A Yayin Da Aka Kashe Janar Saura Wa Kuma Ya Rage?
Daga Danladi Z. Haruna
__________
Labarin rasuwar tsohon jami’in tsaro kuma tsohon mai magana da yawun rundunar tsaro ta Najeriya, Manjo-Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), yayin da yake tsare a hannun ‘yan bindiga, babban rashi ne mai karya zuciya, wanda ya jefa ɗaukacin Arewa da ma Najeriya baki ɗaya cikin juyayi da alhini.
Janar Rabe, wanda ya fito daga Ƙaramar Hukumar Batsari da ke Jihar Katsina kuma ya kwashe shekaru yana yi wa ƙasarsa hidima da yaƙar ta’addanci, ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya na ciwon suga da hawan jini.

Kamar yadda sanarwa daga Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar, Janar ɗin ya rasu ne a yayin da yake tsare a sansanin ‘yan bindigar, bayan o sace shi da suka yi, tare da matarsa, tun ranar 30 ga watan Mayu na bana, a kan hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli.
Wannan mummunan lamari, wanda Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar, babban saƙo ne da ke nuni da irin barazanar da kowanne ɗan ƙasa ke ciki a yau; inda hatta ƙwararrun dakarun soja da suka yi hidimar kare ƙasarsu a tsawon rayuwarsu, ba su tsira daga barazanar tsaro ba.
A wani bidiyo, wanda ya karaɗe kafafen sada zumunta, an nuno Janar ɗin, kafin rasuwarsa, inda yake roƙon a kawo masa ɗauki saboda halin rashin lafiya, ya sa zukata sun karaya. Kuma ya nuna yadda Arewa ta zama fagen fama – babu wanda ya isa ya bugi ƙirji ya ce zaune lumui ake.
Ga shi dai manyan masu faɗa a ji da manyan jami’ai masu ƙwarewa suna gangarawa a hannun mutanen da ko “alu ambaki” ba su iya ba, ballantana “abacada.”
Ga mai hankali, ya san cewa yanzu ba lokacin zargi ba ne. Ba lokaci na surutu mara amfani ba ne. Ba kuma lokaci ne da shugabanni za su cigaba da zabga ƙarya da labarai marasa kan gado ba.
Lokaci ne da Arewa da ma Najeriya baki ɗaya suke buƙatar gaggawar mafita, musamman ta hanyar sauya dabarun zamantakewa. Lokaci ne da gwamnati za ta samar da dabarun yaƙi na zamani.
Masu wannan aika-aika sun nuna a zahiri cewa, tuni sun bijire wa tsofaffin hanyoyin da aka saba da su na yaƙin kuma ba sa buƙatar sulhu ko lallaɓawa.
Ya zama dole a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki kan masu bai wa dakarun ta’addanci bayanai (informants). Wajibi ne shugabannin Arewa na siyasa, na gargajiya da na addinai su ajiye bambance-bambancensu gefe guda, domin ceto yankin daga rugujewar tattalin arziki da yunwar da ke tafe saboda rashin zaman lafiya.
Muna roƙon Allah ya ji ƙan Janar Rabe Abubakar da sauran bayin Allah da suka rasa rayukansu, ya bai wa iyalansa juriya, sannan ya tseratar da matarsa da ke hannunsu. Allah ya dawo da zaman lafiya mai ɗorawa a ƙasarmu.
Malam da Malama masu karatun wannan tsokaci, Idan har kun damu da halin da Arewa take ciki, ku danna maɓallin “Share” domin yaɗa wannan saƙon, ya kai ga kunnuwan masu ruwa da tsaki a gwamnati.
__________












