• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (7)

RAHOTON MUSAMMAN

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 25, 2025
in Gizago
0
TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (7)

Alhaji Jibrin Sama'ila (Jinsin)

21
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (7)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)

January 13, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (7)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (7)

January 9, 2026
Alhaji Jibrin Sama’ila (Jinsin)

 

•••••••

Jama’a masu bibiyar wannan rahoto mai kama da muƙala, wannan shi ne rahoto kashi na 7, dangane da wannan babban taro da aka gudanar na Malumfashi Facebook Connect. Idan ba mu mance ba, an gudanar da taron ne a ranar Lahadi, 12-12-1446 (Hijiriyya), 08-06-2025 (Miladiyya).

A wannan rahoto, kamar yadda muka bayyana a ƙarshen kashi na 6, cewa a yau za mu tattauna ne game da Alhaji Jibrin Sama’ila (Jibson), wanda shi ma ya kasance cikin zaratan mutanen da aka karrama da kambi, a yayin taron.

√ Wane Ne Jibrin Sama’ila (Jibson)?

Babu shakka Allah ya albarka Malumfashi da zaratan mutane masu kishi, waɗanda kuma Allah ya azurta da dukiya mai albarka tun suna da ƙuruciya. Alhaji Jibrin, kamar abokinsa Injiniya Muntari Sagir, shi ma matashin attajiri ne, wanda dukiyarsa ke amfanar al’ummar Malumfashi da kewaye.

Alhaji Jibrin Sama’ila, Shugaban Kamfanin Nasaka/Jibson Investment

A takaice dai, an haifi Jibrin Jibson a Unguwar Sodangi, Malumfashi a shekarar 1980. Ya yi dukkan karatunsa na firamare da sakandare, duk a Malumfashi. Daga nan ne ya shiga gwagwarmayar neman abin rayuwa.

Jibson ya taso cikin ƙwaƙuduba da faɗi tashin neman na kansa. Mutum ne mai ƙoƙarin nema, tun yana ƙarami. Ya yi ayyuka da sana’o’i iri daban-daban. Kamar yadda bincike ya tabbatar, ya taɓa yankar ciyawar dabbobi yana sayarwa. Akwai lokacin da ya riƙa shiga dazukan Malumfashi, yana saro itace, yana sayarwa.

Ya yi sana’o’i iri-iri, duk domin ya rufa wa kansa asiri a rayuwa. Waɗannan kuwa sun haɗa da sana’ar sayar da fetur da dizal a bakin titi. Ya yi sana’ar ruwan leda da yogot. Allah ya tarfa wa nemansa albarka, inda a halin yanzu yake da kamfanin Nasaka/Jibson Investment. A ƙarƙashin kamfanin, yana da gidajen mai, yana noman zamani, kamar kuma yadda yake gudanar da kwangilar gine-gine da sauransu.

√ Abin Da Ya Sa Aka Karrama Shi:

A wannan taro na Malumfashi Facebook Connect, an zaɓi mutane ne masu mutunci, masu amfanar da al’umma, aka karrama su. Alhaji Jibrin Jibson, babu shakka ya cancanci wannan karramawa, kamar sauran waɗanda aka karrama a ranar. Dalili kuwa shi ne, ta hanyar sana’arsa, ya yi sanadiyyar koya wa matasan Malumfashi sana’o’in dogaro da kansu. Ya koya masu cewa su tashi su nemi na kansu cikin ƙoƙari da jajircewa.

Ta fannin taimakon al’umma, musamman ma raunana da mabuƙata, Jibson a gaba-gaba yake. Yana da zumunci da taimakon ‘yan uwa da abokai. ‘Yan uwansa na jini da abokansa su ne manyan shaidu. Duk wani da ya rayu ko yake kan rayuwa a Unguwar Sodangi Malumfashi, zai kasance mai shaidar alheri ga Jibson. Mutum ne shi kuma mai ƙanƙan da kai – ba ya da girman kai ko toƙabo da dukiyar da Allah ya ba shi. Haka kuma ba ya yayata kyauta ko taimakon da yake wa mutane.

Jibrin Jibson, a yayin da ake karrama shi a yayin taron Malumfashi Facebook Connect

Wani babban al’amari game da shi kuma shi ne – Jibson mutum ne mai kishin addini. Taimakon masallatai da masallata da malaman addini, halinsa ne. Akwai makarantar islamiyya mai suna HIDAYA, a Unguwar Sodangi Malumfashi, a duk lokacin da aka zo bikin yaye ɗalibai, shi ke saya masu sabbin suturu, maza da mata. Wani lokacin ana yaye ɗaliban da suka kai 100 ko sama da haka.

√ Ƙarin Bayani:

A wata ganawa da na yi da shi, kwana biyu da kammala taron nan, na tambaye shi cewa, shin mene ne yake ba shi karsashi da ƙwarin gwiwar taimakon al’umma? Ya amsa da cewa:

“Maganar gaskiya, babban abin da ke mani ƙaimi kuma nake son taimakon mabuƙata shi ne, na taso cikin wahala, na ɗanɗani raɗaɗin talauci. Kan haka na san irin raɗaɗin da mabuƙata ke ciki. Dalili ke nan, idan na wayi gari ba tare da na taimaka wa mabuƙata ba, ba na jin daɗi.”

Jibson ya ƙara da cewa: “Na yi imani da Allah, cewa shi ke bayarwa kuma shi ke hanawa. Ni, Allah ya ba ni kuma shi ya ce yana son masu taimakon bayinsa. Dalili ke nan ya sa nake bayarwa kuma ina ganin falala da buɗi daga Allah, a sakamakon wannan taimako da nake bayarwa ga mabuƙata.

Daga Hagu: Injiniya Muntari Sagir ne, tare da Alhaji Jibrin Jibson a zauren taron Malumfashi Facebook Connect

Jama’a, wannan shi ne Alhaji Jibrin Sama’ila (Jibson) a taƙaice. Idan Allah ya kai mu rahoto na gaba, kashi na 8, za mu kawo bayani game da Dr. Injiniya Tukur Hassan Tingilin, wanda shi ma aka karrama a yayin wannan taro na Malumfashi Facebook Connect.
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago a intanet

Previous Post

COMMENDATION: Essence of Loyalty to a Principal

Next Post

Muhimmanci Da Tasirin Biyayya Ga Ubangida

Related Posts

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)

January 13, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (7)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (7)

January 9, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (6)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (6)

January 6, 2026
Next Post
COMMENDATION: Essence of Loyalty to a Principal

Muhimmanci Da Tasirin Biyayya Ga Ubangida

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Auren Al-Amin Ciroma Da Wasila Isma’il: Kira Na Musamman Ga Dattawan Kannywood

Auren Al-Amin Ciroma Da Wasila Isma’il: Kira Na Musamman Ga Dattawan Kannywood

July 6, 2023
Shekara 3 Baya: Tunawa Da Majidaɗin Galadiman Katsina

Shekara 3 Baya: Tunawa Da Majidaɗin Galadiman Katsina

June 8, 2023
Re: SARAUTA TUSSLE: The Debacle in Kano State

Re: SARAUTA TUSSLE: The Debacle in Kano State

June 1, 2024
FAƊA DA ‘YAN TA’ADDA: Malam Dikko Kada Ka Shiga Daji – Abdullahi Mahuta

FAƊA DA ‘YAN TA’ADDA: Malam Dikko Kada Ka Shiga Daji – Abdullahi Mahuta

October 16, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.