rayuwa, a matsayin mahaifinka direba. Ka samu ilimin boko kuma ka ɗauki mataki tun da wuri wajen zaɓar aikin da kake so a rayuwa, kuma ka tsaya a kansa bisa tarbiyyar da ka samu daga halaye nagari abin koyi; irin na marigayi Malam Aminu Kano – wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare muradun talakawa.

Ka samu amincewa da amana daga iyayen gidanka, waɗanda ka yi wa hidima cikin tsantsar sadaukarwa tare da amfani da dabaru da hikimomin da ka koya a fagen aikin jarida da sadarwa. A cikin wannan aiki, ka yi haɗin kai da abokan aikinka cikin zumunci da kyakkyawar alaƙa.

Ba shakka, masu aikin jarida da hulɗar jama’a, ko waɗanda ke sha’awar yin karatu a waɗannan fannoni, suna da abubuwa masu yawa da za su koya daga wannan littafi, domin ka fayyace irin ƙalubalen da ake iya fuskanta a fagen aiki da kuma muhimmancin lura da su domin samun nasara.

Haƙiƙa, akwai haɗurra ko ƙalubalen aikin da kan iya kai mutum zuwa kurkuku, waɗanda dole ne mutum ya shirya wa fuskantarsu, musamman idan ya tsaya kan gaskiya da adalci a aikin nasa.

A aikin jarida, halayyar riƙe sirri, hanyoyi da hikimomin isar da saƙo domin kare mutumci suna da yawa. A zahiri, irin waɗannan hikimomi sun haɗa da fahimtar ƙarfi da tasirin kafafen watsa labarai, kula da muhimman bayanan sirri, karewa da ɓoye kafofin samun bayanai da fahimtar bambanci tsakanin “yaɗa labarai” da “sadarwa.” Haka ma, akwai fahimtar yadda za a kwantar da rikice-rikice, sanin makamar hulɗa da jama’a, kasancewa a iya samun mutum da ƙwarewa wajen iya tsarawa da aika saƙo. Sauran sun haɗa da natsuwa, cancanta, daidaito, gaskiya, tsantseni, adalci da tsayawa kan gaskiya da sauransu da dama.

Tabbas al’amarin a bayyane, cewa Ubangidanka na ƙarshe, Shugaba Buhari, kamar yadda ya ce, ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen yi wa ƙasa hidima daidai iyawarsa kuma cikin sadaukarwa. Haka ma za a iya cewa kai ma ka yi iya bakin ƙoƙarinka a fagen aikin jarida da sadarwa, wajen yi wa ubangidan naka da ƙasar nan hidima. Ka zama abin alfahari, wanda ya cancanci girmamawa daga abokan aikinka, ganin yadda ka gudanar da aiki cikin ƙwarewa, ta yadda hatta su iyayen gidan naka da sauran jama’a suka yaba. Ina taya ka murna ƙwarai!

Ina yi maka fatan alheri a harkokinka na rayuwa, musamman a fagen aikin jarida da sauran sabgogi.
__________
Bukar Usman, OON, tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.

Previous Post

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (7)

Next Post

GASAR RUBUTUN HAUSA TA GIDAUNIYAR ZANNA/WALI (2025)

Related Posts

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu
Adabi

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

August 22, 2026
Malam Ɗan Masani
Adabi

Malam Ɗan Masani

August 20, 2026
Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage
Adabi

Nazari Da Sharhin Littafin Tarihin Garin Lassa

July 18, 2026
Next Post
GASAR RUBUTUN HAUSA TA GIDAUNIYAR ZANNA/WALI (2025)

GASAR RUBUTUN HAUSA TA GIDAUNIYAR ZANNA/WALI (2025)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

KWANKWASO BAI CIKIN WAƊANDA SUKA KAFA APC

KWANKWASO BAI CIKIN WAƊANDA SUKA KAFA APC

September 22, 2025
KAMUN LUDAYIN JEMAGE

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

August 5, 2023
AIKIN JIN ƘAI: Isma’eel Jauro Ya Shiga Kundin Tarihi Na Duniya

AIKIN JIN ƘAI: Isma’eel Jauro Ya Shiga Kundin Tarihi Na Duniya

September 26, 2023
Huɗubar Limamin Masallacin Eriya Malumfashi

Huɗubar Limamin Masallacin Eriya Malumfashi

June 30, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)
  • Professor Bello Sa’idu: The Demise of Literary Icon
  • Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)

Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)

August 24, 2026
Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Professor Bello Sa’idu: The Demise of Literary Icon

August 23, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.