SADAUKARWA: Tinubu Tsaye Yake Ga Manufofin Najeriya Da Afirka – Minista Idris
Daga Wakilinmu
~~~~~~~
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa sadaukar da kai da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi bai tsaya ga Nijeriya kaɗai ba, har ma da dukkan nahiyar Afrika.
Ya ce: “Tun daga lokacin da ya kama aiki, an gan shi sosai a faɗin duniya yana yayata manufofi da burukan Nijeriya da ma nahiyar Afrika.”
Ministan ya faɗi haka ne a wurin wata walimar cin abincin dare, wadda Ofishin Jakadancin ƙasar Angola ya shirya a Abuja a ranar Alhamis.
Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu yana da shauƙin ganin ya inganta mu’amalar da ke tsakanin Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika, ciki har da Angola.
Idris ya ce yanzu ana kallon Shugaban Ƙasa a matsayin uba a faɗin Afrika, wanda ke jagorantar ƙasar da ta fi kowace yawan jama’a da ƙarfin arziki a nahiyar.
A cewar sa, wannan ne ya sa aka naɗa Tinubu Shugaban Ƙungiyar Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), jim kaɗan bayan an rantsar da shi a matsayin Shugaban Ƙasa.
Ya ce: “A jawabinsa a wajen babban taron farko da ya halarta na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) a watan jiya, ya yi magana mai gamsarwa ƙwarai kan dalilan da suka sa Afrika take buƙatar sauran ƙasashen duniya su yi mata adalci, da abin da ya sa ci gaban duniya yana tattare ne da ci gaban Afrika.
Ya ce, “Wato dai manufa, idan har duniya ta ɗauki batun samun ci gaba da gaske, to tilas ne kuma ta ɗauki batun ci gaban Afrika da gaske.”
Ministan ya ƙara da cewa mafarkin Shugaba Tinubu da burinsa su ne ƙasashen Afrika su haɓaka dangantaka mai zurfi da ƙarfi a tsakaninsu wanda “zai ba da dama ga nahiyar ta samu matsayin da ya fi na da girma da ƙarfi a fagen duniya da kuma samun dama mafi girma wajen samun ‘yanci mai ɗorewa da arziki. Duk abin da ya gaza kan wannan, to ba za mu yarda da shi ba.”
Ya yi la’akari da cewa idan har ba a haɗa kafaɗa aka yi mu’amala da haɗin kai tare ba, Afrika ba za ta cin ma nasarar warware matsalolinta ba.
Idris ya ce: “Ƙoƙarin magance ɗimbin ƙalubalen da ke fuskantar nahiyar a wannan zamani – irin su rashin tsaro, fatara, rashin aiki, labarai marasa daɗi, ƙarancin hada-hadar kasuwanci a tsakanin nahiyoyi, da sauransu – duk yana buƙatar yin aiki kafaɗa da kafaɗa a matakin yanki da na nahiya baki ɗaya.
“Duk da yake akwai bambance-bambancen harsuna da al’adu da tsarin zamantakewar al’umma da na siyasa, tilas ne mu samo hanyoyin da za mu amince da su domin gabatar da matsaya ɗaya kan al’amurran da suka shafi mu su waye a matsayin nahiya, da abin da muke so mu cin ma wa a dukkan ɓangarori na rayuwa.
“Tilas mu haɗu mu tattaro tunani kan batun ci gaban ƙasa, kafa masana’antu, cinikayya, samar da aikin yi, da kuma matsayin nahiyarmu a ƙarni na 21. Yanzu haka an yi nisa wajen aiki kan hakan, don a fitar da matsaya ɗaya haɗaɗɗiya wadda za a yi aiki da ita a matakai daban-daban.”
~~~~~~~












