• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, May 2, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Rigakafi Ne Babban Jagoran Yaƙi Da Sankarar Mahaifa – Janar Buratai

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

webmaster by webmaster
May 29, 2023
in Babban Labari
4
Rigakafi Ne Babban Jagoran Yaƙi Da Sankarar Mahaifa – Janar Buratai
28
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Rigakafi Ne Babban Jagoran Yaƙi Da Sankarar Mahaifa – Janar Buratai
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), CFR, ya ja hankalin al’umma, musamman mata da su maida hankali wajen kula da lafiyarsu ta hanyar kula da matakan rigakafi, domin yaƙi da cutar Sankarar Mahaifa da ta Yoyon Fitsari da ke barazana gare su a yayin ɗaukar ciki ko wajen haihuwa.

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026

Buratai, wanda shi ne Garkuwan Keffi kuma Betaren Biu, yayi wannan jan hankali ne a yayin gabatar da jawabi, a matsayinsa na Babban Baƙo na Musamman, a Bikin Ƙaddamar da littafin wasan kwaikwayo mai suna NADAMA, wanda ya gudana a zauren taron Aso na International Conference Centre, Abuja a ranar Asabar (6-4-2023).

Tun da farko, ya gode wa marubuciyar littafin, Malama Fatima Sanda Usara, da ta gayyace shi a matsayin Babban Baƙo na Musamman. Haka kuma ya yaba mata saboda namijin ƙoƙarin da ta yi na rubuta littafin, wanda ya ce zai taimaka matuƙa wajen faɗakar da mata, domin daƙile wannan cuta da ke sanadiyyar halaka mata da dama a ƙasar nan.

Ya kuma gode wa Shugaban Kwamitin Ƙaddamarwa, Farfesa Umar Adam Katsayal, wanda kuma ya kasance mai sharhi kan littafin. Ya taya shi murna, kasancewar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi muƙamin Shugaban Jami’ar Sufuri ta Gwamnatin Tarayya da ke Daura na farko.

Da yake karin bayani game da haɗari da ƙalubalen da ke tattare da cutar Sankarar Mahaifa, Janar Buratai ya ce a wani nazari da ya gudanar, ya karanta nazarin Farfesa Oliver Ezechi, Daraktan Bincike na Cibiyar Binciken Cututtuka ta Najeriya (NIMR), wanda ya bayyana cewa: “Akwai ƙiyasin cewa mata a Najeriya kimanin miliyan 36 da ke tsakanin shekara 15 zuwa sama, suna fuskantar barazanar kamuwa da cutar Sankarar Mahaifa. Haka kuma a kowace shekara ana magance majinyata dubu 12, ake kuma samun mutuwar mata dubu 8. Hakan ke nuna cewa a kullum ana samun masu kamuwa da cutar adadin 33, inda mata 22 ke rasa ransu a kowace rana a Najeriya.”

A kan haka Buratai ya buƙaci hukumomi, majalisu da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar lafiya da ɗaukacin al’umma da su maida hankali wajen rigakafi domin a taru a kashe mahaukacin kare, ma’ana, a magance cutar Sankarar Mahaifa da Yoyon Fitsari da ke barazana ga dubban mata a Najeriya.

Da ya juya kan littafin NADAMA kuwa, ya ce saboda muhimmancinsa, yana shawartar al’umma da su mallaki littafin, domin fa’idantuwa da ilimin da ke cikinsa.
“Yana koyar da tsarin kiwon lafiya, kamar yadda yake gargaɗi game da munanan laifukan da ke faruwa a cikin al’umma, musamman masu cutar da mata,” in ji Buratai.

Haka kuma ya buƙaci da a fassara littafin zuwa yarukan Ingilishi da Yarabanci da Ibo, domin saƙonsa ya mamaye ko’ina. A kan haka ya yi alƙawarin zai tallafa da kuɗi, domin ganin an samar da na Ingilishin, sannan ya buƙaci ɗaya daga manyan mata da suka halarci taron, Uwargidan tsohon Gwamnan Jihar Imo, Zinariya Neoma Nkechi Rochas Okorocha da ta bayar da tallafi wajen ganin an fassara littafin zuwa harshen Ibo.

Bikin dai ya samu halartar muhimman mutane daga sassa daban-daban na ƙasar nan, waɗanda suka haɗa da Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, Shugaban Hukumar Al’amuran Hajji ta Najeriya da Farfesa Ahmed Ahidjo, Shugaban Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da Farfesa Umar Adam Katsayal, Shugaban Jami’ar Sufuri ta Tarayya Daura da Farfesa Ibrahim Malumfashi na Jami’ar Jihar Kaduna da wakilan hukumomin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya da na Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa da sauran al’umma, maza da mata.

Previous Post

Dokta Bukar Usman: Garkuwan Adabi Ya Cika Shekara 80

Next Post

Sharhi A Kan Sharhi: Nazari da Sharhin Ayyukan Adabin Bukar Usman

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Babban Labari

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume
Babban Labari

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel
Babban Labari

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026
Next Post
Sharhi A Kan Sharhi: Nazari da Sharhin Ayyukan Adabin Bukar Usman

Sharhi A Kan Sharhi: Nazari da Sharhin Ayyukan Adabin Bukar Usman

Comments 4

  1. Ja'en Anas says:
    3 years ago

    Masha Allah

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      3 years ago

      Alhamdu lillah!

      Reply
  2. Yunusa Makarfi says:
    3 years ago

    Saura Sharhi kan Littafin NADAMA, da na hango an kaddamar da shi a Abuja kwanakin baya

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      3 years ago

      In sha Allah!

      Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Abin Lura Game Da Bazuwar ‘Yan Kasuwar Sola Da Janareta A Najeriya

Abin Lura Game Da Bazuwar ‘Yan Kasuwar Sola Da Janareta A Najeriya

October 23, 2025
DISCOS or Agents of Darkness?

DISCOS or Agents of Darkness?

April 25, 2024
Nigeria at 64: How Far So Far?

Nigeria at 64: How Far So Far?

October 7, 2024
Bayan Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihar Katsina: Ya Kamata A Tallafa Wa Iyalan Mutanen Da Aka Tarwatsa

Bayan Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihar Katsina: Ya Kamata A Tallafa Wa Iyalan Mutanen Da Aka Tarwatsa

October 15, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)
  • General Buratai (A Poem)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

April 27, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.