NASIHARMU TA YAU (05)

__________
ATTAJIRAI KU YI KOYI DA DR. HARUNA MAIWADA:
Kamar yadda ya saba tallafa wa al’umma, a wannan karon ga abin da ya ce:
“A yunƙurinmu na faɗada ayukan raya jiharmu ta Katsina Zone, wannan karon za mu faɗa Gmgarin Safana, Batsari da Danmusa; inda za mu zaƙulo ɗalibai na waɗannan yankunan da ke karatu a Katsina Polytechnic, FCE Katsina da kuma Jami’ar Umaru Musa ‘Yar-adua, domin ba su tallafi na Scholarship a kan karatun da suke yi.”
__________












