Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-01)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Sunan Fim: Gidan Badamasi (08-01)
Marubucin Labari: Falalu A. Ɗorayi
Tsara Labari: Nazir Adam Salih
Mai Shiryawa: Falalu A. Ɗorayi da Nazir Adam Salih
Tagwan Mai Shiryawa: Nasiru NID
Umurni: Falalu A. Ɗorayi, Ahmad A. Ɗorayi da Sunusi Ɗanyaro
Kanfanin Shiryawa: Ɗorayi Films, Kano, Nigeria
Shekarar Shiryawa: Nuwamba 2026
‘Yan Wasa: Magaji Mijinyawa, Nura Muhammad Ɗandolo, Hussaini Sule Ƙoƙi, Sani Ɗangwari, Falalu A. Ɗorayi, Haruna Baban Chinedu, Umma Shehu, Hadiza Kabara, Aminu Mirror, Hauwa Ayawa, Amira Shu’aib, Hajiya Jummai da Sauransu
__________
Gidan Badamasi, fim ne mai dogon zango, wanda aka gina bisa tubalin barkwanci, wanda kuma ya tattara zaƙaƙuran ‘yan wasan kwaikwayo na dauri da kuma ‘yan-bana-bakwai. Haka kuma, ya dace da ƙwararrun marubuta, masu shiryawa da kuma masu ba da umurni.
Fim ɗin, wanda ake wa laƙabi da “Bindigar Harbe Baƙin Ciki, wanda yake cike da cakwakiya, badaƙala da harigido… a ranar Asabar da ta gabata, 7 ga Nuwamba aka fara haska Zango na 8, Kashi na 1.
A wannan zango, an buɗe da labarin ɓata ko sace ɗan lele, ɗan autan hamshaƙin attajiri, Alhaji Badamasi (Magaji Mijinyawa), wato Badamasi Jiniya (Ibrahim Ɗalhatu Usman). Al’amarin da za a kira da ta faru kuma ta ƙare, wai an yi wa mai dami ɗaya sata. Dalili kuwa shi ne, Alhaji Badamasi ya shirya tsaf, shi da amaryarsa ‘yar lele, Junaidiyya (Amira Shu’aib) za su tafi ƙasar Moroko. Amma ina, sai aka yanka kuma ta tashi, domin kuwa an sace ɗan amarya, Badamasi Jiniya.
Wannan shi ne ƙullin zaren labarin fim ɗin kuma shi ne aka fara warwara, a wannan fitowa ta ɗaya. Zargi mai ƙarfi ya rataya a wuyan kangararru kuma karkatattun ‘ya’yan Alhaji Badamasi, mazansu da matansu. Domin gano wane ne ko kuma wace ce daga cikinsu suka ƙunduma wannan aika-aika, an miƙa lamarin ga ‘yan sanda, waɗanda cikin lokaci suka shiga aikinsu na bincike.
‘Ya’yan Alhaji Badamasi da suke kusa, Ayuba Ɗanƙwambo (Nura Muhammad Ɗandolo) da Indiye (Sani Ɗangwari) da Malam Zaidu (Aminu Mirror) da Hadimin Badamasi, Taska (Falalu A. Ɗorayi) da Hauwa (Hadiza Kabara) da Azima (Hauwa Ayawa), duk saita suka halarci binciken ‘yan sanda. Haka kuma, sauran da suke nesa, Haruna Bazuka da Zillaziyya (Umma Shehu), an ayyana sunayensu cikin waɗanda ake nema.
Irin yadda zaratan ‘yan wasan nan suka tafiyar da labarin fim ɗin, ya samar da abin da ake buƙata, daidai da babban jigon fim ɗin – barkwanci da nishaɗantarwa. Haka kuma, cike yake da darussa masu yawa.
Darasi na farko da za a iya tsinta a fim ɗin shi ne, faɗakarwa game da mummunan abin da ke faruwa a alummarmu a yau – satar mutane da garkuwa da su, domin neman kuɗin fansa. Don haka wannan gargaɗi ne ga al’umma, musamman iyayen yara, da su kula da ‘ya’yansu, domin kauce wa abin da ya faru ga Badamasi Jiniya.
Darasi na biyu, an faɗakar da al’umma dangane da aikin ‘yan sanda da kuma al’amuran da suka shafi doka, cewa idan wani lamari ya faru a cikin al’umma, jami’an tsaro suna da ikon yin binciken duk wanda ake zargi, domin gano gaskiya, ba tare da la’akari da kusanci ko nasabar wanda ake zargi ba. Misalin dai yadda aka tarkata ‘ya’yan Alhaji Badamasi, aka kai su wajen ‘yan sanda.
Darasi na uku kuma shi ne, faɗakarwa ga al’umma da ma jami’an tsaro, domin su gane cewa ba daidai ba ne a ci zarafin wanda ake zargi ko tuhuma da aikata wani laifi, ta hanyar duka ko zagi da sauransu.
An fayyace wannan ta yadda aka nuno jami’an ‘yan sanda suna jibgar su Ɗankwambo da Taska da Indiye da ƙatuwar gora, kamar suna kirɓin sakwara. DPO ya fayyace wa jami’ansa cewa ba daidai ba ne a doki wanda ake zargi, kamar yadda ya faɗa wa Alhaji Badamasi cewa ba a yin bincike da duka ko tursasawa, sai cikin hikima da dubarar aiki.
Haka kuma DPO ya nuna yadda ake mu’amalantar wanda ake zargi da aikata laifi, cewa yana da wasu ‘yanci da haƙƙoƙi, a matsayinsa na ɗan Adam, kamar dai yadda ya ba Ɗankwambo damar ya yi waya da likitansa.
Darasi na huɗu, an nuna illar rashin zumunci da zaman lafiya a zamantakewa. Dubi dai yadda Junaidiyya ta yi ta tuhuma ga kishiyarta da Azima da sauran ‘ya’yan Alhaji Badamasi. Wannan yana nuna cewa akwai buƙatar a yi zaman lafiya tsakanin kishiya da kishiya da sauran abokan zama.
Darasi na biyar, an tunasar da al’umma illar bibiyar bokaye da malaman tsibbu da ‘yan bori, cewa duk maƙaryata ne. Hakan ya bayyana ne a lokacin da Alhaji Badamasi ya ɗauko malamin tsibbu da ‘yan bori, da nufin su gano masa wanda ya sace masa ɗa. Daga ƙarshe dai suka yi ta wasa da hankalinsa kuma babu biyan buƙata.
Darasi na shida, an nuna wa al’umma, musamman attajirai da su riƙa kyautata wa hadimansu. Hakan ya bayyana ne yadda Alhaji Badamasi ya gano cewa hadiminsa Taska yana da matuƙar amfani a zamansu na sama da shekara 40, inda cikin kwana uku kaɗai da ya rasa shi, ya shiga damuwa.
Darasi na bakwai, an nuna muhimmanci da tausayi da jin ƙai da ke tsakanin uwa da ɗanta. Dubi dai yadda aka nuno Junaidiyya ta zautu saboda ɓacewar ɗanta, Badamasi Jiniya.
Wani abin lura kuma shi ne, bayyanar Malam Haruna Baban Chinedu (Obinna) a wannan Zango na 8, duk da cewa ya bayyana sanarwar daina fim kuma kowa ya shaida cewa yanzu babban malami ne shi, mai aikin Da’awar Musulunci tare da abokinsa Sheikh Adam Ashaka.
To, babu mamaki, domin kuwa na taɓa ganin sanarwa daga shi Baban Chinedu, inda ya bayyana cewa ya daina harkar fim da waƙa. Sai dai ya yi togacciyar cewa, zai kammala duk wani fim da ya shiga kwantaragi, kafin ɗaukar wannan mataki. Ke nan, Gidan Badamasi na ɗaya daga cikin waɗannan finafinai nasa da suka rage.
Babu shakka su Falalu A. Dorayi da Nasiru NID da Nazir Adam Salih da sauran jami’ai, sun baje hajar fasaha da barkwanci a Gidan Badamasi. Amma duk da haka, akwai buƙatar su ƙara wa fim ɗin nan tagomashi. Abin nufi shi ne, su samar da fassarar Turanci (subtitles), domin kuwa hakan zai ƙara wa fim ɗin armashi ga masu kallo na faɗin duniya, musamman waɗanda ba su fahimtar Hausa.
Idan Allah ya kai mu Asabar lafiya, za mu ga ci gaban wannan fim na Gidan Badamasi, Zango na 8, kashi na 2.
TAURARO:
A matsayina na mai sharhi da nazari, na ba fim ɗin nan TAURARI UKU DA RABI (3.5/5 Stars). Gare ku masu kallo, taurari nawa za ku ba fim ɗin Gidan Badamasi?
__________












