Tiƙar Rawa A Yayin Kamfen: Isar Da Saƙo Ne Ko Rashin Kunya?
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

_________
Kakar yaƙin neman zaɓe ta kama a Najeriya, inda ‘yan takara suke ta yawo lungu da saƙo suna baje hajar jam’iyyu da ‘yan takararsu.
Sai dai kuma a kan haka, ‘yan siyasa da magoya bayansu sun fara sukar juna, musamman dangane da salon yaƙin neman zaɓen juna, dangane da abin da ya shafi rawa, kiɗa da waƙa a yayin gudanar da yaƙin neman zaɓen.
Babban lauya Abba Hikima kuma mai goyon bayan ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya kushe salon yaƙin neman zaɓen Jam’iyyar APC, musamman yadda ya ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shattima da Sanata Adam Ashiomhole suna tiƙar rawa a gaban ɗimbin magoya bayansu.
Ga abin da Barista Hikima ya ce: “Wallahi Atiku Abubakar ne kawai maganin mutanen nan. Ba su da daraja. Ba su da imani. Ba su da kunya. Sun hana jam’iyyu rijista. Sun kunna wa waɗanda suka rage wuta. Sun lalata kotuna. Dama Majalisar Tarayya ta zama ‘yar amshin Shata. So suke yi su yi ta dukan mutane suna hana su kuka. A ce a ƙasa mai mutane sama da miliyan 220, jam’iyya mai mulki ce kawai ke rawar gaban hantsi, bayan sun musguna wa jama’a?”
A kan haka, ita kuma Hadima ta Musamman ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Rahma Abdulmajid, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, ta mayar da martani ga Barista, inda ta bayyana cewa:
“Barista Abba Hikima, posting ɗinka fa a kan rawar Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, kamar zai fi cutar da ɗan takararka, don shi fa mutum ne mai son rawa idan ya je Kudu, yanzu kuma duk ka janyo mun sa masa ido; ba dama ya yi rawa sai mun yi magana. Ga shi kuma kamfe a Kudu dole sai an taka.
“Wato wani abu da na san ka sani tun duniya na bacci shi ne Najeriya, Arewa da Kudu ce, masu al’adu daban-daban. Duk mai son ya jagorance ta, ko Waziri ne shi ko Jagaba, dole sai ya nuna wa al’ummar Kudu da Arewa cewa zai rungumi al’adu da fahimtarsu, ba kawai ya zama kallon yanki ɗaya yake wa komai ba.”
To, wai ba wannan ba ma, idan muka duba tarihin siyasa a ‘yan shekarun nan daga 1999 zuwa yau, wane ɗan siyasa ne bai yi rawa a gaban jama’a ba? Kamar yadda Taskar Gizago ta kalato, ta samo hotunan Janar Olusegun Obasanjo yana rawa. Ga hoton Goodluck Jonathan da Mataimakinsa, Namadi Sambo suna rawa.
Haka kuma, marigayi Janar Muhammadu Buhari ya taɓa yin rawa a gaban jama’a, a yayin yaƙin neman zaɓe a Kudu. Hatta Gwamnoni masu kamun kai, irin Malam Ibrahim Shekarau, sun taɓa taka rawa a wajen yaƙin neman zaɓe, wanda haka ya sa har mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya yi masa zambo, a waƙarsa ta “Zuwan Mai Malfa Kano.”
Manyan ‘yan siyasa, irin su Atiku Abubakar, Bola Ahmed Tinubu, Rabi’u Musa Kwankwaso da Peter Obi, duk suna yin rawa a gaban ɗimbin jama’a, a yayin yaƙin neman zaɓe.
Abin tambaya a nan shi ne, shin wai rawa da kiɗa da waƙa ga ‘yan siyasa, a gaban jama’a, hanya ce ta isar da saƙo ga magoya baya ko kuwa rashin kunya ce da zubar da mutunci?
__________













