• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Wednesday, October 7, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

DIKKON KATSINAWA

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
September 6, 2026
in Labarai
0
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

Gwamna Dikko Umaru Radda tare da shugabannin da suka halarci taron

11
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

Daga Wakilinmu

Related posts

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

September 26, 2026
Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Dikkon Katsinawa (14)


__________
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya buƙaci mata da matasa su dage wajen koyon sana’o’i, bunƙasa ƙwarewarsu da kuma samar da kasuwannin da za su ba su damar dogaro da kansu.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Asabar, yayin taron Shugabannin Masana’antu Da Baje Kolin Harkokinsu (CEOs Round Table Summit and Exhibition) karo na huɗu da aka gudanar a ɗakin taro na Hillside a garin Katsina, inda ya jaddada cewa bunƙasa sana’o’i da kasuwanci na da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma inganta tsaro.

Ya ce samun kuɗi kaɗai bai wadatar wajen samun nasarar kasuwanci ba, domin ana buƙatar ƙwarewa, kasuwa da jari domin gina sana’o’i masu ɗorewa. Ya kuma ƙarfafa matasa da su rungumi sana’o’in hannu da na gargajiya, tare da sabunta su ta hanyar amfani da fasaha da inganta kasuwancinsu.

A nata bangaren, mai shirya taron, Lubabatu Umar Ahmed, ta yaba wa Gwamnatin Gwamna Radda bisa tallafin da take bai wa ƙananan da matsakaitan ‘yan kasuwa, inda ta ce shirye-shiryen gwamnati sun taimaka wajen ƙarfafa rayuwar mutane 17,400 a jihar Katsina.

Da take wakiltar Uwargidan Gwamna, Hajiya Zulaihat Dikko Radda, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan harkokin Banki da Kuɗi, Bilkisu Suleiman Ibrahim, ta ƙarfafa matasa da su rungumi fasaha, neman shawarwari daga ƙwararru da kuma amfani da damar samun tallafin gwamnati.

Shi kuwa Kwamishinan Noma, Hon. Aliyu Lawal Zakari Shargalle, ya bayyana cewa sama da matasa 800 sun amfana da shirin Songhai, inda ake ba su horo da tallafin fara sana’a bayan kammala karatu. Ya kuma ce wasu matasa kusan 700 na samun horo kan sana’o’i daban-daban tare da kayan aiki da tallafin kuɗi a wannan cibiyar, inda ya buƙaci ƙulla alaƙa da ma’aikatar gona domin tallafawa mata.

A nata bangaren, Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Aisha Aminu Abdullahi Malumfashi, ta ce gwamnati na ƙara faɗaɗa shirye-shiryen tallafa wa mata irin shirin “Nigeria for Women Project,” inda sama da mata 4,000 za su baje kolin sana’o’insu, yayin da 2,200 za su samu tallafin kuɗi.

Taron ya haɗa jami’an gwamnati, ‘yan kasuwa, masu ƙirƙire-ƙirƙire da matasa domin musayar dabaru da neman hanyoyin bunƙasa sana’o’i da kasuwanci masu ɗorewa a jihar Katsina.
__________

Previous Post

Ayyukan Alheri Daga Gidan Amana

Next Post

Malumfashi: Mun Yi Babban Rashin Uba

Related Posts

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro
Labarai

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

September 26, 2026
Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin
Labarai

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)
Labarai

Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)

August 31, 2026
Next Post
Malumfashi: Mun Yi Babban Rashin Uba

Malumfashi: Mun Yi Babban Rashin Uba

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

BIU: A Visit to a City on a Plateau (2)

BIU: A Visit to a City on a Plateau (2)

December 13, 2023
Gwamnatin Tinubu: Tallafin ₦8000 Ba Zai Yi Tasiri Ba!

Gwamnatin Tinubu: Tallafin ₦8000 Ba Zai Yi Tasiri Ba!

July 16, 2023
Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madallah

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madallah

August 11, 2023
BAKIN JAƁA (7)

BAKIN JAƁA (7)

October 15, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Nasiharmu Ta Yau (13)
  • NASIHARMU TA YAU (12)
  • Nasiharmu Ta Yau (11)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Nasiharmu Ta Yau (13)

Nasiharmu Ta Yau (13)

October 6, 2026
NASIHARMU TA YAU (12)

NASIHARMU TA YAU (12)

October 5, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.