KADARKO
~~~~~~~
Ɗan uwa kada ka yi hanzari.
Rayuwa ba ta buƙatar sauri.
Kai dai yi juriya sanya kuzari.
A kalar ƙasa akwai jangargari.
Aiki da natsuwa mu yo nazari.
Ƙyale wancan mai son garari.
Lizimci ƙana’a ban da alfahari.
Abin da ɓoye za ya fito sarari.
Allah ta’ala majiɓincin lamari.
Ba Ya buƙatar sulu ko lusari.
A miyar daɗi sai an sa gishiri.
Shayi da madara a biɗo sukari.
Gaskiya guda ita ce aikin zahiri.
Bambancin imani kallo shi kafiri.
Bari ƙyashi Allah Shi ne yai tajiri.
Koda a inuwa babu batun ƙoƙari.
Kiyayi zuba ratata kamar kanari.
Aikinsa jaki harbi ba ya tunkuri.
Duk mai ƙishirwa ya bid’o ƙunari.
Amma kiyayi tonon munin bahari.
Allah muke roƙo Ya kai mu gari.
Ya kyautata mana kyawun ƙuduri.

~~~~~~~
© Bashir Yahuza Malumfashi, Alhamis (04-05-1438BH = 02-02-2017).
~~~~~~~












