• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Jajirtataccen Jigo A Fagen Samar Da Nagartaccen Shugabanci: Gabatarwar Littafin Tarihin Dokta Adegoroye

GABATARWAR LITTAFI

Bukar Usman, OON by Bukar Usman, OON
June 30, 2025
in Adabi
0

Hagu-Dama: Marubucin Littafin, Dr. Goke Adegoroye, Bangon Littafin da kuma Dr. Bukar Usman

42
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Jajirtataccen Jigo A Fagen Samar Da Nagartaccen Shugabanci: Gabatarwar Littafin Tarihin Dokta Adegoroye

Daga Dokta Bukar Usman

Related posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Hagu-Dama: Marubucin Littafin, Dr. Goke Adegoroye, Bangon Littafin da kuma Dr. Bukar Usman

 

Yana daga cikin martaba da girmamawa da kuma farin ciki a gare ni, a matsayin wanda zai rubuta wannan Gabatarwa ga littafi mai taken “Shugabanci A Ma’aikatun Gwamnatin Tarayyar Najeriya: Tarihin Shekara 50 Na Darussan Aiki, Musharaƙa Da Nasarori” (Leadership in the Nigerian Civil Service: Five Decades of Lessons in Performance, Encounters and Triumphs), tarihin rayuwar ɗaya daga cikin abokan aikina na da, da muka yi aiki tare na lokaci mai tsawo a Ma’aikatar Gwamnatin Tarayyar ƙasarmu, Najeriya.

Kodayake Dr. Adegoke Adegoroye — marubucin littafin kuma wanda tarihin ya shafa kai tsaye, ya daɗe yana yi min tayin cewa ni zan rubuta wannan Gabatarwa, ban samu damar ganin daftarin littafin ba sai ranar 3 ga Fabrairu, 2025, lokacin da ya turo min da shi a kammale, tare da buƙatar cewa in rubuta Gabatarwar. Na karɓi wannan buƙata da hannu bibbiyu ba tare da wani jinkiri ba.

Ko da na ga take da sunan littafin, na yi amanna da cewa zan iya rubuta wannan Gabatarwa ba tare da na karanta cikakkiyar ƙunshiyarsa ba. Tsawon mu’amalarmu da juna ya sa na fahimci irin zurfin ilimi da ƙwazo da Dokta Adegoroye yake da shi dangane da harkoki da hidindimun gwamnati gaba ɗaya. A kodayaushe batutuwan da suka shafi aikin gwamnati su ne abin tattaunawarsa tsakaninsa da mutane hatta da uwargidansa, wacce ‘yar asalin ƙasar Mexico ce. Ya haɗu da ita ne lokacin da ya halarci wani taron ƙasa-da-ƙasa dangane da kare muhalli, wanda aka gudanar a birnin Harare na ƙasar Zimbabwe (Convention on International Trade in Endangered Species of Wild Fauna and Flora — CITES).

Marubucin Littafin, tare da Matarsa da kuma Ɗiyarsa

Yanzu shekaru fiye da goma sha biyar ke nan da Dokta Adegoroye ya yi murabus daga aiki, amma bai taɓa kawar da kai daga tattaunawa kan harkokin gudanar da gwamnati ba. Har yanzu yana rubuce-rubuce da gabatar da jawabai da suka shafi aikin gwamnati, musamman ta fuskar shugabanci nagari da kare muradun al’umma. Mutum ne mai himma da kawo gyara, mai kishin ƙasa kuma yana matuƙar bin ƙa’ida da tsarin doka, musamman wajen zaɓi da tantance mutanen da za su rike ofisoshin gwamnati. Za a iya cewa ya ɗauki nauyin lura da muradun ƙasa na rayuwa gaba ɗaya, bisa dogon tarihin aikinsa na gwamnati da hidimar ƙasa na tsawon shekaru fiye da talatin da biyar da kuma tarbiyyar da ya ginu kanta, ta gaskiya da riƙon amana.

Wannan littafi na tarihin Dr. Adegoroye ne da ke ƙoƙarin bijiro da darussan da ya koya daga aikinsa da gogewarsa a aikin gwamnati ta fuskar gudanarwa da shugabanci, domin wasu su amfana. Yana da ƙwarin gwiwar cewa Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya ta Najeriya, wadda ita ce ginshiƙin tafiyar da gwamnati, dole ne a sake inganta ta da ma’aikata nagari, domin cika burin da aka daɗe ana mafarkin samu. Ya samar da dalilai masu ƙarfi da suka sa ya rubuta wannan littafi, wanda ke matsayin ci gaba ga littafinsa da ya gabata a can baya (2015), mai juzu’i biyu, mai taken “Dawo Da Martabar Kyakkyawan Mulki A Najeriya” (Restoring Good Governance in Nigeria). Amma wannan sabon littafi, ya fi na baya zurfafawa ta fuskar tsage gaskiya da faɗakarwa. A zubi da tsarinsa, yana kamanceceniya da tsarin shari’a a kotu, inda marubucin ke bijiro da tsauraran tambayoyi kuma daga bisani ya bayar da amsoshi gamsassu, ba tare da nuƙu-nuƙu ba.

Hagu-Dama: Marubucin Littafin, tare da Tsofaffin Shugabannin Ƙasa, Janar IBB da kuma Janar Muhammadu Buhari, a yayin wani taro a shekarun baya

Abin da ya fi ɗaukar hankalina a littafin nan, shi ne yadda aka sake jaddada muhimmancin gaskiya da amana a matsayin ginshiƙai wajen magance matsalolin da ke damun Ma’aikatun Gwamnati a Najeriya. Dokta Adegoroye ya jaddada cewa ɗaya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da ya kamata a yi la’akari da su wajen naɗa shugaba a ma’aikata, ita ce cancanta – wato a riƙa naɗa ma’aikatan da suke da nagartattun halayen gaskiya da amana. Haka kuma a riƙa tantance su, bisa la’akari da tsarin dokoki da ƙa’idojin aikin gwamnati, da dokokin kuɗi, dangane da abin da kundin tsarin aiki ya tanada da kuma sanannun takardun umarni. Ya bayyana cewa ta hanyar tabbatar da gaskiya da amana a cikin tsarin ɗaukar ma’aikata, da tura su wuraren da za su yi aiki, da bayar da horo da ladabtarwa za a iya samar da ingantattun shugabannin ma’aikatu, waɗanda za su iya daidaita zaman waɗanda ke rike da madafun iko na siyasa da kuma ƙarfafa ma’aikata da ke ƙarƙashinsu, wajen kiyaye doka da oda.

Marubucin Littafin ne, a yayin da yake musanya da tsohon Shugaban Ƙasa, Marigayi Umaru Musa ‘Yar-adua

Ya kara da cewa, babban ƙalubalen da ke gaban Ma’aikatun Gwamnati, shi ne samar da isassu, ƙwararru kuma nagartattun ma’aikata, masu halin kirki. Waɗannan irin ma’aikata ne ake da buƙatar su cike manyan muƙaman shugabanci, domin su zama madubi ga ƙananan ma’aikata, su kuma gina sabon rukunin shugabanni masu kishi da biyayya ga ƙa’idojin tsarin aiki. Hakan yana da alaƙa da buƙatar samar da rumbun adana muhimman bayanan kowace cibiyar ma’aikata (institutional memory) — inda rashin haka ke tilasta ƙirƙirar sabbin ƙa’idoji da tsare-tsare, musamman a lokacin sauye-sauyen mulki. Littafin nan yana nuna irin hazaƙa da kaifin ƙwaƙwalwar Dokta Adegoroye, wajen adana tarihin da ya dace don tabbatar da kyakkyawan shugabanci. Ya bayyana cewa, babban burinsa shi ne ya ga ya ɗare bisa kujerar muƙami mafi girma a ma’aikatar gwamnati, domin cika burinsa na aiwatar da manufofi da tsare-tsaren da ya yi amanna da su. Wannan buri nasa ya samu goyon bayan wasu jiga-jigan gwamnati a lokacin. Kodayake bai kai ga samun wannan matsayin ba, amma waɗanda suka samu sun shaida irin namijin ƙoƙarinsa a lokuta daban-daban masu muhimmanci da kuma gudummawar da ya bayar a samun nasararsu. A haƙiƙanin gaskiya, mutane da dama suna kallon Dokta Adegoroye a matsayin mafi dacewa da cancantar ya zama Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya – amma Allah bai nufa ya zama ba.

A cikin barkwanci, ina yawan cewa Dokta Adegoroye mutum ne mai son “tunkarar al’amura,” amma shi kuma yana cewa shi mutum ne mai “yunƙurin tantance matsala da nemo hanyoyin gyara” ne kawai. Wannan littafin tarihi nasa, babban kogin ilimi ne mai zurfi, yana buƙatar mutum ya nazarce shi cikin natsuwa da basira, domin ya fahimci gagarumar gudummawar da ya bayar a harkar samar da kyakkyawan ilimin gudanarwa da shugabanci a ma’aikatu da hukumomin gwamnati. Ya kamata kuma wajibi ne ga kowane mai riƙe da madafun iko, da masu shirin shiga gwamnati, da malamai da ɗaliban da ke koyarwa da nazarin ilimin harkokin shugabanci da sarrafa albarkatun buƙatar ɗan Adam da dukiya su mallaki littafin kuma su nazarce shi.

Dr. Adegoroye ne na, a matsayinsa na Shugaban Ayarin Najeriya, a taron Ƙungiyar UNESCO da aka gudanar a 2009

Haka nan kuma, kowane ɗan Najeriya nagari ya kamata ya karanta wannan littafi — ba kawai domin fahimtar irin kyawawan ƙa’idojin da ake buƙata domin gina tsarin gudanarwar ma’aikata ba, har ma domin gane irin jajircewar da Dokta Adegoroye yake yi a yayin bincike da rubuce-rubuce da ƙoƙarin gyara, a lokacin da yake kan aiki da ma bayan ya yi ritaya. Ya cancanci yabo bisa jajircewarsa wajen inganta shugabanci nagari da kuma tsayuwa tsayin daka wajen kare mutuncin Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya ta Najeriya — ta hanyar samar da shugabanci na koyi.
_______________
Dokta Bukar Usman, OON
Tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja
11 ga Fabrairu, 2025

Previous Post

ALLAH JI ƘAN AMINU DOGO

Next Post

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (4)

Related Posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue
Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
Next Post
TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (4)

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (4)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Taron editoci: Tinubu na so a riƙa yaɗa kyawawan labarai don jawo zuba jari a Nijeriya

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Minista Idris Cikin ‘Yan Kwamitin Garambawul

January 16, 2024
Yadda Bikin Ƙaddamar da littafin SIRRIN MACE MUSULMA Ya Gudana A Kabo

Yadda Bikin Ƙaddamar da littafin SIRRIN MACE MUSULMA Ya Gudana A Kabo

May 29, 2025
HAMISU GUMEL: Dacewarsa A Muƙamin Sakataren Watsa Labaran Gwamnan Jihar Jigawa

HAMISU GUMEL: Dacewarsa A Muƙamin Sakataren Watsa Labaran Gwamnan Jihar Jigawa

June 9, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.