• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, August 14, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

BANKWANA DA GWANI

Ƙasidar Ta'aziyyar Sheikh Idris Abdul'aziz

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
April 7, 2025
in Adabi
0
BANKWANA DA GWANI

Bankwana Da Gwani

15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

BANKWANA DA GWANI
Ƙasidar Ta’aziyyar Sheikh Idris Abdul’aziz
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Bankwana Da Gwani

 

Related posts

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

Nazari Da Sharhin Littafin Tarihin Garin Lassa

July 18, 2026
Maryam ‘Yar Aljanna (2)

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026

                         __________
Yau kwana uku ke nan da rasuwar fitaccen malamin Musulunci, Sheikh (Dokta) Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi Bauchi. Domin alhini da ta’aziyya, Bashir Yahuza Malumfashi ya rubuta tare da rera baitoci 31 a wannan ƙasida da ya sanya wa suna: BANKWANA DA GWANI. Muna ƙara addu’ar Allah Ya ji ƙan Malam da rahama, Amin. Haka kuma ga mai son saurere da kallon bidiyon wannan waƙa, sai ya leƙa shafin Taskar Gizago na YouTube, a wannan liƙau:

https://youtu.be/EKFt-TyaEsE?si=hsqc9BDQdwOv5Agh
                         ____________

“Inna lillahi” kalami babba.
“Wa inna ilaihi” Allah Rabba.

“Raji’una” a rana babba.
Can muka dosa, gida ne babba.

Ba rabo da gwani ba,
Maida kamarsa ba a samu ba.

Rayuwa zango ce.
Kowa ajali ne babba.

Wani shi yai sammako.
Wani ko da rana babba.

Na tuna bawan Allah,
Idrisu Faƙihi ne babba.

Lallai ka cika gwarzo,
Mujaddadin sunna babba.

Na Dutsen Tanshi,
A Bauchi gari ne babba.

Yau ya cin ma sa’i.
Daren Juma’a rana babba.

Mu duba kwanan wata.
Ranar tafiyar Malam babba.

Bayan watan Azumi ne.
Wagga ibada ce babba.

Mun shigo watan Shawwalu.
Shagalin Sallah yaro har babba.

Shidda ne daidai ga wata,
Ya warke jinya babba.

Huɗu ne ga watan Afirilu,
Watan Nasara ku duba.

Allahu Ya amshi abinSa.
Sai mu gode Sarki Rabba.

Malam da halayensa,
Abin koyi ne maza duba.

Lallai Malam ya yo dace.
Aikin Allah ba ya tababa.

Ina ka fito? Karatu.
Ina ka nufa? Gidan ilimi babba.

Malam ya yi karatu.
Ya shayar da karatu babba.

Malam akwai tauhidi.
Wannan shi ne jigo babba.

Malam ba ya wargi.
Da littafin Allah babba.

Ya ƙaunaci Manzo,
Abban Fatima bango babba.

Malam shi ba ya ƙarya.
Ba ya kwaɗayi ƙarami ko babba.

Maganarsa guda ɗaya tilo:
A yi riƙo da igiya babba.

Tafiyar Malam bai sauri ba.
Muna tafe ba jinkiri ba.

Allah muna roƙon Ka,
Ka haskaka ruhin baba.

Ka saka shi a Firdausi.
Malam ka ji makwanci babba.

Ni ne nai yo ta’aziyya,
Bashiru Gizago ɗan baba.

Baitoci sun cika thirty.
Ƙaro guda ɗaya babba.

Jama’a sai mu ɗau haƙuri.
Mu yo koyi da halin baba.

Idirisa bawan Allah.
Dutse na Tanshi Malam babba.
_______________
© Bashir Yahuza Malumfashi,
Juma’a 06-10-1446 (Hijiriyya),
04-04-2025 (Miladiyya).

Previous Post

TABBAS SHEIKH ABDUL’AZIZ DUTESEN TANSHI BAI “MUTU” BA

Next Post

BUWDA is the Pride of Bura People, Humanity in General – Dr. Bukar Usman

Related Posts

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage
Adabi

Nazari Da Sharhin Littafin Tarihin Garin Lassa

July 18, 2026
Maryam ‘Yar Aljanna (2)
Adabi

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026
Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa
Adabi

Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

June 21, 2026
Next Post
BUWDA is the Pride of Bura People, Humanity in General – Dr. Bukar Usman

BUWDA is the Pride of Bura People, Humanity in General - Dr. Bukar Usman

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Bura women Celebrate Bukar Usman at 83

Bura women Celebrate Bukar Usman at 83

January 7, 2026
MATSALAR TSARO: Sakkwatawa Mu Aje Siyasa Don Fuskantar Wannan Babbar Matsala

MATSALAR TSARO: Sakkwatawa Mu Aje Siyasa Don Fuskantar Wannan Babbar Matsala

October 4, 2023
ACF to TINUBU: MR. PRESIDENT, YOUR GOVERNMENT NEGLECTS AND SIDELINES AREWA

ACF to TINUBU: MR. PRESIDENT, YOUR GOVERNMENT NEGLECTS AND SIDELINES AREWA

August 1, 2025
Some Communication Techniques During Crises

Some Communication Techniques During Crises

October 14, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Our Daily Message
  • Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina
  • Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Our Daily Message

Our Daily Message

August 14, 2026
Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina

Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina

August 13, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.