GWAMNA MALAM DIKKO YA YI RASHIN MAHAIFIYA
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Allah yi yi wa mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa rasuwa. Hajiya Safara’u ta rasu tana da shekaru 93.
A wata sanarwa, wacce Babban Sakataren Watsa Labaran Gwamnatin Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed ya sanya wa hannu, an bayyana cewa: “Da cikakken alhini, Gwamnatin Jihar Katsina na sanar da rasuwar Hajiya Safara’u Umaru Baribari, mahaifiyar Gwamna Dikko Umaru Radda.”
Sanarwar ta bayyana cewa, Hajiya Safara’u ta bar duniya daren jiya Asabar (22/09/1446, daidai da 22/03/2025) tana da shekaru 93. Ta kasance mace mai karimci da mutunci, wadda hikimarta ta samo asali daga dogon tarihin rayuwa.
“Baya ga kasancewarta mahaifiyar Gwamna Raɗdɗ, Hajiya Safara’u ta reni shugabanni da jiga-jigan al’umma na tsararraki da dama. Daga cikin ‘ya’yanta akwai Hakimin Raɗɗa na yanzu, Alhaji Kabir Umar Raɗɗa, da kuma Hajiya Hauwa Umar Radda, tsohuwar matar marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’adua.
“Gwarzuwa ce ta asalin Fulani, Hajiya Safara’u ta bar gadon nagarta da ya zarce zuwa sauran al’umma, ba iyalanta kaɗai ba. Darajarta ta gaskiya, juriya da hidima ga al’umma za su ci gaba da ba wanzuwa tsawon lokaci.”
A yau Lahadi za a yi jana’izarta, da misalin karfe 4:00 na yamma a garin Raɗɗa, Jihar Katsina.
Muna miƙa ta’aziyyarmu tare da addu’ar Allah Ya ji ƙan Hajiya Safara’u, Ya gafarta mata kuma ya ba ta Jannatul Firdaus.













