• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, July 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta

• Ta Sake Jaddada Aniyarta Ta Tsaron Ƙasa

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 7, 2026
in Labarai
0
Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta

Bangon Mujallar Taskar Gizago 53

10
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta

• Ta Sake Jaddada Aniyarta Ta Tsaron Ƙasa

Related posts

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

_________

A ranar Lahadin da ta gabata, Rundunar Sojojin Najeriya ta gudanar da gagarumin biki a birnin Fatakwal, Jihar Rivers, inda ta karrama tsofaffin sojoji da kuma wasu jami’an da ke kan aiki, a matsayin wani ɓangare na bukukuwan Ranar Rundunar Sojojin Najeriya ta 2026 (NADCEL 2026).

Bikin, ya nuna irin ƙudurin Rundunar Sojojin Najeriya na ci gaba da girmama sadaukarwar jami’anta, tare da ƙarfafa haɗin kan ƙasa, ƙwarewar aikin soja da kuma haɗin gwiwar kare tsaro da cikakken ikon mallakar ƙasar Najeriya.

Da yake jawabi a zauren bikin na EUI Event Centre, Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana cewa NADCEL 2026 wani muhimmin mataki ne na kawo sauyi da bunƙasar Rundunar Sojojin Najeriya. Ya ce ayyukan da aka gudanar a faɗin ƙasar sun nuna rundunar a matsayin wata muhimmiyar hukuma da ke ƙarfafa haɗin kan ƙasa da zaman lafiya. Ya ƙara da cewa tarihin rundunar na jaruntaka, juriya da hidimar ƙasa ba tare da son kai ba, kamar yadda aka gani a ayyukan wanzar da zaman lafiya a sassa daban-daban na Afirka da kuma ayyukan tabbatar da tsaron cikin gida, na ci gaba da ƙarfafa tsaron ƙasa da kuma ƙara wa al’umma ƙwarin gwiwa.

Babban Hafsan Sojin ya kuma yi ta’aziyya tare da karrama gwarazan da suka rasa rayukansu, yana mai jaddada cewa sadaukarwarsu ita ce ginshiƙin da Rundunar Sojojin Najeriya za ta ci gaba da gina ƙasa mai ƙarfi, aminci da tsaro a kai.

Janar Shaibu ya sake tabbatar da cikakken biyayyar rundunar ga Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, kula da walwalar jami’anta da kuma ci gaba da inganta ƙarfin aikinta, domin fuskantar sabbin barazanar tsaro masu sauyawa. Haka kuma ya nuna matuƙar godiyarsa ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu saboda irin goyon bayan da yake bai wa rundunar ta sojojin Najeriya, wanda ya ci gaba da ƙarfafa ingancin ayyukan rundunar, bunƙasa ƙarfin dakarunta da kuma shirinta na gudanar da ayyuka a dukkan wuraren da take aiki.

Bangon Mujallar Taskar Gizago 53

A madadin Gwamnan Jihar Rivers, Sir Siminalayi Fubara, Sakataren Gwamnatin Jihar, Dr. Dagogo Wokoma, ya bayyana bikin a matsayin wata dama da ta dace, wajen karrama sadaukarwar hafsoshi da sojojin da ke ci gaba da kare ƙasa. Ya kuma yi ta’aziyya ga gwarazan da suka rasa rayukansu tare da nuna alhini da goyon baya ga iyalansu.

Bugu da ƙari, ya yaba wa Rundunar Sojojin Najeriya saboda muhimmiyar rawar da take takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Rivers, musamman ta hanyar haɗin gwiwarta da Runduna ta 6 ta Sojojin Najeriya. Ya kuma sake tabbatar da aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da haɗin gwiwa wajen samar da kayan aiki, tallafin gudanar da ayyuka da kula da walwalar jami’ai domin cin ma muradin tsaron ƙasa.

Tun da farko, Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na Sojoji da Fararen Hula, Manjo Janar Musa Etsu-Ndagi, ya bayyana Bikin NADCEL 2026 a matsayin wani abin tunawa da ya nuna nasarorin da Rundunar Sojojin Najeriya ta samu a fagen ayyuka, ayyukan jin ƙai da kuma ƙara faɗaɗa haɗin gwiwar dabarunta. Ya yaba da ayyukan jin ƙai da Ƙungiyar Matan Hafsoshin Sojojin Najeriya (NAOWA) ke gudanarwa ƙarƙashin jagorancin Shugabarta ta Ƙasa, wadda kuma ita ce matar Babban Hafsan Sojojin Najeriya.

Haka kuma ya yaba da nasarar shirya Taron Shugabannin Rundunonin Sojojin Ƙasa na Afirka (African Land Forces Summit). Ya kuma nuna godiyarsa ga Gwamnatin Jihar Rivers, Shugabannin Rundunonin Sojojin Ƙasa na Afirka, tsofaffin sojoji da kuma tsohon Kwamandan Rundunar ECOMOG, Manjo Janar Felix Mujakperuo (Mai Ritaya), saboda gudummawar da suka bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.

Bikin na NADCEL 2026, ya ƙunshi wasannin al’adu, nuna shirye-shiryen bidiyo na tarihi, raye-raye da waƙoƙi, barkwanci da kuma bayar da lambobin yabo ga Shugabannin Rundunonin Sojojin Ƙasa na Afirka da kuma fitattun tsofaffin sojoji, domin girmama irin hidimar da suka yi da gudummawar da suka bayar wajen tabbatar da tsaro a yankin Afirka da ma nahiyar baki ɗaya.

Kamar yadda Muƙaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojojin Najeriya, Kanar Appolonia Anele ya bayyana, ya ce taron ya samu halartar tsofaffin Hafsoshin Tsaron Ƙasa, tsofaffin Hafsoshin Sojojin Najeriya, Shugabar NAOWA, mambobin ƙungiyar jakadun ƙasashen waje, sarakunan gargajiya, manyan hafsoshin soja masu aiki da masu ritaya, tsofaffin jami’an da suka bar aiki da iyalansu. Hakan ya sake nuna irin ƙaƙƙarfan alaƙar da ke tsakanin Rundunar Sojojin Najeriya, tsofaffin sojojinta, abokan hulɗarta na dabaru da kuma al’ummar Najeriya.

__________

Previous Post

Lionel Messi: Tauraron Da Ya Sauya Tarihin Ƙwallon Ƙafa A Duniya

Next Post

Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

Related Posts

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi
Labarai

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Labarai

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina
Labarai

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026
Next Post
Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara - Farfesa Lawanti

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

MENTAL HEALTH: A UNIVERSAL HUMAN RIGHT – Gen. Buratai, CFR

MENTAL HEALTH: A UNIVERSAL HUMAN RIGHT – Gen. Buratai, CFR

October 12, 2023
Gwamnati Ta Kula Da Mu

Gwamnati Ta Kula Da Mu

May 29, 2023
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
An Samar Da Maslaha A Takaddamar Sheikh Idris Da Gwamnatin Bauchi

An Samar Da Maslaha A Takaddamar Sheikh Idris Da Gwamnatin Bauchi

July 29, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.