NASIHARMU TA YAU (06)

__________
SHUGABANNIN KANO KU YI SULHU
Wannan kira ne na musamman ga shugabannin al’umma a Jihar Kano – Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sarki Muhammadu Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero. Don Allah ku zauna ku kawo maslaha da sulhu game da lamarin SARAUTA a Kano. Ku haƙura ku samar da aminci da zaman lafiya a tsakaninku, domin ku zauna lafiya kuma al’umma ta zauna lafiya. Rashin SULHU tsakaninku rugujewar al’umma ne. Babu shakka sulhu alheri ne, rashin sa kuwa sharri ne!
__________












