SHANSHANI mai ƙafar yawo ya leƙa gidan marubuci, ɗan siyasa kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Reno Omokri, inda ya jiwo shi yana bayyana cewa mutanen Kudancin Najeriya, musamman na yankin Kudu Maso Gabas da Kudu Maso Kudu ba su san komai ba sai sharholiya da bushasha, a yayin da takwarorinsu na Arewa da na Kudu Maso Yamma suka ƙware wajen sarrafa dukiya domin amfanin al’ummarsu.
Da yake doka misali, Reno ya ce a kwanakin baya wani hamshaƙin ɗan kasuwa daga Kudancin Najeriya ya riƙa bugun gaba da alfaharin cewa ya gina katafariyar matatar sarrafa giya a Najeriya.
“To, ina amfanin giya? Najeriya matatar sarrafa mai take buƙata ba ta giya ba. Haka fa abin yake kasancewa. A yayin da attajiran ‘yan kasuwa daga Kudu ke rige-rigen gina matatun sarrafa barasa, shi kuwa attajiri daga Arewa, Aliko Ɗangote sai ya gina katafariyar matatar man fetur da ta fi kowace girma a duniya, a kan Dala biliyan 19.” In ji Reno.
Ya gargaɗi ‘yan Kudu da cewa ba su da bakin da za su zargi Ɗangote da laifin babbake harkar kasuwanci. “Shin akwai wanda ya ɗaure hannuwan attajiranmu, ya hana su zuba jari domin gina matatun mai a ƙasar nan?” Ya ƙalubalance su.
Marubucin, wanda ya yi ƙaurin suna wajen tsokano magana, ya ƙara da cewa nan gaba kaɗan Abdulsamad Rabi’u shi ma zai gina tasa matatar a kan Dala biliyan 9.
“Mutanen Kudu su daina kukan cewa ‘yan Arewa sun danne su. Muna da dukiya amma me muke yi da ita idan ba sharholiya da bushasha ba? Za ka ga muna kashe miliyoyin kuɗi wajen bikin binne mamatanmu amma su mutanen Arewa da farin ƙyalle suke binne mamatansu.”
NI kuwa SHANSHANI, ina cewa: Ga dukkan alamu, akwai ƙanshin gaskiya a batun Omokri. Ko kuwa yaya kuka gani?













