• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, April 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Yadda Bikin Ƙaddamar da littafin SIRRIN MACE MUSULMA Ya Gudana A Kabo

Mukhtar Yakubu by Mukhtar Yakubu
May 29, 2025
in Adabi
0
Yadda Bikin Ƙaddamar da littafin SIRRIN MACE MUSULMA Ya Gudana A Kabo

Marubuciya Fatima Aminu da littafinta

41
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Yadda Bikin Ƙaddamar da littafin SIRRIN MACE MUSULMA Ya Gudana A Kabo

Daga Mukhtar Yakubu

Related posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Daga Hagu: Ado Ahmad Gidan Dabino, marubuciya Fatima Aminu Kabo da wasu marubuta, bayan kammala bikin ƙaddamar da littafin

A daidai lokacin da ake ganin harkar rubutun littattafan Hausa tana samun koma baya sakamakon yadda kasuwar littafin take durƙushewa, sai ga shi ana samun wasu masu kishin Hausa da ci gaban adabin suna iya ƙoƙarin su domin ganin harkar ba ta kai ga durkushewa ba.

Fatima Aminu Alhassan Kabo tana ɗaya daga cikin mata da suka tsaya tare da jajircewa wajen rubutun littattafai a wannan lokacin. Bisa ƙoƙarin nata na samar da littafin da zai koyar tare da faɗakar da al’umma abin da ya shafi zamantakewar rayuwar aure, musamman mata a wannan lokacin; don haka ne ta yi namijin ƙoƙari wajen wallafa littafin “Sirrin Mace Musulma” domin bayar da gudummawarta ga al’umma.

A ranar Asabar, 17 ga Mayu ne dai aka yi taron ƙaddamar da littafin a Ƙofar Fadar Hakimin Kabo, da ke Karamar Hukumar Kabo a Jihar Kano.

Bikin, wanda ya samu halartar manyan baƙi kama daga ‘yan siyasa da sarakuna da malaman addini, an fara ne da taƙaitaccen bayani daga Babban Baƙo mai jawabi, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino. Ya yaba wa marubuciyar bisa ƙoƙarinta na rubuta da littafin, wanda a ganin sa; ba ƙaramin ƙoƙari ba ne.

A ta bakinsa, ” Rubutun littattafai a yanzu sai wanda ya daure kuma ya yarda sadaukarwa ne rubutun da ya yi, domin ba da gudummawarsa.”

Don haka ya yi kira ga al’umma da su daure su sayi littafin, domin amfanuwar su ga abubuwan da littafin ya ƙunsa. Haka nan ya yi kira ga ‘yan siyasar yankin na Ƙaramar Hukumar Kabo da ma na Jihar Kano baki ɗaya da su ɗauki nauyin buga littafin da yawa domin rabawa ga makarantu, don ƙaruwar su da ilimin da ke cikin littafin.

Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo, Alhaji Lawal Najumen Kano, wanda shi ne Babban Mai Ƙaddamarwa, ya nuna farin cikinsa a game da samar da wannan littafin, wanda kuma ya kasance marubuciyar ‘yar ƙaramar hukumarsa ce ta Kabo. Don haka ya ƙara jinjina a gare ta, tare da ba ta ƙwarin gwiwa don ganin ta ci gaba da rubuta da littattafai masu inganci don faɗakar da al’umma. Ya ƙaddamar da sayen kwafin littafin a kan Naira miliyan ɗaya da rabi. Yayin da Ƙaramar Hukumar Kabo ta saya a kan Naira miliyan ɗaya.

Previous Post

HANJIN JIMINA

Next Post

Tribute to Ngũgĩ wa Thiong’o: The Literary Lion of Africa (1938-2025)

Related Posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue
Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
Next Post
Tribute to Ngũgĩ wa Thiong’o: The Literary Lion of Africa (1938-2025)

Tribute to Ngũgĩ wa Thiong’o: The Literary Lion of Africa (1938-2025)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

TEARS AND BLOOD

TEARS AND BLOOD

November 4, 2024
Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

April 18, 2026
RAYUWA (Sadaukarwa Ga Talakawan Najeriya)

RAYUWA (Sadaukarwa Ga Talakawan Najeriya)

September 5, 2023
Gwamnatina Za Ta Mutunta ‘Yancin Kafafen Yaɗa Labarai

Gwamnatina Za Ta Mutunta ‘Yancin Kafafen Yaɗa Labarai

December 19, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.