• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (2)

RAHOTON MUSAMMAN

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 15, 2025
in Gizago
0
TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (2)

Daga Hagu: Hon. Abdullahi Ibrahim Mahuta da Bashir Yahuza Malumfashi

74
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (2)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Daga Hagu: Injiniya Muntari Sagir da Alhaji Jibrin Sama’ila (Jibson) da Sarkin Fulanin Galadima da sauran manyan baƙi, a zauren taron

Tun da farko dai, an fara tsagwaron taron ne da misalin ƙarfe 10 na safe, inda bayan buɗewa da addu’a sai aka biyo da taken Najeriya. Daga nan kuma aka gabatar da mai muƙala ta farko. Hon. Abdullahi Ibrahim Mahuta, shi ne ya gabatar da muƙala ta farko mai taken “Alherai, Matsaloli Da Ƙalubalen Soshalmidiya.”

Wane ne Abdullahi Ibrahim Mahuta? “Malam” kamar yadda ake masa laƙabi, gogaggen ɗan siyasa ne kuma masani a fannin al’amuran mulki. Ya taɓa zama ɗan Majalisar Dokoki a Jihar Katsina, inda ya wakilci Ƙaramar Hukumar Malumfashi. Haka kuma ya taɓa zama Kwamishinan Jin Koken Jama’a na Gwamnatin Tarayya, a Jihar Katsina.

A sanadiyyar gogewarsa a fannonin ilimi daban-daban, ya yi wa wannan muƙala tasa adalci, inda ya gabatar da ita cikin walwala da annashuwa, a kan tsarin musharaƙa da masu sauraro. Ya nuna ƙwarewa ta fannin koyarwa, inda ya riƙa tuntuɓar masu sauraro, su kawo mas’ala da ta danganci maudu’in da yake gabatarwa, daga bisani kuma ya biyo da sharhi da tsokaci da ƙarin bayani.

Wani abin burgewa da ban sha’awa, Malam Abdullahi ya riƙa bijiro da hujjoji daga Alƙur’ani mai girma da hadisan Manzon Allah (saw), a dukkan wuraren da suka dace, kamar kuma yadda yake doka misalai da al’amuran rayuwa, domin su zama gargaɗi ga al’umma, musamman masu tu’ammali da Soshalmidiya.

Bayan Hon. Abdullahi ya kammala muƙalarsa, ba tare da jinkiri ba, Kwamared Ibrahim Jaji ya gabatar da Bashir Yahuza Malumfashi, wanda ɗan jarida ne, marubuci kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum. Shi ne ya gabatar da ta’aliƙi a kan muƙalar da Hon. Mahuta ya gabatar.

Wasu daga cikin mahalarta taron

Kamar yadda muƙalar Mahuta ta gudana, ta tsefe wasu daga cikin muhimman alherai guda tara da Soshalmidiya take da su. Waɗannan kuwa sun haɗa da ƙarfafa zumunci, kasuwanci, yaɗa ilimi da koyonsa da gudanar al’amuran addini, isar da saƙo cikin sauri, bunƙasa tsaro da kuma nishaɗantarwa.

Malam Bashir, a ta’aliƙinsa ya bayyana cewa, ga duk mai tu’ammali da Soshalmidiya, ya yi ƙoƙari ya ci gajiyar waɗannan alherai nata, sannan ya guje wa faɗawa cikin sharrukanta. Misali, ya ce mutum ya yi ƙoƙari wajen amfani da ita wajen sada zumunta, domin girbar ladar da ke cikin zumunci. Amma tare da gargaɗin cewa a kiyayi hulɗa da abokai ko ƙawaye na banza. Musamman matan aure, su kiyayi keta hurumin Allah, wajen yin abin da bai dace ba a Soshalmidiya.

Ya ƙara da cewa, ‘yan kasuwa su yi amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen inganta sana’o’insu. Amma su kula sosai domin kauce wa faɗa wa mazambata da marasa gaskiya a irin waɗannan kafafe. Ta fuskar ilimi da koyon addini kuwa, mutum zai iya koyo kuma ya koyar ta kafar Soshalmidiya, kasancewar akwai malamai a kowane fanni na ilimi da suke gabatar da karatu da wa’azi, kamar kuma yadda ake samun makarantu da ke gabatar da kwasakwasai na ilmi a kowane fanni.

An buƙaci ‘yan siyasa da magoya bayansu da su ci gajiyar Soshalmidiya ta hanyar yekuwa da faɗakarwa a siyasance, daidai da abin da ya dace. Sannan kuma a kauce wa zage-zage da cin mutuncin juna. Haka ma ta ɓangaren bunƙasa tsaro, an yi kira ga al’umma da su guji yaɗa labarun ƙarya, dangane da abin da ya shafi tsaro. An ƙarfafa shawarar cewa, mutane su lizimci tuntuɓar jami’an tsaro kai tsaye don kwarmata bayanan sirri na masu karya doka ko game da ‘yan ta’adda, maimakon mutum ya ce zai ɓoye sirrin mai aikata laifi. Kuma mutane su guji ɗaukar doka a hannunsu.

Bisa ga yadda Soshalmidiya ta zama wata kafa ta nishaɗi da nishaɗantarwa, an ja hankalin mutane da su yi taka-tsan-tsan wajen bibiyar tashoshi da wuraren da ake tallata baɗala. Haka kuma, an gargaɗi musamman mata da su kiyayi bayyana tsiraici da rayeraye na rashin kunya a Soshalmidiya.

Daga ƙarshe, Bashir ya rufe ta’aliƙinsa da wata ƙasida da ya rera, mai taken HANJIN JIMINA. Ƙasidar, mai baitoci 15, babban jigonta ya ta’allaƙa ne ga alherai da sharrukan da ke tattare da wayar hannu ko kuma Soshalmidiya gaba ɗaya. Kamar dai kwatankwacin jigon muƙalar da Abdullahi Mahuta ya gabatar. Hanjin Jimina – akwai na amfani kuma akwai na zubarwa.
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online)

Previous Post

DEMOCRACY IN NIGERIA (1999–2025): A PROMISE UNFULFILLED

Next Post

WATER PROJECT IN MALUMFASHI: COMMUNITY URGED TO SUPPORT GOVERNMENT

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
WATER PROJECT IN MALUMFASHI: COMMUNITY URGED TO SUPPORT GOVERNMENT

WATER PROJECT IN MALUMFASHI: COMMUNITY URGED TO SUPPORT GOVERNMENT

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Gwamnati Ta Kula Da Mu

Gwamnati Ta Kula Da Mu

May 29, 2023
RAMADAN KARIM: 07-1447

RAMADAN KARIM: 07-1447

February 24, 2026
Ali Nuhu Ya Shiga Rukunin Fitattun Taurarin Fim 100 Na Afirka

Ali Nuhu Ya Shiga Rukunin Fitattun Taurarin Fim 100 Na Afirka

July 9, 2023
Lt. Col. Danjuma’s Book: Captivating Insight Into Civil-Military Relations In Nigeria

Lt. Col. Danjuma’s Book: Captivating Insight Into Civil-Military Relations In Nigeria

January 22, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.