• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, July 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Ta'aziyya

ALLAH JI ƘAN AMINU DOGO

ƘASIDA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 29, 2025
in Ta'aziyya
0
ALLAH JI ƘAN AMINU DOGO

Alhaji Aminu Ɗantata (1931-2025)

46
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

ALLAH JI ƘAN AMINU DOGO

Alhaji Aminu Ɗantata (1931-2025)

 

Related posts

Inna Lillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un! Allah Ya Ji Ƙan Malam Lawal

Inna Lillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un! Allah Ya Ji Ƙan Malam Lawal

June 10, 2026
Malumfashi An Yi Babban Rashi

Malumfashi An Yi Babban Rashi

May 11, 2026

__________
Wannan ƙasida daga Bashir Yahuza Malumfashi, Fasihin Galadiman Katsina, ta’aziyya ce ga Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu a ranar Asabar, 03-01-1447 (Hijiriyya), 28-06-2025 (Miladiyya).
__________

1
Da farko ni na yi himma,
Nai nufina babu hamma,
Zan yi roƙo babu homa,
Rabbi tanyo ni da goma.
Ta’aziyyarsa Aminu Dogo.

2
Alhayyu kai ka yi rayuwa,
Kai ke mai kawo rasuwa
Ko gida ko ko kasuwa
Jiddun fa kai ke wanzuwa.
Ka tufata ruhin Aminu Dogo.

3
Ya Manzona ɗan Amina.
Ya mai tsarki mai sakina.
Ya mai Makka gwarzon Madina.
Masoyinka yau ya mirgina.
Yai wafati Aminu Dogo.

4
Bawan Allah ya yi suna
Halaye nai sun yi rana
Mai himma ne ko’ina na.
Ba ya shirgi shi da sauna.
Mai daraja ne Aminu Dogo.

5
Dukiya tai babu tsatsa,
Romo daɗi in ka tsotsa
Goro marsa babu tsutsa
Aikin ɓur sai dai su tusa.
Allah ka ji ƙan Aminu Dogo.

6
Ga uban al’umma kwata
Aikin Allah ya kwatanta
Duk marayu ya killata
Raunana shi ya suturta
Aikinsa ne Aminu Dogo.

7
Bai gadara ba ya homa,
Ba ya raini bai taƙama.
Aikinsa kullum salama.
Haka kuma shi bai zalama.
Kun ji halayen Aminu Dogo.

8
Ya riƙe Allah da Manzo.
Ba ya fashin keta hazo.
Kai ziyara tai ga Manzo.
Har mutuwa tai da taz zo.
Wannan shi ne Aminu Dogo.

9
Dogo fari mai haiba,
Fararen tufafi ya saba.
Farar zuciya ba ya gaba.
Burinsa kullum cigaba.
Bawan Allah Aminu Dogo.

10
Katangar suga mai kauri.
Bangon ƙarfe mai ƙwari.
Ingarma ne mai sauri.
Ruwan Jakara ba bauri.
Allah yafe wa Aminu Dogo.

11
Mai nasiha mai nuni,
Mai zumunci mai tsani.
Mai ƙana’a mai bayani.
Aikin assha shi yai hani.
Wannan shi ne Aminu Dogo.

12
Ya jama’a ga roƙona.
Mutan Kano har Kaduna
Jama’ar Borno har Katsina.
Duk duniya har Dekina.
Ku mai addu’a Aminu Dogo.

13
Ina ‘ya’yansa, duk ‘yan uwa,
Ina masoya, kui yo zuwa,
Ina sarakai masu ƙawa,
Malamai, ya masu baiwa.
Yau kuma babu Aminu Dogo.

14
Ni Bashir yau na yi shela,
Ina maƙiyansa masu talla?
Suna ta kira wai ya shilla!
To ya tafi, ai sai kui Gala!
Allah ka ji ƙan Aminu Dogo.

15
Ya Allahu gafarta masa.
Ya Rahim sanyaya masa.
Ya Affuwu, sauƙaƙa masa.
Ya Salam, ka faranta masa.
Allah yafe wa Aminu Dogo.
__________
© Bashir Yahuza Malumfashi
Lahadi, 04-01-1447 (Hijiriyya)
29-06-2025
__________

Previous Post

Next Post

Jajirtataccen Jigo A Fagen Samar Da Nagartaccen Shugabanci: Gabatarwar Littafin Tarihin Dokta Adegoroye

Related Posts

Inna Lillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un! Allah Ya Ji Ƙan Malam Lawal
Ta'aziyya

Inna Lillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un! Allah Ya Ji Ƙan Malam Lawal

June 10, 2026
Malumfashi An Yi Babban Rashi
Ta'aziyya

Malumfashi An Yi Babban Rashi

May 11, 2026
Malumfashi Mun Yi Babban Rashi
Ta'aziyya

Malumfashi Mun Yi Babban Rashi

March 26, 2026
Next Post

Jajirtataccen Jigo A Fagen Samar Da Nagartaccen Shugabanci: Gabatarwar Littafin Tarihin Dokta Adegoroye

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

SASSANYAN AMINCI (2)

SASSANYAN AMINCI (2)

September 5, 2025
Muhimman Ayyukan Da Shugaba Tinubu Ya Ɗora Mani – Ministan Yaɗa Labarai

Muhimman Ayyukan Da Shugaba Tinubu Ya Ɗora Mani – Ministan Yaɗa Labarai

October 19, 2023
Tattaunawar Ɗan Jarida Da Bazawara ‘Yar Tuwo-Tuwo

Tattaunawar Ɗan Jarida Da Bazawara ‘Yar Tuwo-Tuwo

June 23, 2026
A Review of “Leadership in the Nigerian Civil Service…”

A Review of “Leadership in the Nigerian Civil Service…”

July 8, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.