• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, April 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Ƙungiyar BUWDA Abin Alfahari Ce Ga Al’ummar Bura Da Duniya Baki Ɗaya

JAWABIN BABBAN BAƘO

Bukar Usman, OON by Bukar Usman, OON
April 16, 2025
in Babban Labari
0
BUWDA is the Pride of Bura People, Humanity in General – Dr. Bukar Usman

Dr. Bukar Usman delivering Keynote Address as Guest Speaker at the Bura Women Development Association (BUWDA) Bura Day Celebration, Abuja 2025

31
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Ƙungiyar BUWDA Abin Alfahari Ce Ga Al’ummar Bura Da Duniya Baki Ɗaya
– Dokta Bukar Usman

_______________

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026

Wannan shi ne jawabin Dokta Bukar Usman, a matsayinsa na Babban Baƙo mai jawabi a Bikin Ranar Al’ummar Bura, wanda Ƙungiyar Bunƙasa Rayuwar Matan Bura (Bura Women Development Association – BUWDA), reshen Babban Birnin Tarayya, Abuja ta gudanar tare da ƙaddamar da Bankin BUWDA Microfinance da kuma gyaran gidan saukar baƙi na ƙungiyar a Cibiyar Horar da Sana’o’i da ke Marama, Ƙaramar Hukumar Hawul, Jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya, wanda aka gudanar a AGNL Park Apo, Abuja, a ranar 12 ga Afrilu, 2025.

_______________

Dokta Bukar Usman, Babban Baƙo Mai Jawabi, a Bikin Ranar Al’ummar Bura, wanda Ƙungiyar Bunƙasa Rayuwar Matan Bura (Bura Women Development Association – BUWDA) ta gunadar a Abuja, 2025

Gaskiya na ji daɗi kuma na yi alfahari da samun wannan dama don gabatar jawabi ga wannan taro na al’ummarmu da masoya da abokan arziƙi da suka hallara, domin nuna goyon bayansu ga Ƙungiyar Bunƙasa Rayuwar Matan Bura, reshen Babban Birnin Tarayya, Abuja da kuma uwar ƙungiya gaba ɗaya.

Na kasance mai bibiyar ayyukan uwar ƙungiyar tun kafuwarta, kuma ana sanar da ni haka kai tsaye. Na tabbata cewa ƙungiyar tana da kyawawan manufofi don inganta rayuwar jama’armu da ci gaban al’ummar Bura. Har ila yau, ƙungiyar ta dace da shugabanni masu kishi da sadaukar da kai, waɗanda suka ɗauki nauyin aiwatar da waɗannan manufofi kuma da ƙima da tawali’u. Sun gabatar da muhimman ayyuka, waɗanda za a iya kira da gani-ya-kori ji. Ayyukan suna nan a fili, musamman a Marama, inda Cibiyar Horar da Sana’o’i ta ƙungiyar take aiki. Dukkan waɗanda suka samu horo a wannan cibiya, sun amfana. Sun samu ƙwarewa da koyon sana’o’in dogaro da kai. Haka kuma cibiyar a buɗe take ga ƙarin masu son koyon sana’o’i da baƙi masu son kai ziyara. Koyon sana’a wani ɓangare ne na ilimi wanda jama’armu suka runguma tun lokacin da Turawan Mulkin Mallaka da ‘Yan Mishan suka gabatar da shi shekaru da dama da suka gabata.

Dama-Hagu: Janar PC Tarfa, Babban Baƙo, Dokta Bukar Usman, Babban Baƙo Mai Jawabi da Misis Aspa P. Thahal, tsohuwar Shugabar Ƙungiyar Bunƙasa Rayuwar Matan Bura, a Bikin Ranar Al’ummar Bura, wanda Ƙungiyar Bunƙasa Rayuwar Matan Bura (Bura Women Development Association – BUWDA) ta gunadar a Abuja, 2025

A bayyane yake cewa ƙungiyar BUWDA, wadda aka kafa a shekarar 2014, ta samar da Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Marama a shekarar 2020. Gwamnatin Jihar Borno ce ta ƙaddamar da cibiyar a hukumance, a ranar 31 ga Disamba, 2022, wadda kuma ita ce ranar da aka yaye ɗaliban farko da cibiyar ta horar kan sana’o’i daban-daban.

Dama-Hagu: Janar Tukur Yusuf Buratai, tsohon Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya kuma Ambasada a Jamhuriyyar Benin (Betaran Biu), Shugaban Taro, tare da Dokta Bukar Usman, Babban Baƙo Mai Jawabi, a Bikin Ranar Al’ummar Bura, wanda Ƙungiyar Bunƙasa Rayuwar Matan Bura (Bura Women Development Association – BUWDA) ta gunadar a Abuja, 2025

Wannan cibiya abin alfahari ce a gare mu, kuma wata shaida ce abin misali kuma abin koyi; wacce take nuna yadda ake gabatar taimakon kai-da-kai a ƙasar Bura, Masarautar Biu, Jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya. Har ila yau, wannan wani babban abin tarihi ne da ke nuna kyakkyawar niyya da sadaukarwa daga waɗanda suka assasa wannan aiki – waɗanda cikinsu har yanzu wasu suna raye, wasu kuma sun riga mu gidan gaskiya. Ya dace mu gode wa waɗanda ke raye da jinjina masu, bisa sadaukarwar da suka nuna. Su kuma waɗanda suka rasu, ya kamata mu ci gaba da tuna su ta hanyoyin da suka dace.

Yanzu da ƙungiyar ta samu sababbin shugabanni, suna ɗaukar sabbin matakai domin inganta kayayyakin da ke cikin cibiyar da samar da ƙarin wasu; domin daɗaɗa wa baƙi masu ziyara daga nesa da kusa. Shirin kafa Bankin Microfinance, wanda zai ƙara buɗe ƙauyukanmu ga harkokin kuɗi na zamani domin ci gaba da sauri a zamantakewa da tattalin arziki, abu ne mai kyau ƙwarai. Sai dai kuma kafin a fara, ya kamata a yi bincike mai zurfi na yiwuwar nasararsa da kuma tabbatar da tsayayyen tsarin kula da kuɗi. Wannan nauyi ne mai girma da ke kan shugabannin yanzu da waɗanda za su zo nan gaba. Ina fata kuma ina addu’ar cewa, shugabannin za su ci gaba da yin aiki yadda ya kamata, domin samun amincewar jama’a da ci gaban al’ummar Bura da kuma ɗorewar abubuwan alherin da waɗanda suka kafa ƙungiyar da farko suka sa gaba.

Wasu daga cikin matan al’ummar Bura, suna taka rawa cikin murna, a yayin Bikin Ranar Al’ummar Bura, wanda Ƙungiyar Bunƙasa Rayuwar Matan Bura (Bura Women Development Association – BUWDA) ta gunadar a Abuja, 2025

A nan, ina so in jaddada cewa koyon sana’o’i da ayyuka iri-iri, abin buƙata ne matuƙar gaske ga jama’armu, domin su ƙara a kan harkar noma, wadda ita ce babbar sana’ar gargajiya ga al’ummarmu. Ita kanta sana’ar noma, tana buƙatar sabbin dabarun zamani, domin haɓaka amfanin gona da sanar da shi mai yawa, domin biyan buƙatun jama’ar da ke ta ƙaruwa. Muna da filayen noma masu faɗi da suka dace a aikata su da injina da na’urorin noma na zamani, amma muna barin su haka nan. Lokaci ya yi da za mu rage amfani da garma da fatanya na gargajiya, marasa inganci da wahalar da jiki.

Nan ma wasu daga cikin ‘yan biki da kuma baƙi ne, a yayin Bikin Ranar Al’ummar Bura, wanda Ƙungiyar Bunƙasa Rayuwar Matan Bura (Bura Women Development Association – BUWDA) ta gudanar a Abuja, 2025

Duk da cewa abu ne mai muhimmanci mu adana tsirranmu na gargajiya, ya kamata mu samo hanyar yin hakan ba tare da hana haɓakar amfanin gona ba. Ya dace a dawo da bukukuwan nunin amfanin gona da dabbobi, domin baje kolin nuna sabbin nau’o’in iraruwa da dabbobi, kamar kuma yadda za a riƙa saka wa haziƙan manoma nagari da raba masu kyaututtukan ƙarfafa gwiwa, musamman ma samar masu da sabbin kayan noma masu inganci.

Wasu daga cikin ‘yan biki da kuma baƙi, a yayin Bikin Ranar Al’ummar Bura, wanda Ƙungiyar Bunƙasa Rayuwar Matan Bura (Bura Women Development Association – BUWDA) ta gunadar a Abuja, 2025

Daga ƙarshe, ina yi wa shugabannin Ƙungiyar BUWDA, reshen Babban Birnin Tarayya Abuja da uwar ƙungiyar fatan nasara a dukkan ayyukan da suka sanya gaba. Sun cancanci goyon baya a kowane mataki kuma a kan lokaci.

Nan ma wasu daga cikin ‘yan biki da kuma baƙi, a yayin Bikin Ranar Al’ummar Bura, wanda Ƙungiyar Bunƙasa Rayuwar Matan Bura (Bura Women Development Association – BUWDA) ta gunadar a Abuja, 2025

Na gode.

Dokta Bukar Usman, OON
Tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.

Previous Post

BUWDA is the Pride of Bura People, Humanity in General – Dr. Bukar Usman

Next Post

IDAN APC TA AMSHI KANO: INA MAKOMAR SARAKUNA BIYU?

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Babban Labari

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume
Babban Labari

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel
Babban Labari

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026
Next Post
IDAN APC TA AMSHI KANO: INA MAKOMAR SARAKUNA BIYU?

IDAN APC TA AMSHI KANO: INA MAKOMAR SARAKUNA BIYU?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

DARASIN JUMU’A DAGA SHEIKH GAMAWA

DARASIN JUMU’A DAGA SHEIKH GAMAWA

September 29, 2023

April 15, 2024
DEMOCRACY IN NIGERIA (1999–2025): A PROMISE UNFULFILLED

DEMOCRACY IN NIGERIA (1999–2025): A PROMISE UNFULFILLED

June 15, 2025
ADADIN KUƊIN DA NAJERIYA ZA TA SAMU IDAN TA CI KOFI A YAU

ADADIN KUƊIN DA NAJERIYA ZA TA SAMU IDAN TA CI KOFI A YAU

February 11, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye
  • Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.