NASIHARMU TA YAU (62)
Kada Ka Raina Mataki Ko Matsayinka A Rayuwa
__________
Matashi Ishaq Sama’ila, ɗaya ne daga cikin hadiman Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Ta Fuskar Siyasa, Elder Alhaji Ibrahim Kabir Masari. Ya yi tsokaci ga al’umma, musamman matasa, game da rayuwa. Ga abin da yake cewa;
“Kada ka raina ƙaramin matakin da ka taka a yau. Domin babbar nasara ba ta samuwa a rana ɗaya. Tana farawa ne da ƙaramin ƙoƙari, jajircewa da dagewa. Kada ka damu da matakin da kake tafiya. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, kada ka tsaya. Ka ci gaba da ƙoƙari, domin nasara tana jiran masu haƙuri da juriya.”
___________











