Da Albarkar Littafi Na Je Saudiyya – Sa’adatu Kankia
~~~~~~~
Hajiya Sa’adatu Saminu Kankia tana ɗaya daga cikin fitattun marubutan littattafan Hausa na zamani. Ta wallafa littattafai 48 y

a zuwa yanzu. Wani abin mamaki shi ne, a tattaunawar ta da Babban-Editan Taskar Gizago, Bashir Yahuza Malumfashi, ta ce ta daina rubutu yanzu saboda wani dalili. Ko mene wannan dalilin? Ku biyo mu domin jin ƙwaƙwaf:
~~~~~~~
TG: Kina ɗaya daga cikin manyan marubutan Hausa, ko za ki gaya mana tarihinki a taƙaice?
SA’ADATU: Assalamu alaikum Sunana Sa’adatu Saminu Kankia (Aunty Uwani), kamar yarda aka fi sani. Ni haifaffiyar garin Kankia ce a Jihar Katsina. Ina da shekara 45 yanzu. Da farko na yi karatun firamare a Sada Primary School Kankia, na yi sakandare a Makarantar Musayar Ɗalibai ta Jibia, 1989 zuwa 1995. Bayan nan na yi Diploma a kan Aikin Lafiya Da Tsabtace Muhalli a School of Health Technology, Kankia.
TG: Tun yaushe kika fara rubutu kuma mene ne ya ja ra’ayinki ga harkar rubuce-rubuce?
SA’ADATU: Na fara rubutu tun ina makarantar sakandare aji biyu, inda muka rubuta wani littafi mai suna KOMI NA ALLAH NE, ni da wata ƙawata wadda jika ce ga marigayi Malam Abubukar Imam. To sai dai saboda yanayin yarinta, ba a buga littafin ba, sai dai muka riƙa karantawa tsakanin abokanmu. Da haka har littafin ya shiririce.
Sai bayan mun gama makaranta, shekarar da aka yi mani aure, 1996, saboda yanayin kaɗaici idan maigidana ya tafi wajen aiki, kuma lokacin ban fara karatu ba, sai na ji ina sha’awar in fara rubutu. Don haka idan ya fita, ni kuma sai in ɗauki littafi in ta yin rubutu. Na rubutu littattafai kala biyu. Su ma ɗin ba a buga ba, na ajiye su, na fara karatu.
Sai a shekarar 2002 ce na ɗauko waɗannan littattafan na sake rubuta su. Saboda lokacin na fara aiki, don haka na ci alwashin ko albashina na shekara ɗaya za ya ƙare, sai na buga ko littafi ɗaya ne, in riƙe a hannuna a matsayin ni na rubuta shi. Don haka na sake rubuta na farkon, shi ne IGIYAR ZUMUNCI. Kuma shi ne littafina na farko da na fara rubutawa.
Sha’awa da ra’ayi su ne suka sanya ni son rubutu. Saboda gaskiya ba zan ce ni ma’abociyar karatun litattafai ba ce. Na fi ƙarfi ga maida hankali ga kallon finafinan Indiya.
TG: Ya zuwa yanzu, littattafai nawa kika rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda kuma nawa kika buga a intanet?
SA’ADATU: Aƙalla na rubuta littattafai guda 48 kuma duk an buga su a takarda. Cikinsu guda ɗaya na addini, sai kuma guda ɗaya na koyaon dubarun rayuwa da mu’amala. Babu ko ɗaya cikin littattafaina da na sanya a intanet.
TG: Waɗanne irin matsaloli kike fuskanta a matsayinki na marubuciya, musamman ma a soshalmidiya?
SA’ADATU: Gaskiyar magana babu wata matsala ƙwaƙƙwara da zan ce ta takura ni, ko ta tsaya mani a rai. Saboda idan ka fahimci rayuwa, za ka san cewa ita soshiyalmidiya, waje ne da ya tara mutane masu mabambamtan halaye da ɗabi’a da tunani. Don haka ba zai yiwu ka yi tunanin za ka samu yadda kake so ba, ko kuma ba za a ɓata maka ba. To Amma a tsari na rayuwata, ni ba kowa ko komi ke ɓata mani rai ba. Ina ƙoƙarin ganin na kyautata kalamaina a kan duk wani abu da zan furta, kuma ina kiyaye shiga ko magana wajen da na san za a iya ci mani fuska. Sau tari na sha yin rubutu a kan wani ra’ayi na kaina amma idon na tuna ƙila ba za ya yi wa wani daɗi ba, ko kuma wani za ya iya yin amfani da wannan damar ya ci mani mutunci, sai in janye rubutun, in goge. Don haka zan iya cewa, ba ni da wata gagarumar matsala tsakanina da mutanen da nike hulɗa da su a soshiyalmidiya.
TG: Tun daga fara rubutu, waɗanne irin nasarori kika samu ko kuma akasin su?
SA’ADATU: Alhamdu lillah! Daga lokacin da na fara rubutu, har yau da nike wannan magana, cikin samun nasara nike da sanin alfanun rubutu. Kusan zan iya cewa a rubutu, zai yi wuya a samu wanda ya ci ribar rubutu irin wadda ni Sa’adatu na samu. Littafina na farko, IGIYAR ZUMUNCI, da kuɗin da na samu wajen ƙaddamarwa na je Saudiya na sauke Farali, Hajjita ta farko ke nan. Kuma daga lokacin nike cin arzikin rubutu har yau ɗin nan. Saboda ko yau an sayi littattafaina daga Kwalejin Isa Kaita, ɓangaren masu digiri, reshen ABU Zaria, ɗaliban da ke karantar harshen Hausa. Sun saya ne za su yi nazari a kansu. Don haka Alhamdu lillahi!
TG: A harkar rubuce-rubuce, waɗanne marubuta ne gwanayenki, da kike koyi da rubutunsu?
SA’ADATU:Gaskiya ba zan ce maka ina da wata gwana ba saboda ban cika karatun littattafai ba. Amma dai cikin waɗanda na ɗan bi rubutunsu, ina son salon Bilkisu Salisu Ahmed Funtua (Aunty Bilki).
TG: Marubuta na kuka da kasuwar littafi, ganin an rajja’a ga intanet, shin ke ma wannan abin ya shafe ki? Ko za ki daina fitar da littafi a takarda?
SA’ADATU: Eh to, kusan tun kafin kasuwar littafi ta durƙushe, gaskiya ni dama ina jin na gama rubutu. Don haka ba zan ce ta shafe ni ba, amma dai ina so idan ta yiwu nan gaba in ɗora tsaffin littattafaina a intanet ɗin. Amma ba sabbi ba, ba ni ma iya yin rubutun yanzu.
TG: Wasu marubuta sun koma rubutun fim, ko ke ma kina da shirin haka?
SA’ADATU: Eh, na ma fara, akwai littafina guda biyu da na fara rubuta labarin fim ɗin su, TALAUCI KO SAKACI? da BAƘAR ƘAYA, sai kuma SANADI. Na fara ban ida ba amma su sauran har ɗinke su an yi lafiya lau, wasu matsaloli suka gitta da suka sanya harkar ta fita raina na bar su.
TG: Mene ne babban burinki dangane da rubutu?
SA’ADATU: Duk wani burina a rubutu Alhamdu lillahi, ya cika. Na ba da iya gudunmuwar da nike da hali, kuma littattafaina sun karɓu. Na samu arziki daidai gwargwado, na yi fice, na samu ɗaukaka a harkar rubutu. Don haka Alhamdu lillahi! Na yi iya abin da zan yi, saura kuma an bar wa ‘yan baya Allah Ya dafa masu.
TG: Ko kina da wani kira ga gwamnati da marubuta ‘yan uwanki da kuma al’umma masu karanta littattafanki?
SA’ADATU: Ina yi wa kowa fatan alheri, kuma ina kira ga marubuta masu tasowa, da su yi ƙoƙarin rubuta abin da za ya amfani al’umma, saboda rubutu ba ya tsufa. Duk abin da ka rubuta sai ya yi tasiri a kanka komai daren daɗewa.













