TSOKACINMU NA YAU (19)
Yau Laraba, 19-Ramadan-1446, Hijirar Manzon Allah (saw), wacce ta yi daidai da 19-Maris-2025, Miladiyya.
A yau tsokacinmu zai ta’allaƙa ne wajen ƙarfafa gwiwa da kira ga matasa, game da zaman kashe wando. Ya kai matashi, ka gaya wa kanka gaskiya. Kada ka sake ka ce za ka zauna haka nan babu aiki ko sana’a. Ka kama sana’a komai ƙankantarta, ka nemi falalar Allah da ita, za ka rabauta.
Kada ka sanya girman kai a rayuwa. Kada ka kashe zuciyarsa da riƙon ko tumasanci. Babu abin da haka zai haifar maka sai ƙasƙanci da wulaƙanci.
Allah sa mu dace, Amin.
Mu wuni lafiya.
Naku,
Bashir Yahuza Malumfashi,
Editan Mujallar Taskar Gizago.













