TABBAS SHEIKH ABDUL’AZIZ DUTESEN TANSHI BAI “MUTU” BA
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
An wayi gari a ranar Juma’a, 06-Shawwal-1446 (Hijiriyya) daidai da 04-Afirilu-2025 (Miladiyya) da babban labarin rasuwar fitaccen malamin Musulunci, Sheikh (Dokta) Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi. Kamar yadda labarin ya bayyana, malamin ya rasu ne a daren na Juma’a, a sakamakon wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.
An gabatar da jana’izar Sheikh Abdul’aziz a filin Masallacin Idi na Games Village da ke Bauchi da misalin karfe 10 na safiyar Juma’a.

Wata majiya ta kusa da shi, wato Majalisin Dutsen Tanshi Bauchi, ta bayyana cewa malamin ya rasu yana furta Kalmar Shahada. Haka kuma cikin wasiyyar da ya bari, ta haɗa da cewa, ya hana ɗaukar hoto a yayin jana’izarsa. Ya hana zaman makoki a gidansa. Ya hana a riƙa kokawa wajen raka gawarsa zuwa maƙabarta, kamar kuma yadda ya ce, kada mutane su shiga maƙabarta da takalma.
Bayan wannan, shin jama’a ko kun san cewa tabbas Sheikh Idris bai “mutu” ba? Babu ko shakka, fitaccen malamin bai mutu ba. Babu shakka zai ci gaba da rayuwa a wannan duniya tamu. Kai bari in yi ta ta ƙare – Malam a yau ne ma zai ci gaba da da rayuwa tamkar yau aka haife shi.
Ga dalilan da suka sanya na faɗi cewa Malam bai “mutu” ba, duk kuwa da cewa a yau an binne gangar jikinsa a kabari.
Na farko dai, a Hadisi mai lamba 1631 na Sahih Muslim, an ruwaito cewa; Manzon Allah (saw) ya ce: “Idan mutum ya mutu, ayyukansa sun zo ƙarshe, illa abubuwa uku – sadaƙatul jariya, wato sadaka mai gudana, ilimi mai amfanin al’umma da kuma nagartaccen ɗa.”
Idan mun duba waɗannan abubuwa uku, Malam Abdul’aziz duk ya mallake su. Batun sadaƙatul jariya, Malam ya kafa makaranta wacce babu shakka za ta ci gaba da gudana har illa ma sha Allah.
Na biyu, batun ilimi, Dutsen Tanshi ya sadaukar da rayuwarsa wajen neman ilimin addinin Musulunci. Ya yi karatu a Jami’ar Madina, inda ya samu shaidar Digiri a fannin Shari’a. Haka kuma ya samu Digirin Digirgir a fannin Fikihu a Jami’ar Musulunci ta Sudan. Malam ya bayar da karatu, ya shayar da ɗalibai masu tarin yawa ilimi. Ya yi rubuce-rubuce masu tarin yawa a fagen Musulunci.

Na uku, Allah Ya albarkaci Malam Idris Abdul’aziz da nagartattun ‘ya’ya, waɗanda babu shakka za su riƙa yi masa addu’a.
Malam Idris zai ci gaba da rayuwa a duniyar nan, a zukatan miliyoyin nagartattun Musulmin duniya saboda ayyukansa na jaddada Musulunci da suka cika kafafen sadarwa na soshalmidiya.
Malam Abdul’aziz zai ci gaba da rayuwa a zukata da bakunan maƙiya Musulunci, musamman waɗanda ya riƙa yaƙa a zamanin da yake raye.

Babu shakka, Dokta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi bai mutu ba. Zai ci gaba da rayuwa. Sunansa zai ci gaba da ƙwanƙwasa ƙofofi da zukata. Iliminsa da wa’azojinsa za su ci gaba da wanzuwa har illa ma sha Allah. A taƙaice, daga yau ma wasu dubban mutane za su fara saninsa da ayyukansa.
Muna roƙon Allah Ya ji ƙan shi da rahama. Ya yafe masa kurakurensa. Amin!
_______________
Bashir Yahuza Malumfashi, Editan Mujallar Taskar Gizago (online)
Juma’a 06-10-1446 (Hijiriyya)
04-04-2025 (Miladiyya).














Tabbas malam yarasu amma kuma kamar yana raye sbd ayyukansa nabada shidima ga al umma sunanann sunata tfy kmr malam yn raye
ina mika ta azziya daganan garin potiskum Allah yjkn malam