Muhimman Batutuwan Dubawa A Littafin Tarihin IBB
Daga Bukar Usman

°°°°°°°
Sunan Littafi: A Journey in Service (Tarihin Rayuwar Hidimar Ƙasa)
Marubuci: Ibrahim Badamasi Babangida:
Kamfanin Wallafa: BookCraft, Ibadan
Shekarar Wallafa: 2025
Yawan shafuka: 420
Farashi: Ba a faɗa ba
°°°°°°°
Tun lokacin da Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), wanda a yanzu yake da shekaru 83 a raye, ya bayyana cewa ya fara rubuta littafin tarihin rayuwarsa, a cikin wata hira da ya yi da Mujallar TELL, a shekarar 1995 – kimanin shekaru biyu bayan saukarsa daga mulki, jama’ar ƙasar nan suke jira daganan fitowar littafin. Ɗokin nasu yana da alaƙa da yadda al’amuran IBB suka kasance wasu na musamman, watau daban da na shugabannin baya. Al’amuran sun haɗa da kitimurmurar da ta kai har ya zama Shugaban Ƙasa da yadda ya sauka daga shugabancin. Ga kuma rikice-rikice da kwaramniyar da ta wakana a cikin shirinsa na maida mulki hannun farar hula. Sai kuma manufofinsa na tattalin arziki irin na jari-hujja, da tasirin da ake hange yana da shi a rundunar sojojin Najeriya da yadda ya sake wa tsarin siyasa da mulki fasali a ƙasar.
Daga ƙarshe dai, bayan an sha jiran littafin, wanda tsohon Shugaban Mulkin sojan ya shafe shekaru 30 yana bita da rubuta abubuwan da ya tuna, an gabatar da wannan littafi ga jama’a a babban zauren taro na Congress Hall a otal din Transcorp Hilton da ke Birnin Abuja, ranar 20 ga Fabrairu na shekarar 2025.
Kodayake labarin da ya fi jan hankali a kafofin watsa labarai a lokacin ƙaddamar da littafin, shi ne na kusan Naira miliyan dubu ashirin da aka samu a lokacin. Abin da ya fi wannan muhimmanci shi ne bayanan da littafin ya ƙunsa dangane da wasu muhimman abubuwa da suka faru, ciki har da soke zaɓen Shugaban Kasar da aka yi ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993. Haka nan kuma, wasu da suka riƙe manyan muƙaman gwamnati a zamanin shugabancin Ibrahim Babangida, ko suka yi fice a kasuwanci, sun yi bayanai ɓaro-ɓaro a wurin ƙaddamar da littafin.
Wannan littafin tarihin rayuwar IBB, ya ƙunshi babi 13 a cikin shafuka 420. An raba shi rukuni biyar daki-daki. Haka nan akwai cikakkun rataye da rufewa. Ga kuma babi sukutum da ya ƙunshi bayanai a kan soke zaɓen 12 ga watan Yunin shekarar 1993. In ban da babi na 12, wanda ya yi armashi saboda shi ne babin soke zaben 12 ga watan Yuni, na yi wannan sharhi ne bisa yadda aka jera babi-babin littafin da tsarin yadda aka kammala shi.

Rukunan littafin na Ɗaya da na Biyu sun ƙunshi babi-babi ne na tarihin ƙuruciyar Babangida, haɗe da lokacin da aka haife shi da bayani a kan mahaifansa da irin tarbiyyar da ya samu da makarantun da ya yi da kuma ɗaukar shi aikin sojan Najeriya. An fara ganin alamomin basirarsa wajen iya shugabanci, lokacin da aka naɗa shi Shugaban ɗaliban sakandaren lardi da ke garin Bida a Jihar Niger. An dauke shi aikin soja a shekarar 1962.
A sassan littafin da ke bayani a kan rayuwarsa ta aikin soja zalla, watau da ya yi kafin ya hau kujerar shugabancin Najeriya da ya yi shekara takwas a kai, kuma babban mai ba duk askarawan sojojin Najeriya umarni, za a ga cewa ya goge matuƙa a aikin soja, wanda ya fara da mukamin ƙaramin hafsa a shekarar 1962, har ya zuwa shekarar 1984 lokacin da ya zama Shugaban Rundunar Sojojin Ƙasa ta Najeriya.
A lokacin da yake aikin soja zalla, ya ci karo da matsalolin da suka nuna jarumtakarsa da ƙwazonsa a sha’anin shugabanci. Waɗannan halaye sun sa ya shahara a tsakanin hafsoshi da ƙananan sojoji na rundunanr nan ta zaratan sojojin tankunan yaƙi, har ma a duk rundunonin mayaƙan Najeriya gaba ɗaya. Tabbas farin jininsa da sunan da wannan soja mai wushirya ya yi, sun shallake iyakar sojojin Najeriya, har ma da jama’ar ƙasar. Daga cikin mutanen da suka yi mu’amala da shi, ciki har da ni mai yin wannan sharhi. Za mu iya ba da shaidar cewa yana da sauƙin kai da zalaƙa da kaifin basira.
Ɗaya daga cikin misalan shaidar jajicewarsa da jarumtarsa, ita ce rawar da ya taka a Yaƙin Basasar Najeriya, a muƙaminsa na Manjo kuma Kwamandan Bataliya ta 82 a shekarar 1969. An ji masa rauni a lokacin yaƙin, kuma har yau tabon raunin yana jikinsa. Karin wata shaidar jarumtarsa ta bayanna, lokacin da ya kai sojoiji Gidan Rediyon Tarayya da ke Legas domin fatattakar Manjo Buka Suka Dimka da sojojin da ke ƙoƙarin kifar da Gwamnatin Janar Murtala Mohammed a shekarar 1976.

A rukuni na Uku, Babangida ya yi bayanai da dama, ciki har da tasirin katsalandan ɗin soja a mulkin Najeriya. Ya ce duk da hangen kurakurai na zahiri ko na zato, da akan yi wa mulkin soja, gwamnatocin soja sun taka muhimmiyar rawa wajen gina Najeriya da ciyar da ita gaba. A cewarsa, misalan waɗannan gudunmawa sun haɗa da raba-daidai a tsarin siyasar ƙasa ta hanyar ƙirƙiro jihohi da tsiro da shirin nan na matasa yi wa ƙasa hidima, watau National Youth Service Corps (NYSC) da ƙaddamar da shirin Ilmin Firamare Kyauta Na Bai Ɗaya a ƙasar, (Universal Free Primary Education) da kafa cibiyoyi masu ɗorewa, kamar kafa Bankin nan na Jama’a watau People’s Bank da ƙananan bankuna a garuruwa da ungwanni, watau Community Banks. Ga kuma manyan ayyukan raya ƙasa a duk jihohi da kananan hukumomin ƙasar gaba ɗaya; sai kuma gudunmawar da Najeriya ta bayar a ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya, watau United Nations (UN).
Bugu da ƙari, ya ce Sake Fasalin Tattalin Arzikin Ƙasa ma wata babbar gudunmawa ce da gwamnatocin soja suka bayar, kodayake kusan duk misalan da ya bayar na abubuwan da suka faru ne a lokacin mulkinsa. Ya yi la’akari da azancin maganganu uku irin na mutanen Sin da suke cewa, “A kan fara tafiyar mil dubu da taku ɗaya,” da “Mu gani a ƙasa, in ji kare, wai ana biki a gidansu,” da kuma na ukun, “Ba bambanci idan kyanwa baƙa ce ko fara, muddin tana kama ɓeraye.” Bisa wannan manufa ce Shugaba Babangida ya juyar da tattalin arzikin kasa ya zuwa na jari-hujja tsantsa. Hakan ya kai ga bunƙasa yin kayayyakin buƙata a cikin gida, maimakon shigo da su daga ƙetare. Tsarin ya ba masu hali damar buɗe gidajen rediyo da talabijin da kafa bankuna da kamfanonin sufurin jiragen sama da masaƙu da kamfanonin sarrafa amfanin gona. Amma fa ba a maida hankali a kan harkokin noma da kiwo ba, sai dai IBB ya yi nadama ƙwarai da tsarin ya dogara kusan kacokan a kan harkar mai. Wani abu kuma mara daɗi shi ne, wasu daga cikin manufofi da shirye-shiryensa, kamar Shirin Tsuke Bakin Aljihu watau Structural Adjustment Program (SAP), sun haifar da zazzafar zanga-zanga, tare da zargin cewa ‘yan siyasa da ‘yan hamayya da malaman jami’a masu ra’ayin sauyi ne suka kitsa su. Tsohon Shugaban Kasar ya tattauna waɗannan batutwa a babi na takwas a littafin.
A shafi na 114 zuwa shafi na 115, Janar IBB ya bayyana ra’ayin cewa duk da sauya Fasalin Ƙasa da Kundin Tsarin Mulki da aka yi, ɗorewar Najeriya a ƙasa ɗaya zai dogara ne ga halayyar ‘yan ƙasa da samar da kafofin zamantakewar ƙasa masu nagarta, shigen yadda abin yake a ƙasashen da suka ci gaba. Kamar yadda ya bayyana a cikin littafin, “Yawancin matsalolinmu suna da alaƙa da halayenmu ne. A taƙaice, za a iya kafa dokoki mafiya kyau a duniya, da samar da nagartaccen kundin tsarin mulki a ƙasa da shugabanni masu matuƙar jajircewa; amma idan halayyar manyan ‘yan siyasa na nan a doron tsofaffin hanyoyin baya na tafiyar da al’amura, babu wani canji da zai faru. Tsare-tsare suna da muhimmanci domin sukan yi ƙarko, kuma su ci gaba da kasancewa har bayan rayuwarmu.”
A babi na 9, da Rataye na III Janar IBB ya yi bayyanai dangane da manufofin hulɗar Najeriya da ƙasashen duniya. Ya ce manufofin sun fi maida hankali a neman biyan buƙatun ƙasashen nahiyar Afrika tare da tsunduma cikin gwagwarmayar da za ta kai ga biyan waɗannan buƙatun cikin lumana. Buƙatun da Najeriya ta gabatar a zamaninsa sun haɗa da neman ƙara yawan wakilan dindindin a Kwamitin Tsaro (Security Council) na Majalisar Ɗinkin Duniya domin su haɗa da ƙasashen Afrika tare da buƙatar naɗa ɗan asalin nahiyar Afrika a muƙamin Babban Sakataren Majalisar ta Ɗinkin Duniya. A dalilin wannan kira da IBB ya yi a cikin jawabinsa ne aka naɗa ɗan asalin ƙasar Misra, Boutrous Boutrous-Ghali da Kofi Atta Anan, ɗan asalin ƙasar Ghana, wanda ya gaje shi, a muƙamin Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniyar. Kuma ya bayyana buƙatar a naɗa wani ɗan Afrika a muƙamin Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙasashen da Ingila ta Yaye, (Commonwealth). Ita ma wannan buƙata ta samu shiga da naɗin da aka yi wa Cif Emeka Anyaoku a matsayin Babban Sakatare na Ƙungiyar ta Ƙasashen da Ingila ta Mulka. Haka nan, a zamanin mulkinsa, Najeriya ta shiga tsakani a Yaƙin Basasar Kasar Liberia. Wannan shiga tsakanin ne ya kai ga ƙare yaƙin da wanzar da zaman lafiya a ƙasar. Sai kuma dawo da hulɗar jakadanci tsakanin Najeriya da Isra’ila bayan an daɗe da katse dangantakar. Har wa yau dai, Najeriya ta ƙirƙiro Kungiyar Kasashen Duniya Matsakaita, domin cin ma manufofinsu a al’amuran diflomasiyya a duniya, (Concert of Medium Powers).
Wannan kuwa ya zo ne bayan manyan ƙasashen duniya sun gama Yaƙin Cacar Baki tsakaninsu, (Cold War). Ƙungiyar ta cike makwafin Ƙungiyar Ƙasashe ‘Yan ba Ruwanmu, (Non-Aligned Movement).
Gwamnatin IBB ta fito da hukumar da kan tura kwararru ‘yan Najeriya kasashe masu tasowa da suke da buƙata domin taimaka musu wajen raya ƙasa, (Technical Aid Corps). Haka nan Najeriya ta zama mai masaukin taron Ƙungiyar Haɗa Kan Ƙasashen Afirka, watau Organization for African Unity (OAU), a makwafin Birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha, lokacin da ‘yan tawaye suka yi wa Birnin tsinke, har daga ƙarshe ma suka ƙwace iko da shi. Wani sabon tafarkin diplomasiyya da Gwamnatin IBB ta kawo wa Najeriya, shi ne maida hankali domin biyan bukatun tattalin arzikin ƙasar a huldarta da ƙasashen duniya, (Economic Diplomacy).
A Babi na 10, Janar Babangida ya yi cikakken bayani kan manyan dalilan da suka haddasa adawa da mulkinsa, tare da haddasa tashe-tashen hankali. Dalilan da ya bayyana su ne, kashe Dele Giwa da bam ɗin da aka aika masa a cikin wasiƙa da yunƙurin juyin mulki da Mamman Vatsa da Gideon Orkar suka yi da kwarmato a kan shigar Najeriya Ƙungiyar Kasashen Musulmi, (Organization for Islamic Cooperation – OIC). Sai kuma tashe-tashen hankali saboda tsarin Tsuke Bakin Aljihun Gwamnati mai suna SAP, wanda ya janyo hauhawar farashi da ƙara kuɗin man fetur, wanda gwamnatin ta yi, ga kuma barin jirgin saman sojoji mai lamba NAF C-130; wanda ya jawo halakar matasan hafsoshin soja 159.
Wata marubuciya mai suna Lindsay Chervinsky, wadda ta rubuta littafi mai suna, The Cabinet, ta ce, “Tun lokacin da maza suka fara yin mulki, mata kan taimaka musu a tafiyar da mulkin nasu.” A babi na 11, IBB ya tabbatar da gaskiyar wannan magana, inda ya yi maganganu dangane da uwargidansa Maryam, wadda ta kula da harkokin gidansa. A cewarsa, ɗaya daga cikin ƙa’idojin da rundunar soja ke amfani da su wajen tantance cikar darajar hafsoshinta, shi ne wanzuwar cikakken zaman lafiya tsakanin mai gida da iyalinsa. Ya ce shi kam ya sami wannan zaman lafiya a gidansa dalilin matarsa tagari, Maryam. Ya sadaukar da duk babi na goma sha ɗaya domin tunawa da ita. Ya bayyana yadda mahaifanta suka yi mata tarbiyya da yadda suka haɗu, har ya aure ta da ƙoƙarin da ta yi a lokacin da ta shugabanci Ƙungiyar Matan Hafsoshin Sojojin Najeriya, (Nigerian Army Officers’ Wives Association – NAOWA), da irin hidimar da ta yi a matsayinta na Uwargidan Shugaban Kasa (First Lady) da ayyukan da ta bijiro da su a shirin nan nata na Inganta Rayuwar Matan Karkara, (Better Life for Rural Women). Janar IBB ya yabi himmarta da yin aiki tuƙuru cikin tsari da rashin kasala da jajircewarta tare da burin cin ma manufa a duk wata harka da ta sa a gaba.
A shafi na 236 Janar IBB ya ce, “Wani lokaci, nakan ji kamar dare da yinin kowace rana ba su ishe ta hidima ba. Ta kasance tana yin ayyukan matar aure da hidimar ‘ya’ya da tafiyar da harkokin gidanta da gwagwarmayarta ta rajin kare haƙƙin matan karkara, sannan kuma gaba da duk wadannan, ita ce abokiyar rayuwata. Ta ja ‘ya’yanmu a jika sosai, kuma tana bibiyar duk abin da suke ciki a kowane lokaci. Ni da ita mukan yanke shawara bisa abin da ya fi dacewa da su kuma muna ƙoƙarin kare su daga irin kwaramniyar da fitattun mutane kan shiga. Ba mu so kasawa da kurakurenmu su shafi rayuwarsu.” Ya karasa da cewa ya gode wa Allah bisa rayuwar da suka yi shi da Maryam da kuma albarkar haihuwar da Ya ba su. Ya ce jure rayuwa ba tare da ita ba jan aiki ne, to amma ya kan ji dama-dama idan ya tuna irin zaman daɗin da suka yi, ga shi kuma koyaushe yana tunawa da ita,

A babi na 13, wanda shi ne babin ƙarshe a cikin littafin, IBB ya yi bayani a kan rayuwarsa bayan yin ritaya. Ya ce bayan ya koma mahaifarsa, Minna, a ranar 27 ga Agusta, 1993, yanzu shi dattijo ne, kuma uban ƙasar-Najeriya, wanda ba ya cikin wata jam’iyyar siyasa, mai zaman kansa. Yakan yi baƙi tare da tattauna al’amuran rayuwa da su. Yakan ba jama’a, ko tsofaffi ko matasa da kungiyoyi shawarwari daga abin da ya sani ko yake hange. A cewarsa, yanzu haka babu makon da zai zo ya wuce ba tare da ya yi baƙi ba.
A ƙarshen bayanansa, Janar IBB ya bayyana farin cikinsa saboda Najeriya ta sami karɓuwa a matsayin ƙasa ɗaya, mai ƙarfi kuma Tarayyar da ba za ta wargaje ba. Don tabbatar da wannan fata nagari, ya ware shafukan ƙarshe na littafi domin faɗakar da matasan Najeriya ‘yan shakaru 30 a duniya. Ya yi kira a gare su da su zama masu ɗimbin ilmi, waɗanda Najeriya ce a gabansu, kuma waɗanda za a iya damawa da su a ko’ina a duniya. Ya ba su shawarwari kan su san ƙasarsu sosai. Su ƙulla alaƙa da jama’a a ko’ina. Su yi wa ƙasa hidima cikin gaskiya da ƙwazo. Su haɗa jin ƙai da ƙarfin hali a shugabanci. Su rungumi tsarin Tarayyar Najeriya a matsayin wani ginshiƙi da bai kamata a rusa ba. Su ba tsarin mulkin dimokuraɗiyya muhimmanci. Su kiyayi nuna bambanci da wariyar al’ada. Su guje wa son zuciya. Su zama masu riƙo da addini kuma masu haɗin kai da son juna. Ya kara shawarce su da su sa a cikin ransu Najeriya ce ƙasar baƙar fata mafi muhimmanci a duniya, sa’an nan zamaninsu ne zai zo nan gaba.
A bisa al’ada akan yi ‘godiya’ ne ga waɗanda suka bada gudunmowa wajen wallafa littafi a farkon littafin, amma a wannan littafi na IBB, wanda ya sadaukar da shi ga mahaifansa da matarsa Maryam, wadda ta faranta masa rai da kyautata masa, an kai wannan godiya ne a ƙarshen littafin. Bugu da ƙari, ya sadaukar da littafin ga sojojin da suka rasu a bakin aiki. Kuma ya ce wannan littafi sakamakon aikin da mutane da dama suka yi ne, har ma ya ambaci sunayen wasu, wasu kuwa ya gode musu kurum.
An yi ratayen ƙarin bayani, watau appendices, har guda shida, waɗanda suka cika shafi 81, haɗe da:
Rataye na I – Jawabin farko na IBB bayan kifar da mulkin Manjo Janar Muhammadu Buhari, a ranar 27 ga Agusta, 1985.
Rataye na II – Cikakkiyar tattaunawarsa da Mujallar TELL, a ranar 24 ga Yuli, 1995, inda ya bayyana cewa tun a lokacin ya shiga rubuta wannan littafi.
Rataye na III – Jawabinsa a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya, watau UN a matsayin Shugaban Najeriya da kuma Shugaban Ƙungiyar Haɗa Kan Ƙasashen Afrika, watau OAU a ranar 4 ga watan Oktoba, 1991. A cikin jawabin, ya buƙaci a samar da Sabon Ƙudurin Duniya, domin kawo ci gaba a Afrika.
Rataye na IV – Takardar sakamakon ƙididdigar ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen 12 ga Yuni, 1993, inda aka nuna cewa MKO Abiola ya yi nasara a jihohi 20 da Federal Capital Territory (FCT), yayin da Bashir Tofa ya ci a jihohi 11.
Rataye na V – Jawabin IBB ga sabbin ‘yan Majalisa a ranar 27 ga Yuli, 1992 kan Sabon Tsarin Ƙasa.
Rataye na VI – Jawabinsa a taron tunawa da mulkinsa, mai taken: The Babangida Regime: Problems and Perspective of Interpretation, wanda aka shirya a Hill Station Hotel, Jos, daga 13-15 ga Oktoba, 2000.
A Babi na 12 na littafin, wanda kuma shi ne babi mafi tsawo – an tattauna batun soke zaɓen 12 ga Yuni, 1993. A nan ne IBB ya bayyana dalilan soke zaɓen da ya haddasa tunzuri mafi muni a zamanin mulkinsa. Yayin da ya ke cewa Janar Sani Abacha ne ya jagoranci sojojin da suka hana tabbatar da sakamakon zaɓen, wasu sun ce tun da abin ya faru ne a ƙarƙashin mulkinsa, bai kamata ya jingina laifin ga wani ba. Sai dai IBB ya musanta cewa ya yi hakan don kare kansa, yana mai cewa ya kalli makoma da maslahar ƙasa ne.
A cewarsa: “Na yanke shawarar soke zaɓen na 1993 ne, domin kauce wa rikicin da ka iya rusa ƙasar nan.” (shafi 288).
A lokacin ƙaddamar da littafin a 20 ga Fabrairu, 2025, IBB ya furta a gaban mahalarta taron da suka haɗa da Shugaban Ƙasa mai ci a yanzu, tsofaffin Shugabannin Najeriya huɗu, da tsoffin Shugabannin Ƙasashen Ghana da Liberia cewa:
“Ba shakka, an gudanar da gamsasshen zaɓe, mai inganci a ranar 12 ga Yuni, 1993. Amma abin takaici shi ne, gwamnatin da ta shirya zaɓen, wanda ya kusan zama cikakke, ita ce ba ta kammala bayyana sakamakonsa ba. Wannan babban kuskuren ne mai girma a tarihance.”
Ya kuma bayyana a fili cewa M.K.O Abiola ne ya lashe zaɓen. Wannan amincewa da ya yi, wadda wasu suka yi la’akari da ita a matsayin jarumta, tana iya taimakawa wajen wuce batun 12 ga Yuni.
A ƙarshe, littafin A Journey in Service (Tarihin Rayuwar Hidimar Ƙasa) na IBB ya ƙunshi kyawawan abubuwa da akasinsu da dalilan da su ka haifar da rigingimu a ƙasa. Yayin da soke zaɓen 12 ga Yuni ya mamaye tunanin jama’a, ya kamata a gane cewa gudunmawar da Babangida ya bayar a fannonin siyasa da tattalin arzikin Najeriya ciki har da kawo Zaɓen ‘Yar Tinƙe (Option A4) wanda ingantaccen tsarin zaɓe ne a bayyane, wanda wasu ke kira da “Ƙato-Bayan-Ƙato,” wanda kowa na ganin sakamakonsa a bayyane. Sai kirƙiraro sababbin jihohi 11 da ƙananan hukumomi 288 da sake fasalin hukumomin tsaro inda gwamnatinsa ta kafa hukumomin tsaro da tattara bayanan sirri, (State Security Service – SSS) da (National Intelligence Agency -NIA) da (Defence Intelligence Agency -DIA). Haka nan IBB ne ya farfaɗo da tattalin arziki da samar da tsarin kamfanoni masu zaman kansu, a inda harkokin banki da kafofin watsa labarai da kasuwanci suka habaka. A zamaninsa Fadar Gwamnatin Tarayya ta koma sabon Babban Birnin ƙasar, Abuja, daga Legas.
Batun soke zaɓen Shugaban Ƙasa na 12 ga Yuni, 1993, daga dukkan alamu yana neman ya shafe dukkan waɗannan nasarori da IBB ya samu. Sai dai kuma wasu za su ce idan aka yi haka, ba a yi adalci ba — musamman idan aka yi la’akari da muhimmancin tasirin waɗannan matakai, waɗanda ba a taɓa ɗaukar irinsu ba, sai a mulkin Babangida.
Wasu masu nazarin tarihin Babangida kan batun soke zaɓen 12 ga Yuni, suna ganin ya bayyana gaskiya, yayin da wasu ke yi wa IBB kallon mai son kansa saboda a ganinsu, wasu daga cikin waɗanda aka ɗora wa alhakin batun sun mutu, balle a ji ta bakinsu a kan maganar. Duk da haka, za a iya ba da shawarar cewa, kowa ya nutsu, a kawo ƙarshen wannan batu na 12 ga Yuni, musamman idan aka yi la’akari da matsayar ƙarshe ta IBB kan batun. A yayin gabatar da littafin na tarihin rayuwarsa, a ranar 20 ga Fabrairu, 2025, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, kamar yadda Gidan Rediyon BBC ya ruwaito, ya ce, “Babu shakka, an yi sahihin zaɓe cikin ‘yanci da gaskiya a ranar 12 ga Yuni, 1993. Duk da haka, babban abin baƙin ciki a tarihi shi ne, hukumar da ta tsara zaɓen mai inganci, kuma ta gudanar da shi, ba ta kai ga kammala shi ba. Wannan babban kuskure ne a tarihi, kuma ya zama babban abin nadama matuƙa. Jama’a na da haƙƙin su sa rai zan bayyana nadama a fili.” A fili IBB ya bayyana cewa M.K.O Abiola ne ya lashe zaɓen.
Mutane da dama sun ɗauki wannan furuci a matsayin nadama, wanda ka iya kawo ƙarshen zancen soke zaɓen 12 ga Yuni. Babangida yana magana ne a gaban taron manyan mutane, ciki har da Shugaban Ƙasa na yanzu da tsofaffin Shugabannin Ƙasa huɗu na Najeriya, da tsofaffin Shugabannin Ƙasashen Ghana da Laberiya. Wannan ne irin dandalin da yake buƙata domin bayyana ta bakinsa dangane da abubuwan da suka faru a zamanin mulkinsa.
Bayan kammala karatun wannan littafi na tarihin rayuwar Babangida, wanda a cikinsa ya fayyace al’amura masu yawa kuma da zurfi, ba zan iya musanta maganar David Torrance, ɗan jarida kuma marubuci ba; wanda ya ce, marubutan tarihin siyasa sukan rubuta irin waɗannan littattafai ne da nufin saita tarihi, na abin alfaharin da za su bar wa ‘yan baya domin a rinƙa tunawa da su. Daga ƙarshe dai, duk abin da kowa zai iya cewa game da Babangida, littafin A Journey in Service (Tarihin Rayuwar Hidimar Ƙasa), yana gayyatar kowa ya karanta dalilan da suka sa ya ɗauki wasu matakai a lokacin ayyukansa na soja da zamaninsa na shugabancin ƙasar nan.
_________
Dokta Bukar Usman, OON, Tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja (17 ga Maris, 2025)













