₦8000 Ba Za Ta Sayi Tiyar Masara 10 Ba – Sarkin Samarin Galadima
Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Sarkin Samarin Galadiman Katsina, Abdul’aziz ibni Abdul’aziz ya bayyana cewa akwai abin dubawa da tsarin tallafin da Gwamnatin Tarayya ke shirin aiwatarwa, na bayar da Naira dubu takwas ga alakawan Nigeria miliyan 120 da nufin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da ta yi a watan Mayu da ya gabata.
Tun farko, Taskar Gizago ta tambaye shi abin da zai ce game da cire tallafin fetur da gwamnatin ta yi.
Abdul’aziz ya ce “Cire tallafin mai abu ne mai kyau sai dai gwamnatinmu ta APC ba ta yi shi daidai da lokacin da ya kamata ba. Dalilina kuwa shi ne, ya kamata a ce an fara yin shirin kwantar wa talakawa da hankali kamin cire tallafi, ba wai sai yanzu ba da ‘yan kasuwarmu ke jiran irin wannan damar, domin su muzguna wa talakawa.”
Ya ce dan ka dubi Arewaci, musamman Arewa Maso Gabas da Arewa Maso Yamma, da yawan mutane suna kokawa a kan tsadar rayuwa da cire tallafin mai ya haifar masu a wannan lokacin da rayuwar da ƙyar ake yin ta.
Game da tallafin ₦8000 kuwa, mai sharhin cewa ya yi “Maganar shirin rage talauci da suke faɗi ₦8000, wadda ba ta sayen tiyar masara goma, kuma ta hannu su wa kuɗin za su fito, domin a bayar su isa inda ake so su je?”
Ya ƙara da cewa, “Idan ka kalli shugabaninmu, musamman waɗannan da suka shude da waɗanda suke a kan karagar mulki, wace rawa suka taka ko suke takawa don ganin an samu zuba jari a jihohin Arewacin Nigeria?”
Game da matsalar Arewa, ya ce har kullum yana ganin ita ce ta rashin kamfanoni ko kuma ba a maida hankali ga ‘yan kasuwar waje, su zo Arewacin Nigeria don sarrafa kayansu.
“Idan ka kalli 6arewa a kan maganar waken suya kaɗai da riɗi, daga nan ake ɗauka a kai Lagos a sarrafa su kuma a dawo da mansu mu saya,” inji shi.
Taskar Gizago ta tambaye shi cewa, shi a shawararsa, tun da raba ₦8000 ga talakawa ba zai yi tasiri ba, wane mataki ya kamata a ɗauka na rage kaifin talauci a Nigeria?
“Rashin tasiri ko alfanun wannan abu sh ine, idan ka duba inda matsalar take, ba nan ake maida hankali ba.
Yanzu a Jihar Katsina ko Kano kaɗai, talakawan da suke nan wajen, sun fi talakawan da ke Kudu gaba ɗaya yawa. Amma kuma za ka ga cewa taimakon ya tafi Kudu fiye da Arewacin Nigeria.
“Ni yanzu inda zan bai wa Gwamna Dikko Radda shawara, wallahi sai in ce ya amshe duk wani fili da aka bayar don gina wani kamfani amma abin baiyi tasiri ba. Saboda da yawansu sun amshi filayen nan kyauta a hannun gwamnatin da ta gabata da sunan za su yi kamfanoni kuma sun kewaye da katanga sun manta da su kawai.”













