Idan ana maganar yi wa al’umma hidima dangane da bunƙasa ilimi da kare al’adun gargajiya a Najeriya, sunan Dokta Bukar Usman Biu dole ya buga tambura. Wannan bawan Allah ya cika shekara 80 cif a duniya. A yau za mu yi nazari da tariyar irin gudunmowar da wannan muhimmin mutum ke ba al’umma ta fuskoki da dama, musamman ma ilimi.
A ranar 10 ga watan Disamba, 2022, Doka Bukar Usman, D. Litt, M.IoD, OON ya cika shekara 80 a rayuwa. Kasancewar a irin wannan rana ta shekarar 1942 ya zo duniya, Garkuwar Adabi, kamar yadda ake masa laƙabi, bai tara mutane an yi shagulgula ba kamar yadda al’adar wasu mutane take. Mutum ne shi jajirtacce, wanda ya kai ƙololuwar ɗaukaka a aikin gwamnati kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Nazarin Al’adun Gargajiya ta Najeriya (Nigerian Folklore Society) a halin yanzu.
Irin yadda ya ririta rayuwarsa tun daga tushe zuwa ɗaukakar matsayi, abin koyi ne ga al’ummar wannan zamani da ma masu zuwa nan gaba. Tun da farko ya fara aiki ne a matsayin ƙaramin jami’in gwamnati a Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya, inda a shekarar 1969 ya kammala digirinsa a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Hazaƙarsa da himmarsa a aiki sun ba shi damar samun ɗaukaka da ci gaba, inda ya riƙa samun ƙarin girma a lokacin da ya dace. Ta kai ga sai da ya kai muƙamin Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya yi ritaya daga aiki a shekarar 1999.
Al’ada ce ta manyan mutane, idan suka yi ritaya ba su ƙara yin wani aiki sai zama da hutawa a gida amma shi Dokta Bukar sai ya zaɓi ya zama mai yi wa al’umma hidima ta muhimmiyar hanyar nazari da rubuce-rubuce, wanda babu shakka ta haka yake taimakawa wajen bunƙasa ilimi da faɗakar da al’umma da adana tarihi domin al’umma mai zuwa nan gaba. Ya kasance yana amfani da dukiyarsa wajen ɗaukar nauyin nazari da binciken ilimi, sannan yakan wallafa muhimman littattafai a fagagen ilimi daban-daban, musamman ma adabi da sauransu. Kuma mafi yawa daga littattafan da yake samarwa ta hanyar Gidauniyar Bukar Usman, kyauta yake raba su ga al’umma da makarantu da cibiyoyin ilimi na sassan ƙasar nan, har ma da ƙasashen waje.
A lokacin da ya yi ritaya a shekarar 1999, Dokta Bukar yana da shekara 57 a duniya. Kafin sannan, babu wanda ya san shi da harkar rubuce-rubuce, idan ba rubuta bayanan aiki a fayil-fayil na ofis ba. Sai ga shi saboda himmarsa, cikin shekara 20 ya zama wani mashahurin marubuci, wanda sautinsa ke ruri a duniyar rubutu a fagen adabi, ilimin gudanarwa, siyasa da sauran fagage masu muhimmanci a rayuwa.
Kamar yadda ya bayyana a ɗaya daga cikin littattafansa mai suna My Literary Journey, Dokta Bukar ya fayyace yadda aka yi ma ya fara harkar rubutu, domin kuwa ya ce tun da farko ba a haife shi da jinin marubuta ba.
“A batun gaskiya, lokacin da na zaɓi in fara rubuce-rubuce bayan na yi ritaya daga aikin gwamnati, ban taɓa tsammanin zan iya ɗorewa ba. Na rubuta littafin tarihin rayuwata cikin shekarar1992, inda na kammala aka wallafa shi a shekarar 2006. Amma sauran rubuce-rubucen ƙirƙira da na adabi da sauran fagage, na fara su ne daga bisani,” inji shi.
A matsayinsa wanda ya yi wa harkar rubutu shigar sojan Badakkare, ya aminta da cewa ta hanyar adabi za a iya yi wa al’umma hidima. Babu shakka ya samu gogewa da ƙwarewa wajen sanin inda ke wa al’umma ciwo. Don haka ya san wane maudu’i ya kamata ya yi rubutu a kansa. Tun da farko bai samu horarwa a fagen rubutun ƙirƙira da adabi ba amma saboda himmarsa, sai ga shi har ya fi mai kora shafawa, ma’ana “har ya gagari ’ya’yan gado,” kamar yadda marigayi Mamman Shata Katsina ya faɗa a waƙarsa ta Bakandamiya. Ma’ana sai ga shi ya zama kamar ruwan dare gama duniya a fagen wallafa, domin kuwa ko’ina za ka ga littattafansa kuma za ka ga masana na nazari da bitar su a jami’o’i da kwalejojin ilimi.
Kamar yadda shi da kansa ya bayyana, a zamanin da yake ɗalibi bai samu damar karanta littattafan ƙirƙira ba, domin kuwa a lokacin babu su da yawa. Amma duk da haka ya kasance mutum mai ƙwazon karance-karance, wanda haka ya ba shi damar samun sha’awar yin rubutu. “Ban samu tagomashin horo a fagen rubutu ba amma na kasance mai ƙwazon karance-karance matuƙa. Idan aka ce kai mai yawan karatu ne, za ka iya koyon wata hikima da fasaha koda ba a horar da kai a aji ba.” Ya ce haka kuma a duk abin da ya rubuta yakan ba ƙwararrun masana su duba domin gyare-gyare da shawarwari, shi ya sanya ayyukansa suke fitowa da nagarta sosai.
“Haƙiƙa na samu ilimin cewa a duk lokacin da mutum ya sanya kansa a harkar rubutu, zai fuskanci ƙalubale daban-daban na musamman da suka shafi ƙirƙira, nazari bincike da kuma wallafa. Mutum zai kasance cikin aiki na tsawon lokaci a kan daftarin da ya rubuta,” inji Bukar, a yayin da yake bayyana faɗi-tashinsa a harkar wallafa.
Idan muka waiga baya daga lokacin da ya faro rubuce-rubuce, za mu iya cewa ya yi nasarar murƙushe dukkan ƙalubalen da ya riƙa fuskanta a wannan fage da ya saka kansa.
Littafinsa na farko shi ne Voices in a Choir, sai kuma Hatching Hopes (Cikar Buri), wanda na tarihin rayuwarsa ne, ya fara rubuta shi a shekarar 1992, aka wallafa shi a 2006.
Yakan yi rubutu ne a harsunan Ingilishi da Hausa. Babban aikinsa a harkar Adabin Hausa, shi ne babban kundin Taskar Tatsuniyoyi, wanda ke ƙunshe da shafuka 652. A Ingilishi kuwa, ya samar da littattafan tatsuniyoyi daban-daban, wadanda suka hada da The Bride Without Scars and Other Stories da The Stick of Fortune da kuma Girls in Search of Husbands (waɗanda ke ƙunshe da tatsuniyoyi 26). Ya yi aiki sosai wajen zaƙulo tatsuniyoyi masu daɗi da jan hankali, masu koya darussa ga musamman yara da ma al’umma baki ɗaya.
Ya zama wajibi ga al’umma su miƙa godiya ga mawallafi Duve Nakolisa, wanda shi ne mutum na farko a shekarar 2005 da ya ja ra’ayin Dokta Bukar kuma ya ƙarfafa masa gwiwa da cewa ya kamata ya jaraba hannunsa a rubuce-rubucen da suka shafi ƙirƙira da adabi. Ya ankara da himmar marubucin ne, bayan wallafa littafinsa mai taken Voices in a Choir. Tun daga lokacin kuwa ya tunkari wannan harka, inda ya zuwa yanzu ya samar da littattafai daban-daban fiye da 40 a wannan fage. Haka kuma ya ɗauki nauyin nazari da tattara tatsuniyoyin al’ummun sassa daban-daban na Najeriya da suka haɗa da na ƙasar Yarabawa da Ibo da na Tibi da sauransu.
Babu shakka Bukar Usman ya cika mutum mai kishin ƙasa da al’ummarsa, wanda ke sanya darasi ga matasa da ma dattijai, cewa yawan shekaru ba za su iya hana mutum yi wa ƙasarsa da al’ummarsa hidima ba.
A yayin da ya cika shekara 80 a duniya, muna roƙon Allah Ya ƙara masa lafiya da yawan shekaru tare da azamar ci gaba da yi wa al’umma hidima.













