Gabatar Da Shehu Jahan Zamani (1)

__________
Wane Ne Shehu Jaha?
Shehu Jaha, kamar yadda bincike ya tabbatar, suna ne da ake alaƙantawa da ƙirƙirarrun labarun barkwanci irin na dauri, musamman a ƙasar Hausa.
Ba kamar yadda wasu ke hasashe ba, shi ba wani shahararren sarki ko malami ba ne, wanda aka taskance cikakken tarihin rayuwarsa a rubuce ba ne. Abin da bincike ya nuna shi ne, Shehu Jaha ko Juha, wata shahararriyar figar barkwanci da hikaya ce, wadda ta shahara sosai a al’adun Hausa.
Shehu Jaha yana cikin fitattun jaruman labarun barkwanci, hikima da wayewa na Hausa. Labarunsa suna gabatar da shi a matsayin mutum na daban ta fuskar rayuwa, wanda yake da wata fahimta ta daban game da al’amura.
Wani lokaci za a same shi yana nuna wauta a zahiri amma tare da wata hikima a ɓoye. Wani lokaci kuma sai ya juya magana ta yadda mai sauraro zai yi dariya amma ya ɗauki darasi.
Abin lura shi ne, ba a da tabbataccen tarihin mutum ɗaya mai suna Shehu Jaha, wanda za a iya cewa shi ne ainihin wannan jarumin. Wasu bincike kan al’adun labaran Jaha sun nuna cewa, asalin wannan jarumin ya samo tushe ne daga tsohuwar al’adar labaran Juha a duniyar Larabawa da sauran sassan Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.
Wani binciken ilimin harshe ya bayyana cewa an shigar da irin waɗannan labaran cikin Hausa, daga baya suka zama sanannu sosai a tsakanin Hausawa.
(Za mu ci gaba)
__________













