• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, April 6, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Tsarin Mulki: Jan Hankali Ga Shugabannin Arewa

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 13, 2023
in Gizago
0
Tsarin Mulki: Jan Hankali Ga Shugabannin Arewa

Kabiru Ghali Ibrahim (Abban Saudat)

19
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Kabiru Ghali Ibrahim

Tsarin Mulki: Jan Hankali Ga Shugabannin Arewa

Related posts

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

March 29, 2026

Idan an bai wa yalo ruwa ya sha, to a daure a yayyafa wa yakuwa mana!

Wannan tsokaci da zan yi, ina so in cakuɗa shi da nasihohi da jan hankali, sannan kuma da harbin iska a kan abin da ya shafi wannan yanki namu na Arewacin Najeriya. Wanda wannan yanki yana da wata muhimmiyar rawa da yake da ita a kasancewar ƙasa Najeriya a matsayin ƙasa.

Kai! Zan iya cewa mutuƙar babu wannan yankin namu a lissafin Najeriya, to tabbas babu Najeriya. Domin kuwa tamkar jikin ɗan Adam ne ka cire masa kai zuwa kafaɗa, ragowar jikin daga ƙirji zuwa ƙafafu, tarin ƙashi da tsoka ne kawai amma ba mutum ba.

Bayan wannan gajeriyar shimfiɗa da na yi, zan yi dogon waiwayen baya a kan shugabanninmu da suka gabata, tun ba mu san kanmu ba. Irin su Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa, irin su Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da sauran ire-irensu. Allah Ya ji ƙan su da rahma. Waɗannan mutane, mutane ne da suka kurɓi madarar Turanci daga wajen Bature, tun Turanci yana abin birgewa.

Sannan suka tsaya ka’in da na’in don gina yankin Arewa. Sun san Bature sarai fiye da ‘yan bokonmu na yanzu, sun san dokokinsa da ƙa’idojinsa. Amma duk da haka suke rufe idonsu suka karya dokar Bature don Arewa ta ci gaba.

Misali, mun ji a wasu lokutan in an zo ɗaukar soja ɗan Arewa, aka ce tsawonsa bai kai ba, sai Sardauna ya ce a ƙara masa da nasa. Ko kuma idan ya kai ziyara wata muhimmiyar ma’aikata ta gwamnati, ya iske shugabannin ma’aikatar ba daga wannan yankin namu suke ba, sai ya shugabantar da ɗan Arewa a kansu, koda kuwa mai gadi ne.

A irin waɗannan ayyukan da waɗannan shugabannin namu suka yi ne, da yawa daga cikin ‘yan bokonmu na yanzu suka ci moriyarsa, suke fantamawar su, su da iyalansu.

A kan haka zan bayar da misali a kan wata hira da gidan talabijin na Sunnah TV suka yi da babban malami kuma fitaccen mai wa’azi a wannan ƙasa tamu kuma tsohon Ministan Sadarwa da Fasahar Tattalin Arziki Na Zamani wato Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.

An yi hirar ce a ranar 26/6/2023, wato ƙasa da wata ɗaya da saukar sa daga muƙamin Minista a tsohuwar Gwamnatin Muhammadu Buhari.

Ko shakka babu Farfesa Pantami malamin addini ne na gaban kwatance kuma ba mai kwaɗayin tara abin duniya ba. Na amfana da karatuttukansa da fatawowinsa a muhalli da daman gaske. A hirar, Ministan ya ambata abubuwa masu yawan gaske na gaskiya da jan hankali da faɗakarwa, inda har ya yi wani harbin iska wajen nuni da cewa duk cikin ministocin Buhari, babu wanda ya kai shi fuskantar ƙalubale, kasancewarsa malamin addini.

Wannan maganar tasa tabbas haka take kuma sanannen abu ne ko a tsakaninmu Hausa/Fulani, wani mai riƙo da addini ya samu muƙami a siyasance ko a gwamnatance, zai sha suka da izgilanci, balle a ƙasa gaba ɗaya.
Ba shakka Malam ya yi fama ba ɗan kaɗan ba, Allah Ya saka masa da alheri.

Amma ina da ƙalubale a wata gaɓa da Malam yai magana a kanta, inda yake cewa lokacin yana kan kujerar Minista, ya ga ɓarna Kalakala amma a ƙa’ida ba shi da ikon kora ko dakatarwa ko ɗaukar ma’aikaci a ma’aikatar, domin wannan ba aikinsa ba ne, kamar yanda doka ta tanadar; tun da shi ba ma’aikacin gwamnati ba ne, naɗin siyasa aka yi masa, sai dai ko ya gaya wa Babban Sakatare ko Shugaban Ma’aikata, domin su tsawatar ko Kuma in abin ya shafi badaƙalar kuɗi ya shaida wa EFCC Ko DSS da sauransu, su ɗauki mataki. Ya ƙara da cewa shi mai bin doka ne, ba ya son a ga mutum kamarsa ya taka doka.

A irin haka sai na fahimci maganar Malam a kan cewa ko sababbin ma’aikata ma bai ɗauka ba tun da ba shi da iko, in dai a kan dokar da ya tarar a kanta ya tafi.

In dai ko abin da Malam ya faɗa, a kansa ya tafi, to a gaskiya Malam ya tafka kuskure. Dalilina a nan shi ne, shin Malam ya fi shugabannin baya da na bayar da misali a kansu, irin su Sa Ahmadu Bello sanin doka da bin ƙa’idar Bature? Na tabbatar ko Malam da kansa zai ce a’a bai fi su ba. To in haka ne su garin yaya suka rufe idonsu, suka yi fatali da dokar don su kare ‘yancin mutanensu, su gina su? Wanda wannan ginin da aka yi musu da yawan ‘yan Arewa suke cin gajiyarsa a yau, cikinsu har da shi Malam?

Sannan abokan aikin Malam wato sauran ministocin ba haka suka yi ba, sun rufe idonsu sun yi watsi da dokar, sun zuba mutanensu, mabiya addinai daban-daban, sun zuba mutanen addininsu, ɗan iska ko shaiɗani ya zuba mutanensa, yayin da malamin addini ya ɓige da bin doka. Doka kuma ta hana shi ya kai mutanen arziki masu tsoron Allah irinsa, daga nan sai a wayi gari ma’aikatun Gwamnatin Tarayya sun cika da ashararan mutane marasa tarbiyya, domin burin iyayen gidansu ke nan.

Allah Ya gafarta Malam, ba ku kuke gaya mana cewa addinin Musulunci ya yarda da lalura ba, inda lalurar ta halatta cin mushe da jini da sauransu? In dai wannan ce lalurar, to kai bayin Allah nagartattu turbar aikin al’umma tamkar lalura yake in ma bai zama wajibi ba.

Allah Ya gafarta Malam, ina kira da a yi wa wannan gajerun hujjojin nawa duban tsanaki kuma a yi gyara a kansu in Allah Ya ƙara ba da wata damar.

Abu na ƙarshe da zan tuke bayanina da shi, zuwa ga zaɓaɓɓun gwamnoni ne da Shugaban Ƙasa. Ku kiyayi naɗa ‘yan boko muƙaman Kwamishinoni da Ministoci, domin a ɗabi’arsu, ba sa amfanar da al’umma kamar ‘yan siyasa. Su burinsu su tara abin duniya, su yi facaka daga ba gidansu ba sai gidan ‘ya’yansu, idan zaɓe ya zo su yi biris ko kaci ko ka faɗi. Amma ‘yan siyasa su suke da dabarun jan jama’a a jiki, su za su tara maka mutane a zaɓe na gaba.
~~~~~~~
Kabiru Ghali Ibrahim
(Abban Saudat), Ma’ajin Ƙungiyar Gizago Ta Najeriya, ya aiko sharhinsa daga Kano (11/7/2023).
~~~~~~~

Previous Post

Na Wallafa Littattafai 89 A Shekara 25 – Sadiya Yakasai

Next Post

Gizagawa Sun Yi Rashi A Katsina

Related Posts

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso
Gizago

Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

March 29, 2026
Shin An Sallami Malam El-Rufa’i Ke Nan Ko Zai Dawo Shari’a?
Gizago

Shin An Sallami Malam El-Rufa’i Ke Nan Ko Zai Dawo Shari’a?

March 28, 2026
Next Post
Gizagawa Sun Yi Rashi A Katsina

Gizagawa Sun Yi Rashi A Katsina

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

TAURARON GIZAGAWA: ABDULHADI DABO

TAURARON GIZAGAWA: ABDULHADI DABO

July 20, 2023
SASSANYAN AMINCI (7)

SASSANYAN AMINCI (7)

September 18, 2025
₦16,000 Za Mu Sayar Da Taki A Jigawa – Gwamna Namadi

Batun Tsaro A Malam Madori: Jan Hankali Ga Hukumomi Da Al’umma

September 17, 2023
RAMADAN KARIM: 03-1447

RAMADAN KARIM: 03-1447

February 20, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)
  • JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles

Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles

April 5, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)

April 4, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.