ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Shahararren mawaƙin nan na Hausa kuma na zamani, wanda ya yi fice wajen waƙoƙin mata a gidan biki, Ado Gwanja ya samu lafiya.
Mawaƙin ya fito ƙarara a karon farko, ya yi bayani game da rashin lafiyar da ya yi fama da ita. Gwanja ya bayyana cewa ya samu sauƙi kuma an sallamo shi daga asibiti.
Ga abin da yake cewa a shafinsa na Facebook:
Assalamu Alaikum warahmatullah.
Ina son in yi wannan bayani domin kwantar da hankalin masoyana da kuma gyara wasu labaran da ake yaɗawa ba tare da tabbatacciyar hujja ba.
Alhamdulillah, sama da watanni biyu ke nan da muka baro asibiti. Gaskiya ne na yi rashin lafiya kuma hakan ba abin kunya ba ne. Cuta daga Allah take, kuma shi ne mafi cancanta a sanar da komai, domin tun farko shi ya sani, shi ya jarabce ni da ita kuma Alhamdulillah, shi ne ya yaye min ita.
Abin da yake ba ni mamaki shi ne, yadda wasu ke ta yaɗa labarai da cewa har yanzu ina cikin wani hali, alhali kuwa babu wanda ya taɓa ganin hotona ko bidiyona a lokacin da nake jinya. Ko a lokacin da nake asibiti, ban bari a ɗauke ni hoto ko bidiyo ba. Hatta ni kaina ban ɗauki hoto ko bidiyo da wayata ba. Saboda haka duk wanda yake cewa ya gan ni a asibiti ko yana da wani sahihin bayani daga lokacin jinyata, ya san abin da yake faɗa.
Alhamdulillah, na yi rashin lafiya kuma na warke. Amma ba dole ba ne in fito in bayyana irin cutar da na yi ga mutane. Tund a Allah ne ya ɗora min ita, shi ne mafi cancanta da ya san sirrinta. Da zafin cuta da sauƙinta duk daga Allah suke kuma shi kaɗai ne mai ikon jarabtar bayinsa da abin da ya ga dama.
Kwanaki uku da suka gabata, na saki sabuwar waƙata ta siyasa mai suna “Tabare,” wadda manufarta ita ce wayar da kan al’umma da jawo hankalinmu kan muhimman abubuwan da suka shafe mu. Wannan shi ne abin da nake yi yanzu kuma ina ci gaba da aikina cikin ƙoshin lafiya.
Ina kuma jan hankalin gidajen jaridu da masu wallafa labarai da su riƙa tabbatar da sahihancin labari kafin su yaɗa shi.
Ga masoyana kuma, ina roƙon ku da ku kwantar da hankalinku. Wannan jarabawa ce daga Allah kuma Allah yana jarabtar bayinsa. Idan har annabawa sun fuskanci jarabawa, to wane ne ni da ba zan fuskanci tawa ba? Alhamdulillah, Allah ya ba ni ikon cin wannan jarabawa kuma ina ci gaba da gode masa a kowane hali.
A ƙarshe, duk abin da yake faruwa a rayuwa yana daga wani ɓangare na ɗaukaka. Domin idan ba a san mutum ba, ba a cika magana a kansa ba. Ina gode wa Allah a kowane hali.
Na gode da addu’o’inku, ƙaunarku da goyon bayanku.
Alhamdulillah! ina lafiya!
__________













