• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 17, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sharhi

TUKUR BURATAI: Janar, Malamin Makaranta, Marubuci Kuma Saraki

Sharhin Littafi

Dr. Bukar Usman by Dr. Bukar Usman
August 7, 2023
in Sharhi
0
TUKUR BURATAI: Janar, Malamin Makaranta, Marubuci Kuma Saraki

Littafin The Legend of Buratai

146
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Tukur Buratai: Janar, Malamin Makaranta, Marubuci Kuma Saraki

Janar Buratai, yayin ganawa da ‘yan jarida
Betaren Biu, Janar Tukur Yusufu Buratai

Daga Dokta Bukar Usman

Related posts

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

July 18, 2025
Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

December 24, 2024

~~~~~~~
Sunan Litt fiafi: The Legend of Buratai Volume 3
Sunan Marubuci: Ambasada Tukur Yusufu Buratai
Kamfanin Wallafa: Sprezzatura, Abuja
Shekarar Wallafa: 2022
Yawan Shafuka: 238
Mai Sharhi: Dokta Bukar Usman
~~~~~~~

Littafin The Legend of Buratai Volume 3 (Hikayar Jarumi Buratai) yana ƙunshe da babi 9 da shafuka 238 kuma an wallafa shi ne a 2022. Littafin, ci gaba ne daga wasu biyu da suka gabace shi, domin kuwa a can baya, an wallafa kashi na ɗaya da na biyu, inda shi kuma wannan ya kasance kashi na uku.
Wani abin lura na tsanaki shi ne, kashi na farko da na biyu na littafin nan ba su maida hankali wajen zayyano rayuwar aiki da nasarorin da Laftanar-Janar Tukur Yusufu Buratai (mai ritaya) ya samu ba, a matsayinsa na babban jami’in soja. Kasancewar Janar ɗin na da ƙishirwar bayyana wa masu karatunsa irin nasarorinsa ta fuskar aiki, shi ya sanya ya sadaukar da ɗaukacin wannan littafi (kashi na uku), domin samar da wannan bayani. Waɗanne ƙalubale ya fuskanta, wane faɗi-tashi ya sha har ya kai ga zama Janar a Gidan Sojan Nigeria?

A yayin warware jigon bayanin, tun kafin littafin ya yi zurfi, Janar Buratai ya bayyana cewa: “A ƙoƙarina na samar da gamsasshen bayani dangane da irin ƙalubale da faɗi-tashi da kwazazzabon da na biyo har na cin ma nasarar zama Janar da kuma hawa kan ƙololuwar shugabancin Gidan Sojan Nigeria, a nan zan baje komai bisa faifai, bisa fahimtata dangane da ma’anar shugabanci, ire-iren shugabanci da irin matakai da hanyoyin da na bi kuma suka taimaka mani zuwa ga nasara. Haka kuma, zan kawo wasu daga kurakuran da ya kamata mutum ya kauce ma wa, a yayin irin wannan tafiya ta neman cin ma babban buri a aiki mai wuya irin na soja. Littafin nan na ɗauke da bayanan kai tsaye dangane da rayuwata ta aiki, tare kuma da wani ɗimbin ilimi da na koya a cikin aji dangane da aikin.” (Shafi na 6).

A haƙiƙanin gaskiya, tun da farko za a iya cewa Janar Buratai ya faro aikin soja ne tun yana ƙaramin yaro, musamman ma dai zamanin ƙuruciyarsa. Kamar yadda shi da kansa ya faɗa, ya ce an haife shi ne a matsayin soja. Mahaifinsa jarumi soja ne, wanda da shi aka fafata Yaƙin Duniya Na Biyu. Wannan ya nuna cewa, idan dai ana gadon mahaifi, to za a iya cewa Buratai ya gaji aikin soja ne daga mahaifinsa. Haka kuma tun da farko, a zaɓinsa na ayyukan da yake sha’awar ya yi a rayuwa, aikin soja ne zaɓinsa na farko. Kodayake za a iya cewa al’amarin ƙaddara ne ya ba shi dama aka ɗauke shi aiki a Gidan Sojan Nigeria.

Wani abokinsa da suka yi karatu a Kwalejin Horon Malamai ta Potiskum ne ya sanar da shi cewa ana rijistar ɗaukar ɗalibai a Kwalejin Horon Jami’an Soja (NDA). Bai ɓata lokaci ba sai ya rubuta takardar buƙatar shiga kwalejin, inda ya rubuta jarabawar kuma ya samu nasara. Bayan mahaifinsa ya sanya masa albarka, aka ɗauke shi a matsayin Ɗalibin Jami’in Soja a shekarar 1981. Tun daga lokacin ne rayuwarsa ta aikin soja ta fara. Kodayake tun a Kwalejin Potiskum, akwai wani malaminsa mutumin ƙasar Indiya, wanda tun a ƙuruciyarsa ya riƙa shaida cewa ya lura da wasu halaye nasa, cewa zai zama mutum mai ɗaukaka. Dalili ke nan ma ya riƙa yi masa laƙani da “Babban Mutum” tun a lokacin yana ɗalibi. (Shafi na 18).

A littafin, Janar Buratai ya ci gaba da bayyana dalla-dalla irin matakan da ya riƙa bi a yayin aikinsa na soja, waɗanda suka kai shi ga kaiwa muƙamin Janar. Ya samar da bayanan ne da kyakkyawan nufin bayar da jagora ga ɗaliban soja da ma ƙananan jami’an da ke cikin aiki, musamman ma waɗanda ke da burin ganin sun samu ɗaukaka zuwa manyan muƙamai a cikin aikin. Waɗannan matakai, kamar yadda ya zayyana, za su iya kai mutum zuwa muƙamin babban Janar mai tauraro uku, kamar yadda shi ma ya kai, kamar kuma yadda ya samu tagomashin zama Babban Hafsan Rundunar Sojojin Nigeria, wanda ya yi mulki na tsawon watanni 66, biyo bayan kammala aikin soja na tsawon shekara 41.

Ya bayyana dalilinsa na rubuta wannan littafi kashi na uku, inda yake cewa: “Ba abu ne mai sauƙi ba ga jami’in soja ya kai ga muƙamin Babban-Janar Mai Tauraro Uku, har ya kai ga zama Babban Hafsan Rundunar Sojojin Nigeria. Akwai aƙidoji da ayyukan da na ɗabbaƙa a matsayin halayya, sannan kuma na kwantar da kai na koyi wasu muhimman abubuwa daga magabatana. Wannan halayya da ma wasu na daban, su ne tsanin da suka sada ni da nasara a Gidan Sojan Nigeria. Idan na ce zan bar waɗannan bayanai ga ƙirjina ni kaɗai, ba tare da na sanar da su ba, ban yi wa al’umma adalci ba. Don haka, Babban burina shi ne, haziƙan ƙananan jami’an soja da ke son aiki tuƙuru, su koya daga misalan da na bayyana, domin su ma su samu nasarar taka manyan muƙaman da ke cikin aikin soja, kamar yadda mu ma muka samu. (Shafi na 30).

Da yake zayyana shawarwari ga duk wani ɗalibi ko jami’in soja, mace ko namiji da ke son samun nasarar cin ma muƙamin Janar a Gidan Soja, har ya kai ga zama shugaba, Janar Buratai ya bayyana cewa, abu na farko shi ne, jami’in soja ya kasance mai karsashin gina kansa, ta hanyar koyon dukkan ilimin da ya dace. Ya ƙara da cewa, “babban abin da ya kamata jami’i mai irin wannan ƙuduri na son zama Janar ko Shugaba a Gidan Soja ya yi shi ne, ya kasance mai ƙwazo da jimirin biyayyar magabatansa, ya kasance mai jimiri, mai biyayya; sannan duk abin da zai yi a rayuwarsa, ya tabbatar ya yi shi da kyau sosai. Muddin dai kana son ka yi nasarar zama shugaba a Gidan Soja, dole ne ka riƙa yin aikinka da kyau sosai, ka zama mai ƙoƙarin yi wa saura zarra. Saboda me za ka yi haka? Saboda aikin ƙwarai shi ke haifar da kyakkyawan sakamako da kuma manyan damarmaki. (Shafi na 31).

Janar Buratai ya faɗaɗa bayanin yadda ake gina kai cikin ƙwazo da jajircewa, inda ya bayar da misali da yadda ya gina kansa tun daga farko. Ya kawo misalin yadda duk da cewa shi ƙwararren malamin makaranta ne kuma ya kammala kwas ɗinsa a NDA, amma ya yi fafutukar yin karatun jami’a, inda ya samu digiri a Tarihi daga Jami’ar Maiduguri, sannan ya ci gaba da karatu a Jami’ar Ƙwararru ta Bangladesh, inda ya samu Digiri Na Biyu a fannin Falsafar Tsaro. Haka kuma ya yi ta yin kwasa-kwasai na ƙwarewa da suka danganci aikinsa, a matsayinsa na Jami’in soja. Janar Buratai ya bayyana waɗannan matakai ba domin gadara ba, ya ce a duk inda ya shiga karatu ko halartar wani kwas, yana yin komai cikin jajircewa da ƙoƙari kuma yana samun kyakkyawan sakamako. A kan haka ya bayyana cewa babu abin da ya kai neman ilimi da yin karatu tuƙuru wajen gina mutum kuma su ke sanyawa mutum samun nasara. Ya ce ta hanyar karatu ne mutum zai yi koyi da ayyukan magabata, ya ga yadda suka samu nasara domin koyi, sannan ya ga wuraren da suka gaza ko suka yi kuskure, domin kauce wa faɗawa cikinsa. Haka kuma ya ce ta hanyar zuwa ƙaro karatu a gida da waje, mutum kan haɗu da ƙwararrun manyan sojoji, ya yi cuɗanya da su, ya koyi ilimi mai yawa. Haka kuma zai gamu da wasu ƙwararrun a farar hula, waɗanda zai koyi abubuwa masu amfani ga rayuwar al’umma, ba lallai na aikin soja ba.
Janar Buratai ya ce, “Babban abin da ke bambanta shugabanni daga kininsu da kuma mabiyansu, shi ne ƙoƙarinsu da jajircewarsu wajen bunƙasa kansu. Abin nufi a nan shi ne, a lokacin da sauran mutane ke shaƙatawa da bukukuwa da barci, a lokacin ne su kuma shugabanni na can sun taƙarƙare, sun takura wa kansu suna karatu da nazari, suna kwankwaɗar madarar ilimi da fasaha, kamar raƙumin da ya samu ruwa a sahara, bayan ya kamu da tsananin ƙishirwa. (Shafi na 95).

Haka kuma ya ƙara jaddada muhimmancin karatu da cewa, “Yadda sassarfa da motsa jiki ke taimakon jikin ɗan Adam, haka karatu ke taimakon zuciya da ruhi!” (Shafi na 98).

Kamar yadda Janar Buratai ya sake jaddadawa, lallai ne mai son zama shugaba mai nasara ya ladabtu da ɗabi’ar karatu mai yawa kuma mai zurfi, ya ƙwanƙwance, ya surfe abin da ya karanta, ya yi nazari, sannan kuma ya riƙa ƙoƙarin ɗabbaƙa abin da ya nazarta a aikace.

Sauran ƙunshiyar littafin, musamman ma Babi na 7, shafi na 103 zuwa na 154 ya ta’allaka cike da bayanai da tsokaci da nazari dangane da ƙa’idoji da sharuɗɗan shugabanci. A yayin warware ƙunshiyar bayanan, marubucin ya yi ta kama sunayen muhimman mutane daga sassan ƙasar nan daban-daban, waɗanda suka samu nasarar zama wani abu a fagagensu, ya doka misali da su. Bai tsaya nan ba, sai da ya zayyano wasu halayensu na musamman, waɗanda suka ingiza su hawa tubalin nasara. Irin waɗannan halaye sun haɗa da gaskiya, amana, dattako, hikimar tsara zance, biyayya da ladabi, rashin nuna son kai, jajircewa, himma, yarda da kai, burin samun nasara, maida hankali, karsashin jiki da kuzari, shiga sutura ta kamala da halayyar zumunci da abokantaka. Sauran halayen da ya zayyano sun haɗa da amanna da nasara, zama a cikin shiri, tsare mutuncin kai, ƙwarewa a aiki, halayyar auna al’amari tsaka-tsaki, koyon yaruka daban-daban, mallakar baiwar shugabanci da kuma bayar da misali a aikace, ba da baki kaɗai ba. Haka kuma ya kawo sauran halaye da suka haɗa da mutum ya kasance mai ruhin son samun nasara a duk abin da ya tunkara, mutum ya zama mai yawan addu’a kuma mai ƙoƙarin kauce wa maimaita kuskuren da magabatansa suka taɓa aikatawa.

Baya ga waɗannan muhimman misalai, ba nan kaɗai Janar Buratai ya tsaya ba, domin kuwa sai da ya kawo wasu misalan kuma, waɗanda suka shafi falsafa da hikimomin shugabanci. Ya kawo ma wasu daga sahihan tsakuren maganganun hikima daga bakunan hamshaƙan mutanen da aka yi ittifaƙin cewa sun samu nasara a fagagensu, a ciki da wajen ƙasar nan. Haka kuma, sai da ya shiga ƙwaryar tarihi, ya zaƙulo kalaman malaman falsafa da suka yi shuhura a duniya. Waɗannan mutane sun haɗa da Confucius (551-479) da kuma shahararre kuma ƙwararren mayaƙi, Alexander the Great (356-324 Kafin Zuwan Isa AS).

Abu ne mai matuƙar muhimmanci, a fito da batun ƙima da muhimmancin tarbiyyar kai, ga duk mai son yin nasarar zama shugaba a fagensa. Bisa wannan turba, Janar Buratai ya kawo wani tsokaci daga bakin Plato, wanda ya ce: “Mutum ya fi ƙarfin zuciyarsa, shi ne abu na farko kuma mafi daraja, idan ana batun nasarar yaƙi.”

Buratai ya kuma ƙara da cewa, “ana son jami’in soja ya kasance mai tarbiyya a kowane hali ko yanayi na rayuwarsa – yanayin saka suturarsa, yadda yake cin abinci, lokutan barci, yadda yake magana da kuma abin da yake faɗi a maganar tasa, yadda yake tafiya da kuma yadda yake mu’amala da manyansa da na ƙasa da shi. Babu yadda za a yi jami’in soja ya ce zai samu nasarar zama Janar ba tare da yana da tarbiyya ta kashin kansa ba. (Shafi na 118).

Wani abin lura da littafin nan shi ne, kasancewar marubucinsa na ƙwararren malamin makaranta, Janar Buratai ya kattaba littafin nan cikin salo da gwanancewa na musamman, kamar dai malami a gaban ɗalibansa (a nan ana nufin ɗaliban kwalejin sojoji da kuma ƙananan jami’an soja). Haka kuma ya zama wajibi a yaba wa marubucin, inda ya bambanta kansa da yadda wasu tsofaffin sojoji ke rubuta littattafan tarihin rayuwarsu, inda suke amfani da kalmomi na musamman irin na soja. Shi Janar Buratai, ya yi amfani da gama-garin kalmomi da kowa zai iya fahimta, ba lallai sai soja ba.

Babu ko shakka, duk da cewa marubucin littafin nan soja ne kuma ya rubuta littafin kacokan domin jagora ga ‘yan uwansa sojoji, to amma mutum ko ba soja ba ne, idan ya karanta shi, zai amfana da darussa masu yawa da za su taimaki rayuwarsa, musamman ma batun “Tarbiyyar Kai” domin samun nasara a duk fagen da mutum yake. Haka batun yake wajen koyon gina jiki da ruhi, ta hanyar karatu da atisaye.

Game da marubucin littafin kuwa, Laftanar-Janar Tukur Yusufu Buratai ya fito ne daga garin Buratai na Ƙaramar Hukumar Biu, Jihar Borno, Arewa Maso Gabashin Nigeria. An haife shi a ranar 24 ga Nuwamba, 1960. Ya shiga aikin soja ne a shekarar 1981 kuma ya yi ritaya a 2021. Bayan ya kammala kuma sai aka tura shi aikin jakadanci a Jamhuriyyar Benin, a matsayin Jakadan Najeriya, daga 2021 zuwa 2022.

~~~~~~~
Dokta Bukar Usman marubuci ne kuma tsohon Babban-Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa da ke zaune a Abuja. Ya rubuta wannan Sharhi ne a ranar 03-08-2023.
~~~~~~

Previous Post

BULALAR ZUMUNCI

Next Post

Rage Raɗaɗin Talauci: Attajirai Ku Yi Koyi Da Sabi’u Mahuta

Related Posts

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)
Sharhi

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

July 18, 2025
Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi
Sharhi

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

December 24, 2024
SAI AN YI DA GASKE: Littafin Wasan Kwaikwayo A Mizanin Nazari Da Sharhi
Sharhi

SAI AN YI DA GASKE: Littafin Wasan Kwaikwayo A Mizanin Nazari Da Sharhi

November 16, 2023
Next Post
Rage Raɗaɗin Talauci: Attajirai Ku Yi Koyi Da Sabi’u Mahuta

Rage Raɗaɗin Talauci: Attajirai Ku Yi Koyi Da Sabi'u Mahuta

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

October 17, 2023
Bayan Nasara A Kotun Ƙoli, Shugaba Tinubu Zai Ci Gaba Da Aikin Gina Nagartacciyar Ƙasa – Idris

Bayan Nasara A Kotun Ƙoli, Shugaba Tinubu Zai Ci Gaba Da Aikin Gina Nagartacciyar Ƙasa – Idris

October 28, 2023
THE PUNCH EDITORIAL ON BENUE: A FABRICATION IN SEARCH OF A SCAPEGOAT

THE PUNCH EDITORIAL ON BENUE: A FABRICATION IN SEARCH OF A SCAPEGOAT

June 18, 2025
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (3)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (3)

May 12, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye
  • Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.