• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, July 10, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Siyasa

Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

SIYASA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 8, 2026
in Siyasa
0
Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

Farfesa Isah Ali Pantami

33
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Ƙwararren malamin jami’a kuma masanin aikin jarida, Farfesa Kabir Danladi Lawanti ya yi hasashen cewa akwai yiwuwar ɗan takarar Gwamna a Jihar Gombe a ƙarƙashin Jam’iyar PDP, Farfesa Ali Isah Pantami na iya samun nasara.

Related posts

Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya

Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya

June 17, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026

A yayin da yake bayyana hasashen nasa a shafinsa na Facebook, Malam Lawanti ya kawo hujjojin guda bakwai, domin ƙarfafa hasashen nasa, kamar haka:

Na ɗaya, Malam yana da matuƙar goyon baya saboda matsayinsa na masanin addini. Talakawa Musulmi suna matuƙar son shi.

Na biyu, mutanen Gombe suna matuƙar jin haushin Inuwa Yahaya saboda irin yadda ya gudanar da jihar a cikin shekara takwas da ya yi yana mulki. Fushin Inuwa zai iya shafar Jamilu.

Farfesa Isah Ali Pantami

Na uku, har yanzu Jamilu na jan ƙafa wajen tuntuɓar ‘yan takarar da aka kayar a zaɓen-fidda-gwani. Don haka, fushin wasu zai koma kan Jamilu.

Na huɗu, ya ce wasu suna cewa Jamilu ya jima yana cin amanarsu a siyasa. Saboda haka za su rama yanzu.

Na biyar, ɓangaren Goje shi ma yana nan. Wasu jira suke su huce haushinsu.

Na shida, Farfesa Lawanti ya ƙara da cewa, Gombe ta kasance a ƙarƙashin mulkin PDP na tsawon shekaru 16. Ko jihar tana cikin jihohin da aka ce za a bar wa Wike ya samu gwamna? Ita ma wannan maganar akwai ta.

Dalili na 7 kuma na ƙarshe, Malam Lawanti ya ce, Pantami na da ƙima (capacity).

“Wannan ra’ayina ne kawai bisa abin da nake ji daga majiyoyi masu dama. Cikin kwana kaɗan, duk wannan hasashen na iya canzawa. Amma Pantami na da damar samun nasara sosai a 2027, gaskiya.” A cewar Farfesa Kabir Danladi Lawanti, a yayin da yake ƙarƙare hasashen nasa.

Gare ku al’umma, shin yaya kuke ganin wannan takara ta Farfesa Ali Isah Pantami, akwai haske a ciki ko akasi? Ku bayyana ra’ayinku a Comment Section.
__________

Previous Post

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta

Next Post

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

Related Posts

Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya
Siyasa

Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya

June 17, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
Siyasa

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC
Siyasa

Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC

April 9, 2026
Next Post
Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa's Story, Preserve Cultural Heritage

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Kyautata Wa Marayu Da Mabuƙata Alheri Ne

Kyautata Wa Marayu Da Mabuƙata Alheri Ne

July 17, 2023
Tattaunawa Ta Musamman Da Dokta Bukar Usman Da Sashen Hausa Na Rediyo Faransa (RFI)

Tattaunawa Ta Musamman Da Dokta Bukar Usman Da Sashen Hausa Na Rediyo Faransa (RFI)

August 27, 2024
FESTIVAL OF AUTHORS KADUNA 2024

FESTIVAL OF AUTHORS KADUNA 2024

October 24, 2024
YAMTARAWALA Ya Kama Hanyar Lashe Gasar Adabi Ta NLNG

YAMTARAWALA Ya Kama Hanyar Lashe Gasar Adabi Ta NLNG

August 31, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Afirka Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya Na Bana
  • Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage
  • Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Afirka Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya Na Bana

Afirka Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya Na Bana

July 10, 2026
Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

July 9, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.