Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-02)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Sunan Fim:
Gidan Badamasi (08-02)
Marubucin Labari:
Falalu A. Ɗorayi
Tsara Labari:
Nazir Adam Salih
Mai Shiryawa:
Falalu A. Ɗorayi da Nazir Adam Salih
Tagwan Mai Shiryawa:
Nasiru NID
Umurni:
Falalu A. Ɗorayi, Ahmad A. Ɗorayi da Sunusi Ɗanyaro
Kanfanin Shiryawa:
Ɗorayi Films, Kano, Nigeria
Shekarar Shiryawa:
Nuwamba 2026
‘Yan Wasa:
Magaji Mijinyawa, Nura Muhammad Ɗandolo, Hussaini Sule Ƙoƙi, Sani Ɗangwari, Falalu A. Ɗorayi, Haruna Baban Chinedu, Abba S. Boy, Rabi’u Ibrahim Daushe, Sulaiman Yahaya Ɓosho, Umma Shehu, Hadiza Kabara, Aminu Mirror, Hauwa Ayawa, Amira Shu’aib, Hajiya Jummai da Sauransu
__________
A ranar Asabar da ta gabata (14-11-2026), aka haska fim ɗin Gidan Badamasi, Zango Na 8, Kashi Na 2. Kuma daga dukkan alamu, mashirya fim ɗin sun yi dukkan abin da ya dace, domin ɗorawa daga kashi na 1 da ya gabata a makon jiya, dangane da inganci, ilimantarwa, faɗakarwa da nishaɗantarwa da ga al’umma.
A wannan fitowa, bayan an kusa fita daga badaƙalar sacewa da bayyanar Badamasi Jiniya, sai kuma aka sake buɗo wata sabuwa – batun sace zunzurutun kuɗi, har Naira miliyan 250. Wannan kuɗi, su ne adadin kuɗin fansa da suka kamata a ce an biya masu garkuwa da mutane da suka kama Alhaji Badamasi da Baba Daure da Taska, a kwanakin baya.
Bayan batun sace waɗannan maƙudan kuɗi, sai kuma ga batun saka na’urar naɗar hotuna da bayanai (CCTV) a cikin gidan Alhaji Badamasi. An nuno ɗaukacin iyalan attajirin a babban falonsa, inda yake bayyana masu labarin saka wannan na’ura, wacce ya ce an kafa ta a kowane lungu da saƙo na gidan, illa ɗakunan ba-haya.
Har’ila yau, akwai batun bijiro da malaman tsibbu da bokaye da ‘yan bori domin, fallasa maha’inta a gidan Alhaji Badamasi (Magaji Mijinyawa), kamar yadda shi kansa mai gidan ya faɗa da kuma ƙorafin Taska (Falalu A. Ɗorayi), a tattaunawarsu da Sadanu (Abba S. Boy).
Waɗannan saɓatta-juyatta a gidan Alhaji Badamasi, su ke ƙara tabbatar da cewa, jami’an tsaro za su ci gaba da taka muhimmiyar rawa a wannan fim. Shin su wane ne ake zargi da sace dukiyar Alhaji Badamasi, Naira miliyan 250? Babu wai kuma babu inke, ‘ya’yansa ne, waɗanda suka yi ƙaurin suna a fagen rashin gaskiya. Kuma tuni har jami’an tsaro sun shiga aiki.
Wasu Darussa A Fim Ɗin:
Darasi na farko shi ne, muhimmancin ɗaukar matakan tsaro na zamani a muhallai da ma’aikatu da wuraren sana’a da sauransu. Hakan ya bayyana a yadda Alhaji Badamasi ya saka na’urar naɗar bayanai ta zamani (CCTV) a gidansa.
Darasi na biyu shi ne, illar yaɗa hotuna da bidiyo a soshalmidiya. Wannan ya bayyana daga tattaunawar Alhaji Badamasi da surukinsa Adnan (Rabi’u Ibrahim Daushe).
Darasi na uku da za mu iya samu a wannan kashi na biyu, a Gidan Badamasi, shi ne muhimmancin saka hikima da azanci da siyasa wajen mu’amala da tafiyar da iyali. Hakan ya bayyana a tattaunawar Alhaji Badamasi da ɗiyarsa Azima (Hauwa Ayawa), inda yake lallashin ta, har yake cewa da yawa daga abubuwan da yake nuna wa amaryarsa Junaidiyya (Amira Shu’aib) da ɗanta na kyautatawa, duk wasan kwaikwayo yake yi, domin a samu zaman lafiya a gidansa.
Darasi na huɗu shi ne, faɗakar da al’umma dangane da yawaitar rashin gaskiya da aikata laifuka a cikin al’umma, musamman ma yadda cin hanci da rashawa suka yi katutu a cikin al’umma. Hakan kuma ke nuna yadda al’umma ta gurɓace. Hakan ke nuni da cewa, bai kamata a amince wa mutum ba kai tsaye. Wannan ya bayyana a kalamai da ayyukan Sadanu da Taska da Ɗanƙwambo (Nura Muhammad Ɗandolo) da Madaki (Sulaiman Yahaya Ɓosho). Dubi kuma yadda jami’in tsaro na farin kaya, Ali Boy yake amsar rashawa daga hannun Alhaji Badamasi da kuma yadda yake amfani da kuɗi wajen samun bayanai daga wurin Taska.
Darasi na biyar shi ne, faɗakar da jami’an tsaro wajen amfani da hikima wajen samun bayanai. Dubi dai yadda Ali Boy yake gudanar da aikinsa na bincike. Shi ne ya bayyana wa Alhaji Badamasi cewa, domin gano waɗanda suka sace masa kuɗi, bincike zai faɗa kan kowa, ba taƙaitawa kan mutum uku kawai ba.
Baya ga waɗannan muhimman darussa, masu kallo sun samu nishaɗi cikin natsuwa ba tare da harigido ba. Mu duba hirar Adnanu da Alhaji Badamasi, hirar Adnanu da Madaki, hirar Taska da Ɗankwambo da kuma hirar Taska da Sadanu.
Masu shirya Gidan Badamasi sun yi ƙoƙari matuƙa wajen ƙulli da warwarar jigon fim ɗin, ta yadda suke iya riƙa mai kallo daga wannan fitowa zuwa ta gaba.
Idan Allah ya kai mu Asabar mai zuwa, za mu kalli kashi na uku na wannan fim, domin ganin yadda za ta kaya, wajen binciko waɗanda suka sace kuɗin Alhaji Badamasi, Naira miliyan 250.
TAURARO:
A matsayina na mai sharhi da nazari, na ba fim ɗin nan TAURARI HUƊU BISA BIYAR (4/5 Stars). Gare ku masu kallo, taurari nawa za ku ba fim ɗin Gidan Badamasi Zango Na 8, Kashi Na 2?
__________













