Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami
__________
Sananniyar mai kwaikwayon murya a finafinan Indiya, Moofy ta sanya ƙafar wando ɗaya da ɗan fim ɗin barkwanci, Ayatullahi Tage saboda ɗan takarar Gwamna a Jihar Gombe, a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami.
Tage da Moofy sun ɗauki lokaci a makon nan suna caccakar juna a soshalmidiya, inda daga ƙarshe dai ita Moofy ta yi masa gargaɗi na ƙarshe, inda ta rubuta cewa:
Ku gaya wa ɗan barkwancin nan da ya fita daga harkata.Ya nemi namiji ɗan uwansa ya yi faɗa da shi.
Ba na neman izinin kowa kafin in yanke shawarar wanda zan mara wa baya. Na san abin da nake yi kuma ina tsaye a kan zaɓina.
Taimako ba cin amana ba ne, sauya matsaya ba laifi ba ne kuma samun dama ba abin kunya ba ne.
Lokaci zai bayyana komai. Allah ya ba mu ikon bambance siyasa da ƙiyayya.
Ba a wannan saƙon kaɗai Moofy ta tsaya ba, sai da ta haɗa shi da zazzafan bidiyo, inda ta yi wa mutuncinsa biji-biji, har ma da ƙunduma-ƙunduman kayan Maguzawa.
A kan haka ‘yan Comment Section suka tare wa Tage faɗa, suka yi ta antaya mata antayayyun martanoni. Ga kaɗan daga abin da suke cewa:
Buhari Shu’aibu Maiyama ya ce: “Ke ina kika ga wata DARAJA? Kullum sai zage-zage kike yi.”
Sai kuma Ubandoma Haidar Ali, wanda ya ce: “Uhmmm! maganar wannan yariyar tana ban surprise because always kina alfahari da rashin kunya. To ai gwara Ayatullah sau dubu da ke tsohowar kil+ki kawai. Ke ub+nki bai taɓa gaya miki ki daraja namiji ba? Ko Allah ya ce Aljanar mace na ƙarƙashin ƙafar namiji amma da yake ub+nki ba Allazi boko ne, ba Allazi Ƙur’ani ba! Jahil@ me cin mutunci halittar Allah. Shi ya sa aure ya gagara. Ai haka za ki tsufa a gaban daƙiƙin ub+nki da uw+rki,
Isma’il A. Sanda kuwa ba’a ya yi mata, inda ya ce: “Aradu ya fi ki kyau. Gaba ɗaya kin koma Algaita. Allah ya ba ki miji, ki yi aure.”
Sai kuma Queen Teema Love Katu, wacce ta rubuta cewa: “Shegiy@, wawiy@r banz@. Ki je ki yi aure ba gantali a titi ba. Tsohuw@r banz@. Kawai ji muryarta, a dole sai kin zama celebrity ne? Bons¢nse human.”
Shi kuwa Muhammad Yusuf, cewa ya yi: “Ka ga wani namiji da ƙoƙari, har da daura ɗan kwali da rangwaɗa. Lallai hoda ta yi bala’i a fuskar nan” (Hahahahaha, wato shi a nufinsa wai ita Moofy namiji ce, ba mace ba…hahahaha).
Sai kuma tsokacin Abubakar Salisu, wanda ya ce: “Ni ban taɓa kallon ki a matsayin mace ba, a matsayin gardi nake kallon ki.”
Shi kuwa Sarkin Barkwanci, Bala Ba Ka Son Wani Ya Samu sai ya ce: “Ke yanzu dun bakki da kunya, Tage ne yake neman al’umma ta dalilin ki? Kuma yaushe kin ka zama mace?”
A kan haka sai Anas Hassan ya biyo bayansa da cewa: “Bala Ba Ka Son Wani Ya Samu, tambayar mana ita dai, ni wallahi da har tausaya mata nake, ina ganin kamar ba za a samu mai son ta ba; shi ya sa har yanzu ba ta yi aure ba saboda wallahi mummuna ce ta faɗa wa Sarki. Ga shi duk ta bi ta sassoya fatar tata saboda mayikan bilicin, wanda ma bai karɓe ta ba.”
Murtala Ibrahim Sambo kuwa Farfesa Pantami ya yi wa addu’a, yana cewa: “Allah ga bawanka Isah Ali Ibrahim Pantami, ka yi masa Gomnab Gombe, ya Hayyu, ya Ƙayyum'”
Daga nan kuma sai Abubakar Abba Marota, wanda ya tsokanta cewa: “Ashe ba za ki iya faɗan ba? Ku ka ce Ke shegiy@ ce Ke kika fara ci masa mutunci! Ai sai ki ce kawai ya yi haƙuri.”
Haka fa…! Babu shakka, ashe shi ya sa masu hikimar kalami suke cewa, siyasa mugun wargi, idan ba ka shiga ba, kar ka fara!
__________












